CHAPTER 14

2.8K 193 1
                                    

Tsugunawa yayi a gabanta yace kawo hannuki !
Kallonsa take a ranta tana Cewa dama oga sir Dan iska ne?

Dama yawanci sojojin nan mazinata ne ga shan giya da sigari
Dan iska me zibin samudawa

Tafadi hakan a zuciyarta domin it a atunaninta wani abin zaiyi da hannunta domin tun batakai haka Ba inna ke ce mata duk namijin da ya tabata bada sannin innar Ba to Dan iska ne amma banda baba da ya abubakar

Tsawa ya daka mata aiko ta miko hannun nata. Igiyan ya fara shirin kulla mata ai atake ta fara kuka da hawaye

Kallon ta yayi kamin yayi murmushin gefen baki yace:
Ashe de baki cika jarumar Ba
ai nadauka taurin kanki bazai bari kiyi kuka Ba.

Ajiye igiyan yayi a wajan ya fita daga dakin ya jirkita pin din ya rufe.

Kuka ta fashe dashi tana burburwa a kasa har ciwon dake hannunta ya fara jini bata saniba

Wani sautin da cikinta ya bayar shi ya tuna mata da cewar bataci abinci domin sau biyar takecin abinci banda kananun kwamulashe da take yi

Tunawa tayi da wani lokaci

Flash back

Inna Wai haryanzu baki gama miyar bane nifa kinsan bama er mutunci da yunwa

Inna dake kitchen tace Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
kinga ni ki rabu dani kinfiso Nayi irin wannan miyan naku na 'ya'yan yanxu

Amina ce tafara waka tana buga gwannon hannunta da

Iyya yunwa batada kara,iya yunwa ba'a mata lahaula,iya yunwa batada Sabo wayyo iya yunwa na iya karwa Iya yun..........

Muryan inna ta jiyo wadda ta leko tana kallon ikon Allah

ta Ce to ai bazansan kinajin yunwa Ba sai kin fara bin makwabta

Turo baki tayi tana guna guni ta mimmike kafa a kofar daki tace
inna shiyasa nace kiban na dafa kika ki ki Duba fa yadda dare tayi

Inna tace wai karfe biyar kike so na dinga gama abincin dare ne ?

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now