CHAPTER 77

2.8K 189 43
                                    

RECAP

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, wani kuna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan nawa sai na kasheki.

CONTINUATION

Jiki na rawa nurse din dake kula da ita tazo ta riko hannun ta dake zubda jini cikin harshen turanci tace ina rokon ki ki barni in koma kasar mu kar wata rana su gane ba a coma kike ba su kasheni dama ance yan ta'adda ne bakaken fata. Mari ta falla Mata tace ki iya bakin ki. Hawaye nurse din ta fara tace maza goge hawayen nan sannan kika sake wani ya gano me ake ciki ni da ke ne. Kamata ma yayi ki ji dadi ana biyan ki ba tare da kinyi aiki ba.

Cikin kuka nurse din tace idan yanzu suka shigo suka ga hannun ki da ciwa ta yaya zan fara bayani? Hankade ta tayi Tate da zama bakin gado tace gyara min hannu na.
Jiki na rawa kamar mazari haka nurse din ta fara dressing hannun nata. Itako tunani take a ranta kamin tace ni ayush nayi alkawari indai bazan samu yazeed ba toh babu mai samun sa kuma wad......

Ringing wayanta ya fara hakan yasa bata karasa maganan ta ba ganin goje love na yawo akan screen din yasa ta jan tsaki tare da dauka cikin murya my zaki tace my love! Ta dayan bangaren goje yace wifey wai yaushe zaki tashi daga jinyan karyan nan ne ? Nayi missing dinki fa.

Murmushi mai sauti tayi tace soon karka damu sai anjima banason su jiyo ni bye zan kashe wayan ne.
Wani tsaki taja tare da fadin kaina aikinka ya kusa karewa. A bangarenshi kuwa tunanin yadda zai kashe ayush ne da tayi taking control ta masa handing over.
Bokanta ta Kira sukayi kus kus Wanda nima banji ba. Tace shikenan ko da akwai wani Abu. Ta dayan bangaren boka mugu yace wannan aikin babba ne dan haka ina bukatar ki samo fatan farjin mace sabon gawa zan miki wani hadi sai kisa a cikin jikinta,ki tabbata kin tura sosai tace zan iya bayarwa ayi? Boka yace ko da wasa, da kanki zakiyi!
Tace naji matsalata dakai ka fiya tsauri, dariya ya sheke dashi tace dadi na fa? Tace aikin ka ba wasa.
Dariya suka sheke dashi mai ban tsoro Wanda yasa cikin nurse kadawa da daukan ruwa dukda cewa batamin yaren tasa ba abin arziki ake kullawa ba.

Ƙwanƙwasa kofan dakin da akayi yasata kwantawa yayinda nurse din ta lillika mata fake drip da sauran su.
Bude kofan tayi zakiyya ce ta shigo ta zauna a bakin gadon tare da shafo kumatun kanwarta tana Mata kallon so, kamar kullum yauma sanda ta tamabayeta yaushe zaki tashi? Hawaye ne suka dinga zirya a idanunta.

Bayan aani lokaci tace ma nurse din zata tafi nurse dai nata gyada kai ne Dan banda film bata taba ganin irin wannan mugunta ba.
Ayush kam tunani ta lula bayan zakiyya ta fita. Juyi tayi tare da tuno sanda ta fara haduwa da goje.

FLASH BACK

Kamar yadda kuka sani zakiyya ta kasance me kokari,makaranta daya suke zuwa har ayush toh saide zakiyya tafi ayush da aji daya.
Ayush a rayuwanta babu Wanda take mutuwan so kamar Farouk saurayin zakiyya hakan yasa take Mata hassada, gashi ta fita kokari tana karban kyaututtuka.
Yau ta kasance ranan rufe makaranta kamar kullum zakiyya ce tazo na daya, yan ajin su ayush din suke ta tsokanan ta wai itace dakikiyar family din baki daya shiyasa ko turanci bata iya ba lokacin. Da gudu ta fice tana kuka bata ganin inda take tafiya. Cin karo tayi da marka mai goro da Sigari tayi Mata bari nan fa marka tace ta biyata, ita kuma batada kudi. Hayani ne ya kaure, karkashin wani rumfa goje yace ke marka wai me kike ta daga makokoro ne? Tace wannan banziyar kwailar ce ta yi mini bari, karki ga kinje makaranta ki nemi ki kawomin ranin hankali ta karashe tana cin kwalar ayush.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now