CHAPTER 61

3.9K 274 19
                                    


Make sure kunyishi ba tareda wani kuskure ba!
Ta dayan Abangaren akace yes ma.
🌹🍀

Ayush ne ta Shiga dakin zakiyya tace sister zakiyya tace yes kina bukatan wani Abu ne?

Still idonta Adan kumbure. Kamo hannun zakiyya ayush din tayi ta zaunar da ita a bakin gado tace sis nikam tunani na zauna Nayi naga Cewa tunda dai kishiyarki ta rusa miki gida nima an kwacemin saurayi why not muje mu nemi taimako.

Zakiyya tace taimako kuma? Wani irin taimako ? Gyara zama ayush tayi tace akwai wata kawata tacemin akwai wani malami aikinsa Kamar yankan wuka. Indai kikaje wajensa Toh matsalarki tazo karshe ga aikinsa babu wani tsada kuma ance.....

Zakiyya tace dakata! dakata!! dakata!!! Ke yanzu da ilminki da wayewarki zaki dinga yarda da irin abubuwannan ?kuma wa yace miki malamine? Boka ne shi babu wani malanta fakewa kawai yake a inuwar malantaka.
Yanzu ke akan abin duniya kikeson Nayi shirka? Toh bankai nan ba bari kiji tun wuri gara ki cire wannan Abu a ranki ku ko a modern way ai that is madness ba class dinki bane please! Use your sense duk macuta ne malamannan.

Ajiyan zuciya ayush ta sauke tace kuma fa Gaskiya kike fadamin da na kusa In tafka babban kuskure amma na gode da kika fada min Gaskiya Allah ya saka da alkhairi.

Shafa kanta zakiyya tayi tace what are sisters for?Idan ban fada ma little sis dina Gaskiya ba wa zan Fadawa ? Dariya ayush tayi tace am not that little fah. Shekaru nawa ma kika bani ko 9 bai kai bafa.
Dungure kanta zakiyya tayi tace munji dai na girmekin Ashe.

Dan abin tausayi ayush Tayi tace sis Dan Allah Kuban key din motanki inaso inje in siyo wani abu. Zakiyya tace ki bayar a siyo miki mana yaushe muka iso garin ai akwai gajiya. Ayush tace abin is a little bit private kinga ne ai? Zakiyya tace okay bari in canja kaya muje tare mana nima dama inason inje shopping ayush tace yanzu fa kikace akwai hajiya ki bari gone sai mu fita ko? Zakiyya tace to kije dasu sahir mana kinsan birthday din sahir ya kusa he will be six years next month. Ayush tace nima ba dadewa zanyiba, gobe ba sai muyi Komai da Komai ba?

Zakiyya tace okay ba matsala amma karki Dade fa.
Ayush tace okay na wuce Toh saina dawo.

Fita tayi tana tafiya tadan kunna waka tana gyada kai abinta tana rausaya wa. Birki ta taka taji shiru kara takawa tayi still taji shiru ihu ta fara yi yayinda Motan ya fara kobo da ita akan titi.
Bata ankare ba motanta ya Shiga kasan wani trailer.

Mutane ne suka cika wajen makil ga hasken rana ya dallo wal bari yayi zafi Motan da ayush ke ciki bazaka dauka mutum zai fita ba saboda yanda Motan yayi raga raga ga ayush kwance agefe cikin jini atake akayi asibiti da ita.

Wayanta wani ya dauka wayar ma tayi raga raga. Cire sim din yayi yasa a wayarsa sweet sis ya gani Dan haka ya kira

Zakiyya zaune akan gado tana sulhu tsakanin sahir da safwan Cewa Idan suka raba Kansu kowa zai iya Shiga tsakanin su Wayanta yayi ringing ganin ayush ne yasa ta dauka da yar fara'arta amma labari da ya risketa shi ya gigitata tana kasa yin Komai.

Tashi tayi a zabure ta fice ta zauna dabas a parlour Kamar yar bori ta Cire wig dinma Ashe tanada gashi ba laifi rashin godiya wa Allah yasa ta yin karu ihu ta fara yi

Waiyo Allah na,na Shiga uku!YAZEED ka taimakamin yar mutane shikenan ta mutu !ta mutu waiyo ni Allah na.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Yazeed zaune a gefen minal fuskannan babu alamun wasa hannunsa rikeda takalmi. Minal ma fuskannan babu fara'a sai zunburo baki take Wai saboda dance taci abinci kamin yaje wajen mom Idan ba haka ba tasha takalmi.

Ihu suka fara jiyo sama sama yazeed ya ajiye takalmin ya nufi kofa yana farin wannan Kamar muryan zakiyya minal ma dauko sandan ta tayi tana fadin aiko itace.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now