21-22&23-24

1.2K 42 0
                                    

[10/3, 4:59 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*

               *NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*


*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Wannan page din Sadaukarwane ga latest novellas by samee Ina fatan Allah ya temaki wannan group me albarka inajin dadin kulawarku da comment dinku nagode sosai Allah ya Kara Mana Amana da zaman tare*



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI TSIRARA DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD SAW*


            21-22



Nafeesat ce ta Fara dawowa ta kawo Masa wayar ta zauna sai ta hango na arfan yafi nata yawa dabara ta fado Mata la Yaya kaga wani news Yana juyawa ta dauke nasa ta maida Masa da nata ta kyalkyale da dariya tsokanarka nake shima dariyar yai nafeesa bakya rabo da zolaya Wai Ina Maryam ne na aiketa kitchen ta yankon kayan fruit be gama rufe Baki ba sai gata Yana cin abinci cin da kyar ganin Maryam Taki sha Amma nafeesat ta shanye sai da tagama ta shanye tasa sannan hankalinsa ya kwanta har wata ajiyar zuciya ya saki lafiya ko dear ba komai sweety ya saki murmushi ya Kama cin abincin haikan ka'in da na'in sai da yaci ya koshi yadda zeji dadin aikin tukun ya daga lemon ya kwankwade


Yana lasar Baki cike da farinciki muntinsa biyar da Gama ci sun koma parlour suna kallo maryam ta shige daki Arfan yafara doka hamma bacci me nauyi ya Kama shi tuni ya Fara gyangyadi ganin haka nafeesat ta Kama shi da kyar Dan har yafara tangadi bacci yake sosai lafiya Wai dear nafeesat bacci kwantar Dani da kyar taja shi dakinsa na kasa ta kwantar da shi tafita taiwa maryama sai da safe Dan itama bacci take ji dama ita gwanar bacci ce suka wuce ta kulle dakin ta kwanta jikinsa Amma Ina kamar gawa kawai bacci yake bema San metake ba ta tabashi taga kawai sakin munshari yake to shi wnn lafiya wnn bacci haka Tai kwanciyar ta


Ita ko maryama ta shiga tashin hankali bala'in Sha'awa ce ta taso Mata gashi Bata San yaza Tai ba kawai namiji take bukata haka tadinga murkususu tana ciwon Mara tana matse cinya Bata saka hannunta ba Sam Dan tasan haramun ne duk tsananin Sha'awar datake ji haka ta daure gumi kawai take ko Ina jikin ta rawa yake take tayiwo alwala ta tada sallah a haka akan daddumar bacci me nauyi ya dauke ta gaba daya ta gama jikewa da gumi jagab Tai ta wasu irin mafarkai gashi Nan arfan Yana binta da gudu sunata gudu chan sai kawai taganshi a gabanta Yana wata dariya bazaki taba tseremun ba ke tawace hhhhhhh haka Tai ta mafarkai sai bayan magriba ta farka duk ta jike da gumi Tai salati ta sanar da ubangiji


Ta shiga Tai wankanta ta dauro alwala tana ta addu'oi Allah ya tsareta daga sharrin arfan Dan Wallahi masifar tsoransa take ita Wallahi tana tausayin yayarta da Allah ya hadata da Dan iskan namiji nafeesat saliha ce itako zata tambayeta garin Yaya suka hadu da wannan mijin nata duk da tana tunanin rabo ne inba haka ba Ina ita Ina shi a haka tafito parlour tana ta tunane tanane taga wayam basa Nan take ta Fara gyara ko Ina na gidan ta kunna turaren wuta wani Ni'imtaccen kamshine ya ziyarci hancinsa Yana tsaka da bacci a hankali ya bude idonsa meya faru dashi a sukwane ya mike


Yaga nafeesat na bacci itama dama ita mayyar bacci ce ta shinta yai nafeesat ya akai na kwanta bacci me nauyi haka ta mutstsike cike da magana irin ta masu bacci wallahi baccine ya dauke ka daga Shan lemo kadinga bacci da kyar na shigo dakai dakin Nan saboda bacci jikinsa har rawa yake garin Yaya Haka tafaru ya furta a ransa biki Sha lemon ki bane na Sha Mana wayo naima nasanja maka da nawa naka yafi yawa na dauke naka sanda nace ka juya dinnan sannan na dauke gyara kwanciyar ta Tai ta cigaba da baccin ta mtsww wani masifar tsaki yaja ya fada bandaki yai wankansa yafito yasha kana Nan Kaya sun Masa kyau ko kallonta beba ya fice Dan ya tsaneta ita ta janyo Masa tafka wannan asara


DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now