41-50

1.6K 40 10
                                    

[11/7, 3:30 PM] 👯🏻Feedy Bash On Top💃💃: *👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*

               *NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*


*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


~*Wannan page din sadaukarwane a gareku masu mun comment indai kinsan kinasan comment wannan page din nakune Dan Kuna da yawa bazan iya binku daya bayan daya ba wasuma bana cikin group din da suke Ina Jin Dadi masu yimun comment nagode Allah ya biyaku nagode da addu'oin ku agareni nagode sosai nice Taku a Koda yaushe princess feedy cele💃💃💃*~


*Bismillahir rahmanur Raheem*

                 41-42

A guje suka ruga daddy besan sanda ya bangaje mom ba yai gaba ya dare  bene cikin wani irin zafin nama ya karasa dakin a durkushe a gabanta ya ganta tana ta sharbar kuka ki tashi anty Dan Allah ki temakeni a hankali ya karasa ya dagata ya duba yaga Bata numfashi gata kwance warwas a kasa mom ta karaso lafiya alhaji menene ku dakkota maza muje asibiti yanzu da hanzari ya sauka ya juya kan motar saitin fita suka sa mata doguwar Riga suka dakkota suka sakko suka shiga da ita yaja suka tafi  aminu Kano suna zuwa cikin gaggawa akai emergency da ita suka tsaya cirko cirko shiko daddy gaba daya tunani yake wace wannan yarinyar a wannan lokacin ya yardarwa ransa ze Kara aure


Doctor ne ya fito ya katse Masa tunani biyoni office yai gaba ya bishi bayan sun zauna yace alhaji yarka ce ko matarka a a matar danace ok da matsala ne eh to ciki ne da ita sati bakwai to cikin karamine gsky gashi tasa damuwa a ranta Wanda ya haifar Mata da hawan jini Kuma mace me karamin ciki kamar wannan ace tanada hawan jini akwai matsala  hankalin daddy yai bala'in tashi to meyake faruwa Kenan ko dai har yanzu arfan be nutsu ba Yana wahalar da Yar mutane to yanzu metasata Suma eh fargaba da tashin hankali Dan haka a rage bata mata rai to bamatsala doctor yai godiya ya fice ya koma wajensu ta samu bacci yanzu Bari naje gida na dawo hajiya ya fice Dan baze juri ganin Maryam ba zeyi abun kunya abun ya daga Masa hankali da girmsa  wai soyayya ya rabb Katemakeni ya furta a hankali Yama kasa bude motar


Umman nauwara Ihu take kawai a zaune takasa tashi ihunta yasa makociyarta lekowa wadda nauwara ta gudu gidanta ganinta Tai dabas a kasa ta kasa motsi lafiya meyasameki dagani tabawa dagani ta rike hannuta ta kamata Ina gwiwa tayi sindim ta fashe da kuka na karye tabawa nauwara ta karyani kuka take kamar karamar yarinya tabawa ta tausaya Mata Bari na kaiki daki a kirawo malam din dake kakkarfa ce ta sakalo hannunta a kafada sukaje dakin ta ajiye ta sai kuka take gwiywa tahau Tai hani'an Kuma Taki lankwasuwa na karye shikenan wannan shegiyar yarinyar ta karyani Dame zan fita a dorani na shiga uku kuka take wiwi hardasu majina tabawa ta aika yaro yakira malam ta koma gidan


Malam ne ya shigo gidan lafiya tabawa akace kina kirana to indai maganar haule ne gwara ki rabu Dani Dan ninake auren ta ba ita ba Bata Isa ta juyani ba wallahi aurena da Indo Babu fashi idan bazata zauna ba ta koma kauye habawa ta Kara fashewa da kuka tana sheshsheka shikenan ya gama tona Mata asiri ba Wanda yasan me yake faruwa Amma yanzu ya fada agaban makotan ta shikenan Koda anfasa maganar sai ta yadu malam ba wannan maganar bace banma San da ita ba Allah ya kyauta yazaba abun da yafi alkhairi faduwa Tai haulen Ina tunanin ta gulle a gwiywarta to to Allah ya sawake Bari inje maza inkira me Dori ya fita da hanzari ya kira sarkin dorin kofar mazugal ya duba yace gullewace sai an daure kafar kwana goma za adinga gasa Mata ita ba ita ba fita har sati biyu tun kafin ya taba kafar ta Fara zunduma ihu ta shiga uku Allah ya kasheta ta huta Allah ya Isa nauwara kin cuceni muguwa kuka take kamar ranta ze fita ta sassauta ba wani sassaucin kwanakin gaskiya Babu hajiya Nan ya Kama kafar sai da ta saki fitsarin azaba kuka kashir ban malam ne ya rike ta da kyar ta yarda akai gyaran sai kuka take aka Gama ya bada maganin ya tafi


DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now