part 15

803 32 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


                   *70-75*


"Maryam mai ya sameki haka kike kuka mai ya faru? Dubi yadda fuskarki duk ta kumbura sundum, ice ko dai lafiya gaba daya kun dagan hankali na rasa gane meke faruwa?

Naje asibiti amma ban gan kuba hasali na kasa gane me ake boyewa?' Umma ce ta ce "Alhaji nai fa ba lafiya ta ke ta wannan kukan mun taho kawai ya yanke jiki ya fadi ashe hawan jini nai."

Salati suka kama dukansu Mama ta ce "dama Alhaji na da hawan jini tsahon shekarun auren mu ban taba sani ba tun saurayi da budurawa? innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!" Nafeesat ko kuka ta fashe da shi .

Tun dazu ta ke san tayi kukan dama abun ya gagara ba dalili amma yanzu ta samu dalilin yi, ta din ga kuka har da sheshsheka gaba daya ta basu tausayi dan ita Mama ta san kukan rashin mijinta ta ke da rashin kulawarsa gareta .

Mama ce ta ce "gaskiya ban yarda da wannan boye boyen ba tabbas akwai lauje cikin nadi, da fari Uwa ta fara daga bisani Uba ya dauka da naje na tarar da dan a gadon asibiti yanzu kuma mijin mu wai, me yake faruwa nai a gayan gaskiya?

Dan wallahi dama ni zuciyata tana zargi kala-kala akan wannan tarayyar ta auren Nafeesat, wallahi hankalina bai kwanta da wannan auren ba gaba daya bare yadda ake gudanar da zaman auren, ke mai kuke boyewa nai?" ta dakawa Nafeesat tsawa .

Gaba daya ta rikice ta fashe da kuka Mama ba sauki ta damko Nafeesat "wane munafinci kuke kullawa a cikin gidan naki har haka, dan wannan kulla kullar wallahi jikina ya bani daga gidan ki ta ke, dan mafarkin da nai jiya ba banza ba ke kuma zo nan."

Ta damko Maryam kawai bin ta ta ke da kallo ta gwale idanuwanta ta kalli tafun hannunta "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!" ta fashe da kuka tana tafa hannaye kuka ta ke.

"Maryam yanzu zargin da na ke miki sai da ya tabbata zargin da na kewa mijin Nafeesat a kan ki ya tabbata ke nan, yanzu Maryam sakayyar da zakuyi mana ke nan ciki Maryam! ciki! ba tun yau na ke fusankantar halin da kike ciki ba.

Amma zargi na ke shi ya sa na ke hana alakar ki da wannan yaron dan ban yarda da shi ba, amma aka nunan iyaka ta to ga abun da na ke gudu ya faru dan ko kaffara ba zan ba shi yai miki ciki.

Kuka Nafeesat ta ke har da shidewa saboda kuka Maryam ma kukan ta ke gaba daya Mama fada ta ke kamar zata ari baki, Nafeesat ko har ta fara fita hayyacinta saboda kuka.

"Haba Nafeesat kiyi shiru mana" cewar Umma "komai yai zafi maganinsa Allah amma bai kamata ki ta kuka ba a wannan halin da kike ciki da kike karkashin kulawar likitoci."

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now