Book 2 part 1

1.1K 34 3
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI, GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJI WANDA YA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTA MUKU WANNAN LABARI, ALLAH YASA KU AMFANA DA DARASIN DAKE CIKINSA, ABUNDA NA RUBUTA DAI-DAI ALLAH YA HADAMU A LADAN, KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA.*

*NAGODE MASOYANA, KAUNARKU GA DAN ISKAN NAMIJI YASA ZAN CIGABA DA TYPING, GANIN YADDA KULLUM KUKE TAMBAYARSA KUKE, KUNATA DAKON KARSHEN SA, AMMA SO BIYU ZAKU DINGA SAMU A SATI, KAFIN NA KARASA BOOK DIN DANAKE NA KUDI. NAGODE SOSAI.*

_*Wannan book din sadaukarwane ga mahaifina, Allah ya jikansa yai masa rahma ya haskaka masa.*_

               *1-5*

Innalillahi wainna'ilaihir raji'un, Hajiya! Hajiya ta! girgiza ta yake iya karfin sa, ya sungume ta yai waje da gudu.

Haruna! Haruna! juya mota maza maza mu wuce.

Duka masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ganin Daddy yana wannan ihun abunda basu taba jiba.

Hankalinsu be gama tashi ba sai da suka ga Mommy a hannunsa, ga dukkan alamu babu rai a tare da ita.

Gaba dayansu suka yo kansu suna salati, wata tsawa ya watsa musu "ku matsa ku bani waje."

A sukwane ya shiga bayan motar dan tuni Haruna ya juya motar, ya fada ciki yaja suka bar gidan, suka nufi wani private hospital mafi kusa dasu.

Ko parking be gama bari  yayi ba ya fito, kamar jaririya haka ya dauketa ko nauyin ta baya ji yai cikin asibitin da ita.

"Doctor dan Allah katemake ni, karta rasa rayuwarta dan Allah ka temaka mun" haka kawai yake furtawa.

Nan da nan Nurses suka amshe ta sukai emergency da ita, Doctor din na ciki nan da nan yai kanta ya fara bata temakon gaggawa, dan doguwar suma tayi ga dare ya farayi wajen 12.

Bayan awa daya karfe daya shaf, Doctor ya fito yace Alhaji yabi bayansa, bayan sun shiga office ya fara magana.

     "Gaskiya Alhaji daba dan kunyi gaggawar kawota asibiti ba komai ze iya faruwa, dan jininta lokaci daya yai mugun hawa, saboda haka dole a kiyaye bacin ranta, idan ba haka ba zata iya rasa rayuwarta.

       "Shikenan Doctor nagode, ayi duk abunda ya dace na kulawa da ita, zan iya ganinta yanzu.

Eh, "ba matsala zaka iya ganinta, amma bata bukatar hayaniya yanzu, san samu nema ace kaje gida ka dawo da safe, tunda bamu da bukatar masu jinya.

Fafur Daddy yaki tafiya yace anan shima ze kwana, haka ya kwana be rintsa ba.


      ****************

Maryam ce kwance rigingine akan kirjin Arfan,  baccinsa yake hankali kwance ita ko saka da warwara kawai take.

A ranta sam babu wani namiji yanzu sai Arfan, amma tasa a ranta tunda ya gama lalata rayuwarta meyai saura, ai gwara kawai taci gaba da gashi tunda tasan ba ita ba aure a yanzu.

Amma a ranta tanajin ba wani namiji da zata iya bawa kanta sai shi Arfan din, duk da bata san maza ba, amma tabbas  tasan cikakken namiji ne shi ta wajen saduwa.

Hakan shi yasa ta gwammace gwara ta tsaya a shi kadai din, amma kasan ranta tausayin Yar uwarta ne fal ranta da tausayin kanta, dan suna cikin tashin hankalin san abu guda a yanzu.

Musamman idan ta tuna Arfan mijin yayarta ne mafi soyuwa aranta, sai taji tai Masa tsana mafi muni a duniya, amma ba yadda ta iya, ya riga ya gama da ita, ya koya mata sansa a hankali.

"Tabbas zanyi rayuwa mara yanci, rayuwar bariki saboda haka mahaifina ya zabar min rayuwata,zanyi bariki zanyi suna amma bazan yarda wani namiji ya kara kusanta taba, Arfan Kai kadai zan cigaba da bawa kaina saboda kai ka lalatani."

Taci alwashin kodan ta koyawa Abbanta darasi akan san abun duniya, da abunda ya aikata musu, tasan dole yai nadama, tai wani murmushi me ciwo ta fashe da kuka.

Ya ilahi ta furta, jin haka ya farkar dashi ya kara rungumeta tsam.

Nan shedan ya samu dama ya fara kawata mata kyansa da surarsa, nan da nan taji wani abu ya soke ta  aranta.

Haba Maryam meye na kukan, haka nifa nakine kema tawa ce, banga abun kuka haka ba, nasan kema kina sona,dan haka kiyi hakuri mu samu masalaha muyi auren mu.

Murmushi tayi ta boye kanta a kirjinsa, ya kara rungumeta, nan da nan salo yasanja ya samu hadin kanta sosai a wannan karon, ganin hakan ya kara sakankan cewa da ita.

Sai karfe goma da rabi suka farka, da sauri ta mike ta shiga bandaki tana ta astagfurullah, tai wanka tai sallah sannan ta dora abincin, tana kunna wayarta kiran Mama na shigowa.

Gabanta sai daya fadi, tana dagawa Mama tahau fada,"uban me kikeyi a gida har yanzu baki taho ba ."

Ummm gaba daya ta rikice, "Mama baya nan ne be kwana a gidan ba, yana ajiye ni ya tafi aiki, tun dazu na gama abinci ina jiransa yazo mu taho."

Hmmm! Wata ajiyar zuciya Mama ta saki, "to shikenan idan bezo ba ki hawo mota kawai kizo, dama banda rigima tayaya Alhaji zece kije gida ki kwana ke kadai."

"Wallahi ko Mama dakyar nai bacci dan gidan shiru ba kowa, bara na kira shi" a waya ta kashe wayar.

Ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya, ta koma dakin yana kwance, amma ga dukkan alamu ya tashi yai wanka yai sallah, dan taga ga dadduma a shimfide kuma ta nade.

Da sauri ta matsa kusa da shi, ta rasama yaza tai ta tashe shi, a hankali ta matsa kusa dashi takai hannunta zata taba shi, jitai kawai ya fisgota jikinsa.

Kirjinsa ta fada nan ya fara hargitsa ta, yanai mata wani salo me tsayawa arai, wanda ya gama birkita mata lissafi, Allah ne ya temake ta wayarsa tai kara.

Idonsa yai jajur ya saki wani tsaki, ya jawo wayar ganin sunan Daddy yasa yai hanzari ya daga, yai masa sallama.

"Na'am, eh nine innalillahi wainna'ilaihir raji'un" ya saki wayar jikinsa yana rawa, kawai Maryam ya rungume ya fashe da kuka.

Itama rungume shi tai tsam tsam ta fashe da kukan, a hankali tana tambayarsa "lafiya meya faru?

A hankali ya bude baki, Mommy na Daddy na.........


*More comment more typing*

*Comment*
*Vote*
*Share*

*TO FANS MEYA SAMU MOMMY DA DADDY? SHIN SUNA RAYE KO MUTUWA SUKAI? KUDAI KU BIYONI A NEXT PAGE DAN JIN YADDA ZATA KAYA.*

*KO INA LABARIN SU LAWAN DA MUKARRABANSA? YA LABARIN BABY CHAKWAI DA ALHAJI GHALI DA NAUWARA ?YA KUMA WAJEN SU MAIMUNA?*

*KUDAI KU BIYONI KUSHA LABARI, COMMENT DINKU KADAI SHIZE SA NA CIGABA DA POSTING WANNAN BOOK DIN NAWA, IDAN KUNYI COMMENT YADDA NAKESO NACI GABA IDAN BAKUYI BA NA DIRE.*

            *Feedyn Bash*

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now