part 14

757 33 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Bissimillahir rahmanirraheem

                  *65-70*

Alhaji Ghali ya koma gida cike da farin ciki amma bai nuna masa ba ya cigaba da biye masa, duk sanda yai kokarin zuwa dakinta sai yaji shi gam ga shi ya rasa ina ragowar keys din su kai, bai san Baby Chakwai ya kwashe su ba.

Kullum yana zuwa ya dubata duk da ta tsaneshi tsana mai yawa, amma tana cin  abincin da ya ke kawo mata, dan kullum sai ya kawo mata abinci mai rai da motsi da kaji da fresh milk, dan ta gama fuskantar ciki nai da ita shi ya sa ta ke karba tana cika cikinta.

Saboda rabonta da al'ada tun lokacin da Alhaji Ghali ya kusanceta bata kara ganin al'adarta ba, ga yadda take yawan amai da yawan jin yunwa tana cin abinci sosai shi ya sa ta ke cin abun da ya kawo mata.

Bayan sati uku ta warke sarai din kin ya warke dama bukatarsa ke nan shi ya sa ya ke kula da ita da kansa, saboda yadda Doctor din su yai masa takara 2 weeks ya ce a barta ta warke amma shi 3 weeks ya bata dan ya barje guminsa.

Dan sam baya jin dadin kowa da komai a yanzu ba abun da ya ke so sai ya wuni a kanta, shi ya sa ya tama mata yau ya bakantawa Alhaji Ghali rai yau dan ya dade bai dawo ba ya gwangwaje a jikinta.

_(Wa'iyazubillah! Allah ya Allah! kai mana tsari da wannan mummunan aikin, Allah ka karemu da san zuciya ka tsaremu ka tsare imanin mu, na tabbatar banda kwadayi da san zuciya tabbas da Nauwara bata fada wannan masifar ba, wallahi mata mu hankalta mu cire kwadayi da san zuciya da burin auren kudi, dan baka san tayaya namiji ma ya tara kudin ba, wallahi tallahi irin wannan tana faruwa life a gaske duk da na dan sanja wani abu na kara wani, amma wallahi yana faruwa, kuma san zuciya ke kai mu ga halaka, yanzu meye amfanin auren da tai mai ta tsinta a kudin, fatan mu miyi addu'a Allah ya bamu mai zuciya ba mai dukiya ba, dan wallahi namiji mai zuciya shi ne miji, ina kuke matan masu kudin naira dubu gagararsu ta ke, wayanda aka sakarwa kuma mijin gagarar ganinsa suke, daga haka shi ke nan mace ta fada lesbian ko neman maza, ya ilahil alamina ina zamu kai wannan, musamman yan matan yanzu masu dogon buri, wallahi ku cire ranku daga buri ku shi ga hankalinku, ku tsaya matsayin da Allah ya ajiye ku, dan wallahi idan ma kayi da ce ka samu yadda kake so to tabbas wulakancin danginsa ma ya isheka Allah ya tsaremu ya tsare imanin mu dan wannan rayuwar wallahi sai addu'a wata yar tunasarwa ce, musamman da ya kasance 80% cikin hundred na novel dina gaskiya nai Allah ka kiyayemu.)_

Ya siyo mata abinda yaga tafi ci chips da kwai sannan ya hado mata da fresh milk mai masifar sanyi, sai da taci ta ko shi ya bijiro mata da maganganu marasa dadi da rashin dadin sauraro masu barazanar tarwatsa zuciya.

"Kin ga Nauwara bafa zan miki dole ba ba zan takuraki ba amma abun da nakeso ki sani haka zaki ta rayuwa a wannan gidan a wannan halin dan ba mai cetonki.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now