part 17

837 41 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


                   *80-85*

Daddy ya ce "subhahanallah zaka je ka kashe kan ka a baza a wofi akan abun da  ka san gaibu nai ba samu zakai ba, idan ban da baka da hankali tayaya kana auren ya zaka auri kanwa shashasha kawai."

Momy ce ta shigo da sauri ta tallafe shi ta dinga masa fifita har ya samu sa'ida sai da ya lafa yana haki, ya kalli Daddy ya fashe da kuka "tabbas Daddy baka kaunata baka kaunar ganin farin cikina a duniya."

Mikewa yai ya fice daga dakin bai ce komai ba dan gaba daya abun ya gama fice masa arai, mugun tausayin yaransa yakeji a yanzu kawai daurewa yake dan ya nuna masa kuskurensa da abun da ya aikata saboda ya hankalta a gaba.

Hankalinta ya tashi ganin Daddy yai masa banza yama fice, cigaba da rarrashinsa tai tana kwantar masa da hankali a haka bacci ya fara daukarsa ta kamashi ta kai shi dakinsa.

Watan ta biyar a kwance a asibiti duk wani mai imani sai yaiwa Nafeesat kuka ta rame ta jeme sai uban ciki, baci ba sha sai ruwa da ake sa mata masu magunguna alhamdulillah jikin nata yai sauki sosai zuciyarta ce ta kumbura sosai.

Amma ta dan sabe a yau aka mai da ita ainihin dakin da aka kwantar da ita dan bazasu sallameta ba sai lokacinta yayi Edd din ta ya cika sannan zasi mata operations su ciro jaririn saboda bazata iya haihuwa ba a yadda ta ke.

Cikin watan sa bakwai cif a yanzu Maryam ko cikin ta ya kai wata biyar dan tana gidan kanwar Umma saboda mutane sun fara zargin wani abu akanta jikin nata dai alhamdulillah yau tana magana sosai ba laifi.

Bayan ya farka daga baccin ya mike ya dakko takarda da biro ya rubuta mata saki daidai har guda uku saboda sai ya sake ta tabbas zai samu damar auren kanwarta da ta kasance rayuwarsa a halin yanzu, dan wanda yai tunanin rabashi da ita tabbas ya raba shi da duniya nai.

Ya ninke ta ya fito ga bawa driver "ungo ka kai asibitin da matata Nafeesat ta ke ka ce a bata wannan in jini" shi kuma bai kawo komai ba ya hau mota ya tafi yana zuwa su kai kicibus da Abba ya rarrafo ya taho yau saboda yanaso ya duba jikin Nafeesat duk da shi ma sai a hankali.

Suka gaisa ya gaya masa aiken da Arfan yai masa da takkadar gabansa sai da ya yanke ya fadi saboda tashin hankalin ganin takadda, to mai ta kunsa amma ya dake ya amsa yace "bari na shiga na dubata duk da dazu muka dawo da Hajiya jikin nata da sauki ba kamar da ba."

Suka shi ga tare ya dubata tana murmushi ya fito ransa duk a jagule saboda yadda duk ta kare abun tausayi, ba abun da kake gani sai kashi Abba ya zauna suka gaishe shi sannan ya mikawa Mama takardar "karanta mana muji."

Ta karba ta fara warwarewa ta soma karantawa kamar haka.

_Ni Arfan hakika ina tsananin san kanwarki Maryam wadda ta sanadinta na bar duk wasu halayena saboda tsananin san da nake mata wanda rasata daidai ya ke da rasa tawa rayuwar gaba daya a doron duniya, kuma tabbas Nafeesat idan ina auran ki bazan samu damar mallakar muradin raina ba duk da Maryam ta kasance masifa ga rayuwata, ina santa mahaifina na Santa amma tabbas ni zan mallaketa saboda haka na yanke..._

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now