25-26

1K 35 5
                                    

*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*

               *NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*


*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


_*ASSALAMU ALAIKUM MY FANS INA MIKO SAKON GAISUWATA A GAREKU INA ME FARIN CIKIN SANAR DAKU NADENA POSTING DIN KOWANE BOOK DINA A KOWANE GROUP ONLY NA FANS DINA DAGA YAU DINAN NAN DAN KU SANI KULLUM MUNA WAHALA MUNA MUKU TYPING COMMENT YA GAGARA BANSAN YAWAN KORAFI AMMA SAI KUNSA MUTUM YAYI DAN HAKA NA YANKE HUKUNCIN ZAN DINGA YIWA IYA FANS DINA TYPING DAN INA SAMUN COMMENT DAGA GARESU ALHAMDULILLAH KUMA INAJIN DADIN ADDU'OI INSU GARENI ALLAH YABAR KAUNA NAGODE*_

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

              25-26


Baba Bello dai na gidan inna me Koko eh shi maimuna ko kema kinfi San Mai kudin tuni ta Fara zubar kwalla wallahi baba bantaba San namiji me kudi ba nafisan me addini Wanda yasan darajata data iyayena Wanda ze mutun tani Wanda zanfi karfin ci da Sha da Kuma suttura a hannunsa murmushi malam yayi naji dadin hangenki yanzu me kikace alfarma nake nema a wajenki duk da yata tagaza yimun idonsa ya ciko da kwalla baba ba abunda zaka nema a duniya ban maka Shiba Dan kaima karike mu ka kula da rayuwarmu bayan mutuwar mahaifinmu ka zame mana uba mun zamema yaya dan haka na amince baba allah yasa ayi a sa'a kukan dadi ya saka yau ga yarda ba tashi ba ta share Masa hawaye tabbas shima ze faranta Mata dai dai gwargwado Allah yai Miki albarka maimunatu turon mahaifiyar ki Tom tace ta shiga ciki


Malam shika dai yasan meye a zuciyarsa Kuma baze Sanja ba bazeyi watsi da mace me mutunci da karamci ba ita da iyalanta sai ga umman maimuna ta shigo malam Ina wuni lafiya suka Gama gaisawa sannan yai gyaran murya ya Fara magana kamar haka wato hajara muhimmiyar magana nake tafe da ita inaso kiban aran hankalinki Danmu tattauna akanta a tsari na musulunci be kamata mace kamar ki tana zaune ita kadai ba saboda ku Mata Kuna da rauni shekara uku kenan da rasuwar mijinki kinki ki tsaida hankalinki ki aure Kuma kowa yaganki zeyi zaton Baki haifi maimunatu ba Dan haka a cikin manemanki waya kwanta Miki a Rai idan Babu Ni nasamo Miki wani Kuma inafatan bazakiban kunya ba Zaki karbe shi hannu bibbiyu kidauki hakan a matsayin wata kaddara ce da Kuma yin Allah sannan Kuma munyi maga da diyata Maimunatu


Na tsaida aurenta sati biyu masu zuwa ita da Bello Dan gidan inna me Koko dafe kirji tayi malam karufa mun asiri a Kara wannan bikin nayi cuku cuku naseda gonar da mahaifinta ya bar musu saboda kayan daki kasan mu matanen karkara wallahi bazasi Mata komai ba musamman ansa sati biyu Kuma suna ganin muna maraya gani suke wani kudine da mu Kuma kaga dangina fushi suke Dani naki komawa kauye nai aure Ni Kuma wasiyyar malam na cika Akan karatun maimuna da Abba alhamdulillah maimuna tagama saura Abba kana kallo basa temako na dako hatsi bare inje musu da batun auren diyata ai Naga ta kaina murmushi yayi ki kwantar da hankalinki Nina tarko auren nizan Mata komai


A talauce dai namu na talakawa Dan haka ba abunda ze gagara hawaye ta Fara haba malam wahalar tayi yawa Dame zamu sakama murmushi yayi mubar wannan maganar ya maganar manemanki sunkuyar dakai tayi tana Jin nauyinsa malam ba Wanda yai mun ba Wanda na yaba dashi hamadala yai a ransa ya kalleta Ni na Miki wani zaro ido Tai a girgice ta mike Dan Allah malam karufan asiri wannan cin Amana ne dawane ido zan kalli matarka yadda muke tare da ita da wane ido mutanen unguwa zasu kalleni in maji da rade radin da ake mun dorama wahala yanzu Kuma bayan auren maimuna da zakai kace Nima zaka aureni baze yiwuba a fusace tabar wajen tabarshi yanata murmushi yasan meze yi Mata


Ana shirye shiryen auren alhaji ghali da nauwara gefe guda Kuma Yana Shirin auren wani luntsumemen saurayinsa Wanda zasi auren jinsi Wanda zasu je America a daura auren achan an shirya biki nagani na fada inda ze auri baby chakwai sunan da suke Kiran sa kenan ainihin sunansa mukhtar ya iya luwadi har kukan dadi yakesa alhaji ghali Allah ya shirya (Allah ka shirts ka tsaremu da mazajenmu da Yan uwanmu da musulmi Baki daya)an Tsara fati kala kala na watsewa da holewa Dan shi Sam baya farinciki da auren sa da nauwara tunda kudi takewa tazo taci kudin San ranta


Nafeesa ce ta fito lafiya Maryam me kike anan fadawa tayi jikin ta ta saki wani uban Kuka wallahi anty a yau saina koma gida bazan Kara cigaba da Zama a gidan Nan ba wallahi zan halaka kitemakeni Dan girman Allah Yar uwata jikinta na rawa ta rarumo wayarta ta Kira babansu cikin sa a bugu daya ya daga Abba a'a nafeesatu diyar albarka Abba Maryam ba lafiya gamu Nan zuwa kawai tace ta kashe wayar ta Kira arfan Yana tuki cike da nishadi my dear ya akai zan Kai Maryam gida Bata da lafiya murmushi yayi Dan yafi kowa sanin meke damunta ok kawai yace ya kashe wayar



Sororo tayi cike da mamaki sai ga Kiran abbanta karkuzo gamu Nan nida ummanku ranta beso ba to baba ita ko Maryam Taki cewa komai Banda kuka ba abunda take rike da mararta nafeesa natai Mata sannu duk ta hada gumi gaba daya tausayinta ya kamata mu tafi asibiti ne a'a anty kawai tace minti talatin sukaji nocking nafeesa da hanzari taje ta bude kofar baban sune da umman Maryam suka shigo suka zauna tanata murna yau ga umma a gidanta dama Abba yazo so biyu sororo uban yayi chab wannan ce cutar kiga yarinya a zaune dungurgur kice mun Bata da lafiya wannan yarinya da fitina kike duk cikin yayana kece zakka wallahi Baki Isa ki gagaren ba ehe



Kayi hakuri alhaji bita a hankali kaji meke damunta ya fyallawa umma wata muguwar harara kema ta gidan ta koya Miki Ina fada kina fada to wlh ahir dinki kinji nagaya Miki Allah ya huci zuciyarka sukuti yayan sukai cike da jimamin halin baban nasu yarinya ba lafiya Amma ya bi da fada ke nafeesatu yanzu haka uwarki ta koya Miki tarbar Baki harda ubankima jiki na rawa ta mike kuyi hakuri Abba ta shiga kitchen ta debo musu drinks da cups da ruwa ta koma ta debo musu ragowar take away din dasukaci da ragowar gasashshiyar kazar ta kawo sai washe Baki yake umma ko har kwalla take ganin yarta harta fada Amma ba damar magana sai daya zauna yaci yai Kat umma na kallonsa da yaran da kyar ta iya Shan ruwa shima nafeesa ce ta takura Mata



Yaci yai Kat ya nade ragowar na guziri ungo sayamun a hijjabin ki saboda Yan SA ido kamar ta rusa ihu haka ta karba jikinta ba laka sai sannan ya washe Baki ya kalli Maryam Yana kankance ido ke ki fito fili kigayan meke damunki yanzun Nan ranta ya baci ta ajiye kunya a gefe Abba Sha'awa ce Tai mun yawa aure nakeso duk kansu hatta shi sai dayaji shock fuska a hade kinsamo mijin eh malamin bokon mune tun muna boarding yake Sona sai ranar candy ya sanar mun kan uba nizaki zubarwa da mutunci malamin makaranta wallahi kinyi kadan Ni shi nakeso baba wallahi idan bakai mun aure ba kome ya faru Dani Kai ka janyon ka daukeni daga wannan gidan Kar rayuwata ta tarwatse ta fashe da kuka



*To fans mu hadu next page yawan comment yawan typing masoyana Ina godiya da kulawarku gareni Allah ya bar kauna nagode*




               *Feedyn bash*

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now