part 11

1K 47 6
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Bissimillahir rahmanirraheem

*Dedicated to:Fateema U Adam, nagode sis Allah ya bar kauna yadda kike faran ta mun wajen typing Allah kema ya faranta miki thanks dear.*


                   *50-55*

"Haba Alhaji ai sai ka kashe ta daukar doka a hannunka bai kamata ba sam, ka bari ma asan wa yai mata cikin sai ku dau mataki" cewar Doctor Mahmud.

Ina Abba kara matseta ya ke yana "ku barni na kasheta ko na huta da wannan bakin cikin da tashin hankalin da ta kunsa mun, tun da na ke ban taba tunanin zanci karo da wani abu mai kama da wannan ba a zuri'ata."

Ganin da gaske ya ke suka hadu suka bambareshi daga jikinta yana ihu kamar mahaukaci, gaba daya ya zauce saboda tashin hankali, "ku barni na kashe ta dan wallahi da naga wannan tashin hankalin gwara naga gawarta, kuma wallahi ba dai gidana ba ki sanja wani uban ba dai ni ba."

"Ai bata da wani uba da ya fika kuma wallahi a gidanka zata zauna daram." Umma ce ta fada tana kuka "tun sanda kuka taho na biyo bayanku dan duk maganarsa a kunnena yai muku, kuma dama na zargi wani abu a raina tun da naji shiru basu dawo ba."

"Kika kara magana sai ranki ya baci dan ba wata yar iska da zata zauna min a gida, ta koma inda taje tayo iskancin nata har tayo cikin amma wallahi ba dai gidana ba, idan ko ba haka ba wallahi sai dai ki bita ku tafi gaba daya."

"Wallahi ba inda zan bita kuma a gidanka zata zauna ko kaffara bazan ba, waya janyo wannan masifar kai ne da shegen kwadayin ka da san abun duniyarka, to wallahi anan zata zauna dan ko ka saken ba inda zani zama daram zan yi zaman yayana, dan kasan a yanzu dai wallahi sai dai kai ka barmun gida ba dai ni nabarma ba."

"Baki da mutunci naga alamu ni kike gayawa haka? au ho to nagane komai ke kika dorata a wannan turbar kenan, tom yau Allah ya tona miki asiri wallahi sai kun girbi abunda kuka shuka gaba dayanku, ke kike turata iskanci wato ko? to wallahi sai kin yi nadama saboda kin gagara har fadi in fada kike dani saboda fitsara."

"Kai dai zakai nadama wallahi Alhaji ai kafi kowa sanin cewa ba wata kalmar fadi in fada da zata ratsa tsakanina da kai, tun san da na aureka zuwa yau duk umarnin daka bani ina bi ban taba ketare dokarka ba, hasali duk umarnin daka ban sama da shekara talatin ban taba ketare ma ba.

Amma abun da nakeso ka sani hakuri na ya kare, bazan zuba ido kana zaluntar yata ba a banza ni da kai mukaje ta ce aure takeso amma kace baza kai mata ba karatu zatai, yanzu wace riba ka samu ita ba tai karatun ba kuma baka barta tayi auren ba saboda kulafucin san kudi irin naka, to wallahi bazan zuba ido ka salwantar mun da rayuwar yata ba.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now