part 5

1.2K 32 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Assalamu alaikum masoyana nagode sosai da kaunar ku gareni, nagode sosai da wayanda suka dinga kirana suna min ta'aziyya, nagode Allah ya bar kauna, alhamdulillah yau anyi sadakar uku nagode sosai.*

*Dedicated to: kakata Hajiya Talatu, Allah ya jikan ki yai miki rahma, ya gafarta miki zunubanki, Allah ya kai rahma kabarin ki.*

              *20-25*

Caraf ta fada kirjin sa yai sauri ya rungumeta, daidai lokacin da Abba da Umma suka shi go, luuuu ta sume a jikin sa, daidai lokacin Arfan ya iso wajen.

Wata muguwar kutufo yai wa likitan, ya wafceta da karfi daga jikin sa ga rungume ta ana sa jikin yana huci, Abba suman tsaye yai saboda mamaki, Umma ko kuka ta fara shabe-shabe da hawaye.

Abba ne ya karaso yace "menene haka kukeyi? me yake faruwa?" cikin bala'i Abba ya fara fada, likitan ne yai karfin halin magana bakinsa har ya fashe, "wallahi Alhaji ina tsaye anan ina jiran nurse zan shiga tearter, naji kamar an wurgo abu jikina, sai da na duba naga macece ban ma san taba wallahi.

"Karya yake Abba dan iska ne kawai, tayaya zaka rungume mace haka ka sata a cikin kirjin ka, ba wani kunya ko tsoron Allah to wallahi sai munyi shari'a da kai, wallahi bazan bar abun da kai ya tafi a banza ba."

"Haba bawan Allah idan ni ban kararka bisa dukana da kai banji ba ban gani ba, ai kai baka da bakin da zaka ce za kai karata."

"Ya ishe ni kai Arfan ka cika ta mana haka ka rungumeta haka, baka san asibiti bane," sai sannan Momy ta karaso jin shiru basu dawo ba har yanzu, ita ko Umma kuka kawai take saboda sam bata yarda da Arfan ba.

Ita taga lokacin da take gudu ta fada jikin likitan, hankalinta yai mugun tashi, doctor ne yace "Alhaji yarinyar nan fa ba'a hayyacinta take ba." Jin haka Umma ta karasa ta mika hannu ya bata ita.

Shiru yai musu abun da ya bawa kowa mamaki, ya basu yarsu yaki sai nishsi yake kamar wanda yai tsere,  ganin haka Abba ya matsa ya karbeta, luuu ta tafi "innalillahi wainna'ilaihir raji'un!" abunda kawai suka furta kenan.

Doctor yace "koda ta fado jikina ba numfashi a tare da ita, ya bari ma asan abunyi yazo yana haukan kishi akanta, tun da matarka ce ai kayi hakuri a ceci lafiyar ta, tun da a asibiti kake kuma kaga cikin halin da take ciki."

Umma ce tai karfin halin magana "dan Allah likita ka ceto rayuwarta karta mutu." "Kiyi hakuri Hajiya bazan taba masa mata ba yai mun wani sharrin, yanzu kina kallo daga fadowar ta jikina bisa kuskure abun da yake yi."

"Ba matarsa bace kanwar matarsa ce." Cewar Momy  "shakuwa ce a tsakaninsu shi ya sa." Abun yai matukar bawa doctor mamaki amma ya maze, "shi ke nan muje na dubata" shi ko bakin ciki ya cika Arfan, saboda ganinta da yai a kirjin wani shi ne babbar damuwarsa.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now