part 4

1.7K 60 14
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Dedicated to: Ramcy k Aliyu*

*Speacial gift to Nana Aysha Niger*

  
                *15-20*

Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! dan Allah Alhaji ka rufan asiri ka tashi ka temaki rayuwata, dame zanji a wannan lokacin?

A hankali ya miƙe ya ɗebo ruwa me mugun sanyi a firij ɗin ɗakin, ya watsawa Alhaji Ghali da Nauwara lokaci guda suka dawo hayyacin su, banda kyarma ba abunda jikin Nauwara keyi shi kansa Habu a tsorace yake dakiya ce kawai irin ta maza.

Ganin sun dawo hayyacinsu yasa Habu yai maza yaje ya ƙara garƙame ƙofa, saboda kar wani ya sawo kai, hankalin Alhaji Ghali ya gama tashi, duk iskancin sa baya kisa bema taɓa ba, duk wanda ze iya kisa ma tsoronsa yake.

A hankali ya haɗiye wani mugun yawu me ɗaci da ciwo, "waya kashe shi a cikin ku? meyasa zaku kashe shi? ko kunsan babban na hannun daman Baby Chakwai ne?"

"Eh nasani Alhaji" cewar Habu "amma tabbas dabe mutu ba matarka ce zata mutu, nafi kowa sanin halin Baby Chakwai da mummunar aƙida ta tsanar kishiya, baya san a haɗa shi da kowa, wannan shine dalilin dayasa ya turo a kashe matar ka, saboda ya zauna shi kaɗai da kai alhali shi baze iya haka ba.

Kuka Nauwara take da nadamar mugun ƙwaɗayi irin nata wanda ya kai ta ga halaka, da taiwa babanta biyayya da tuni tana nan hankalin ta kwance, amma ga abunda san zuciyarta ya ja mata da zugar uwarta.

Habu ya kwashe duk abunda ya faru ya sanarwa da Alhaji Ghali, amma ya ɓoye masa cewar dashi aka kulle ƙofa, sai ya nuna jinsu yai suna tattaunawa, shi ne ya shigo ya ceceta tunda basu sawa ƙofar mukulli ba.

Jikin Alhaji Ghali yai sanyi ainun, a hankali yace "tabbas Habu wannan ƙullin Baby na ne, amma meyasa zatai haka? meyasa zatai mun haka? kashe Nauwara ai ta sani a bala'i da masifa, mezance da iyayenta? me mutanen gari zasu ɗaukeni? ai har gwara yasa na sake ta.

Haka zalika kashe masa babban yaronsa da kukai kun ƙara samu a masifa, baya yafiya baya haƙuri, yana matuƙar ƙaunar sa bansan dalili ba, kunsan da yaya na same shi? naci wahala sanar har yarda mukai auren jinsi."

_(Duniya ina zaki damu? har alfahari yake yaci wahala kafin ya saɓu ubangijinsa, wannan wace irin masifa ce muke cikin ta, Allah kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu, ka tsare mu ka tsare imanin mu ya rabb.)_

Jin Nauwara tai abun gingirin gim, kamar a kiyama gaban ubangiji ranar da kowa ze faɗi abunda ya aikata yake faɗar wannan mummunar maganar, da kansa yake faɗar kalar ta'addancin da suke aikatawa, kuka ta ƙara rushewa dashi.

"Kiyi haƙuri Nauwara nine na jaza miki, amma kema ke kika jawa kanki,mugun kwaɗayinki na masifa, kinsan cewa bake naso ba amma kika shiga kika fita, ba malamin ku yasa na aureki ba, kwaɗayinki ne yasa na aure ki, dan duk motsin ku a tafin hannuna kuke, kin san duk sammakon mutum wani a tafe ya kwana.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now