LAMRAT 16-20

1K 50 1
                                    

*💖👯LAMRAT👯💖*

💖💋Romantic beby💋💖
           *NIMCY LUV*

  
*just read it before you taken any action✌*




        *➰16-20*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*





  *MAGANIN INFECTION*

*kinemi ɓawon ayaba wanda kikai amfani dashi, ki zuba a bota mai kyau ki zuba ruwa ki rufe ki adanata, wannan ruwan yaza mana shine ruwan tsarkin ki, da yardar allah zaki samu sauƙi wajan ubangiji, domin ƙarin bayani, saiki nemi manyan malamai masana hakan🙏🙌*






💫💫💫💫💫ido ta zaro da mamaki a fuskarta dan batayi tunanin zai riƙeta ba haka kurum, ɗaure face tayi sannan ta kalleshi sama da ƙasa ta taɓe baki kamar bazatayi magana ba saikuma tace.

"malam sakarmin hannu takai karshan maganar tana murgoɗa baki"

Baki yisham ya saka galala kamar ƙaramin yaro, ba maganar ce tabashi mamaki ba sai murgoɗa bakin, tayaya yayi sake lamrat ta rainashi haka, idan tasan wata bata san wata ba, hannu yasa ya murɗe bakin har saida lamrat tayi ƙara saiga hawaye yana zuba dan azaba maimakon bakin ta ya mutu saima ƙara sautin ihun da tayi tana faɗin.

"wayyo allah ni lamrat na shiga uku na lalace ankawoni wajan mugu wanda baisan darajar mata ba, wayyo abba na wayyo ummata, kuna ina zaa kashe maku ni, wlh natsane shi bana sonshi wlh wayyo allah jamaa ku kawo ɗauki wlh ni gidanmu zani"

Wayyo allah gaba ɗaga lamrat ta gama hargitsawa yisham ƙwaƙwalwa, ya rasa mezaiyi mata ya huce, daka ƙarshe ma abin nata dariya ya fara bashi daya tuna fa hadda ƙuruciyya a tare da lamrat kawai girman jiki allah ya bata amma haryau yana lissafe bata huce 17 a duniyya gaba ɗaya, kawai allah ya bata kaifin tunani da basirar yin abune, amma haryau idan tayima abu sai kasan yarinya ce ɗanya, ganin abun nata yaƙi karewa yasa yisham faƙar idonta yayi sama da ita gaba ɗaya kamar ya ɗau ƴar tsana sai parlour daret kan duguwar sofa ya ajjiyeta.

ƙoƙarin tashi take yayi saurin maidata ya zaunar da ita ya ɗau ƙafarsa ya ɗora akan cinyarta ta yadda bazata iya tashi ba.

Joyarda kanta tayi dan batason ganinsa ko kaɗan a idonta, gani tayi bashi da alamar ɗagata, saima lumshe ido dayayi tasa hannu da zummar tureshi kawai maganar ummanta ta ƙarshe ta faɗo mata inda take cewa.

"kiji tsoran allah lamrat kinga gidan miji aka kaiki, banason dai² da rana ɗaya kiyiwa yisham musu tabbas nayarda da tarbiyyar dana baki, ke shedace ko musu bai taɓa haɗani da mahaifin kiba bare faɗa, ko yisham yayi maki abu karki yarda ki muzan tashi adduar mata akan mijinta yana tasiri kisan abin yakeso ki gujewa abinda bayaso, idan yau mune wataran bamu bane"

wasu hayene yake ambaliyya a fuskar lamrat wanda yisham zai iya cewa tunda sokai aure bai taɓa ganinsu a face ɗinta ba, a hankali jikinta ya fara rawa muryar ta fara shaking nutsawa takeson samu amma ta rasa ina zata samu maganar ce ta kufce mata.

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un allahumma ajirni fil musibatu wa'aklifni khairan minha, tabbas zanyi biyaya da abinda kika zaɓamin umma koda hakan yana nufin fitar numfashi nane umma, haƙiƙa nayi rashin gata wanda bazan taɓa mayar dashi ba, bani da kowa saikai abba allah ubangiji ya baka lpa daka ƙarshe ta fashe da wani rikitaccen kuka wanda yasa yisham saurin rungometa bai sani ba, shima idonsa ya kaɗa yayi ja, haƙiƙa rashin umma babban abune shima a rayuwarsa amma yaza suyi da hukuncin ubangiji dole su karɓeshi a yadda yazu musu, a hankali yake buga bayanta yana hura mata iska a kunne.

Gaba ɗaya tashin hankali yasa lamrat fita daka haiyacinta burinta kawai ta samu sassauci wajan ubangiji, jinta ajikin mutum yasa ta ƙara shigewa jikinsa tana maida numfashi, shima lumshe idonsa yayi bai ankara ba saijin saukar numfashin ta da yayi alamar bacce y ɗauke ta bai kula taba saima ƙara gyara mata kwanciyya da yayi a jikinsa.

  A hankali lamrat ke buɗe idonta karaf idonta ya sauka akan agogwan ɗakin karfe 6 dai² adduar tashi daga bacci tayi(allahamdu lillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa'ilaihir nushuru) ido ta zaro ganinta a ɗakin yisham shin hakan na nufin anan ta kwana kome, saurin tashi tayi ta nufi ɗakinta.

Tana zuwa ta faɗa toilet tayi wanka sannan ta ɗoro alwala, bayan tayi sallah tayi azkar haɗe da karatun kur'ani, wajan 8 ta gama komai na abinci kari, kunun gyaɗa tayi sai soyayyen dan kali da miyyar kayan alambu wacce taji hatta, sai soyayyen kwai, sannan shayi mai na'a na'a, wanka ta ƙarayi komai bata shafa ba sabida zafi n da akeyi karar gudun A.C ta ƙaro sannan ta zura duguwar riga ta atamfa wacce ta buɗe ta tsakiyyar gaban rigar gashin ta gyara wannan karan ko ribbon bata saka ba, daman ita batason ɗan kwali a rayuwarta, a parlour sama ta sameshi yana zaune gaban carpet ɗin da aka ajiyye masa abinckn, tun kafin ta ƙaraso yaji ƙamshin ta na turaran ohud mood, bai ɗago ba yaci gaba da danna computer sa, zama tayi kusa dashi ta ɗora kanta a kafaɗarsa tace.

"mrng yaya yisham ta faɗa idonta a kansa"

computer ya ajiyye ya kalleta kanta ya shafa yace.

"mrng too lamrat ykk"

Ta buɗe baki kenan zatai magana taji sallamar zezee ta shigo parlorn.










Kuyi manage🙏🙏

*more comments more typing*

08119237616

LAMRAT Where stories live. Discover now