LAMRAT 136-140

928 66 2
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
         *NIMCY LUV*

@wattpad
Nimcyluv

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

         *➰➰136-140*
       *APOLOGY*



Kallonsa tayi na ɗan lokaci daga shi sai broxer ko riga babu ajikinsa, wadrop ɗin kayanta ta buɗa ta ɗebo kayan baccinta wata golden ɗin riga ta ɗauko wacce ba zata huce iya cinya ba,hanyar bathroom ɗinta tayi tana shiga ta murzawa kofar key,ta ɗauki tsahun lokaci a ciki kafinta murɗa kofar ta fito cikin shigar kayan baccinta.

Turus tayi zuwa yanzo tayi tunanin ya fita domin tana sani ta ɓata lokaci a cikin toilet ɗin,a zaune ta ganshi ya jawo laptop ɗinta yana latse² kome yake dobawa ohhhu?wajan mirrow ta nuta ra zauna lotion ta shiga shafawa tana ƙoƙarin shafawa a cinyarta taji numfashinsa daf da ita,wata irin faɗowar gaba da tsorone suka dirar mata lokaci ɗaya da kewa tayi,haɗe da yin banza dashi kamar bata gansa ba lotion ɗin ta ɗauka da niyar ci gaba da shafawa taji yasa tattausan hannunsa ya riƙe nata bata ɗago ta kallesa ba kamar yadda shima bai kalleta ba,tashi tayi da niyar barin wajan tayi yayi saurin tiƙeta haɗe da bai data wajan zamanta,kamar daga sama taji saukar hannunsa a cinyarta ya fara shafa mata lotion ɗin,saurin runda ido tayi lokaci ɗaya taji tsigar jikinta na tashi ya salam kawai take cewa cikin ranta,wannan wanne irin abune? shin wannan bai wace kome?take ta tunanin cikin ranta tabbas da ace Yisham ra'ayin tane da ayau sai taga ƙarshansa.

A zarihi mai yake shafa mata amma a ba ɗini shi kaɗai yasan mai ya keji,shi bada niyar hakan yazo ba jikin sane ya fara rawa hakan yasa yayi saurin ɗauke hannunsa a jikin wajan 3minutes ya samu yayi control kansa,turare ta shiga fesawa jikinta mai daɗi da kwantar da hankali,a wannan lokacin dukkan abinda take akan idonsa take sai yanzo ya lura da idonta da suka kumbura sukai ja,tambayar kansa ya fara to ita meye da muwarta da zatai kuka aishi yake da ikon yin hakan ba ita ba infact ma ita bata damu da raba son da akai ba to meye nata na kukan?tashi tayi da niyar zuwa bed ɗinta maganaraa ta tsinkaya.

"saying sorry is the purest cure of all heart aches and heart breaks! Admit to yourself that you have done wrong and say sorry. It does not only touches the heart but also touches the soul. It's the greatest thing to do that will give you the greatest feeling to enjoy".

Tsayawa tayi cak daga inda take bata ankara ba taji wani hawaye masu zafi suna bin fuskarta,ganin ta tsaya yasa ya biyo bayanta yazo daf da ita hannunsa ya saka duk biyun ya dafa kafaɗarta ya ƙara cewa.

"bansan mezan ce maki har ki yarda da magana taba,amma tabbas ki sani wannan hanyar da kika ɗauko bamai bollewa bace tunda baki sona kin tsaneni kawai ki kasheni ki huta Lamrat ina ganin hakan zai maki daɗi,nidai rabuwa dake nace bazan ba zaki iya dukkan abinda kikeso"yana gama faɗin hakan ya fice ya bar mata ɗakin.

Wani irin kuka ta fashe dashi haɗe da kiran sunan Allah,wani irin ciwo ta keji a ranta shin ita yaya za tayi taje ta cewa Abba tana son komawa gidan Yisham kome?tabbas ta najin Yisham a ransa bata son lokacin da hakan ya faro ba,a yau ta hango zallar soyyayarta a idonsa soyyaya bata wasa ba,soyyayar da shikansa basai yana yi mata ita ba,da wannan tunanin bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Abu kamar wasa tun Yisham na zubawa Abba ido akan ya bayar masa da matarsa amma shuru kakeji,gaba ɗaya ya wahala ya gaji bai taɓa tunanin yana son kasan cewa da ita ba sai yanzo duk wata hanya da zaibi gaya Abba Umma ta toshe,kullum bashi da aiki sai turawa Abba saƙo ta email ɗinsa na ban haƙuri da yafiya akan bazai ƙara ba,yau wajan wata 5 kenan amma babu replay hakan ba ƙaramin ta yarwa da Yisham hankali yayi ba.

Yanzo haka suna da wata 7 da zuwa gida domin shi bazai iya tafiya babu itaba,tashi yayi daga kwancen da yake da sauri ya fito ya fara taga step ɗin benen yana zuwa ya tarar da Umma zaune a parlourn don amfara shirin bikin Meenat da Mujaheed saura kwana 5 da tuni anyi aka samu matsala shine aka ɗaga,yana zuwa ya zube a gabanta haɗe da ɗora hannunsa akan ƙafarta cikin zafin rai da kuma zallar damuwa ya fara magana.

"Umma kuji tausayi na kinaso ki rasani?wallahi idan baku bani matata ba ina gaf da rasa numfashi na"ya faɗi hakan muryarsa na rawa ana haka Abba ya ƙaraso daman ya najin abinda yake faɗa.

Gyara zama Umma tayi sannan tace.

"kaida baka sonta to meye amfanin komawarta kawai ta kaddar sakinta muke jira"

Da sauri ya ɗago kai ya kalleta tabbas da ace ba Umma ce tayi masa wannan maganar ba dashi kaɗai yasan abinda zai aikata,cikin rawar murya yace.

"wallahi Umma inason matata itama tasan da hakan,Umma bazan iya rayuwa babu Lamrat ba"

Abba ne yayi murmushin gefen baki kana ya dobi Yisham yace.

"mufa babu ruwanmu bamu rabaka da matarka ba,kaine baka sonta shiyasa ba kabi hanyar da zata koma ba"

Juyowa wajan Abba yayi yace.

"wacce hanya Abba?zuwa yanzo hanya ɗaya ta ragemin itace mutuwa idan na matu saiku samu damar bata wani mijin"

Sun kula ya fara fita a haiyacinsa dan haka Abba yace masa "jeka ka nemi yardar matarka,idan ta amince zata bika shikenan haka mukeso ai"

Da sauri ya tashi har yana haɗawa da gudu wajan yin part ɗin Lamrat,dukkan abinda suke a kunanta sosai take kuka tana tausayin kanta amma tabi tausayinsa,kuka take na ƙonan zuciya mai tafiya da tausayin dukkan wanda ya saurara,hannu tasa ta dafe kanta dake barazar tarwatsewa gida biyu, tana jikin ƙofar taji alamun zai shigo yana gaf da shigowa tayi saurin rufe ƙofar haɗe da murza mata key.

Sorry guys lamrat zai maku bye-bye

Vote#
Comments#
Shere#

      Wattpad pls and pls i need ur comments and vote.

Inason kowa ya faɗi raayinsa akan wannan page ɗin,shin idan kece Lamrat wanne irin mataki zaki ɗauka?

Sai najiku

LAMRAT Where stories live. Discover now