LAMRAT 96-100

880 50 2
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
       *NIMCY LUV*

       *➰➰96-100*

         *SAVE THE DATE 2*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

    _lamrat fans nagode da haɗin kanku, kuma inajin daɗin hakan sosai,domin naga kuna ta siyan book ɗina na (sai na aureta)ina alfahari daku,dole na saku cikin masoyana kuma ƴan uwana tnx alot._


💫💫💫💫💫Wata irin faɗuwar gaba Yisham ya ji,lokacin da Abba ke yi masa magana,ta ya ya zai iya auran wata Lamrat,yarinyar daya tsana sama da komai nasa,"no i can't marry her,bazan iya zama da wannan yarinyar as my wife ba."

   Jin shuru ya yi yawa ya sa Abba kallonsa,sannan yace.

"Captain ka yi shuru ba ka ce komai ba,na ga dai tuntuni ka gama gidanka,to kuma meye abin tunani?"

  Gyara zama yayi sannan ya ɗan kwabe fuska yace.

"Abba ni fa ba auren ne bana so ba,a sauyamin wata matar mana,ka ga Lamrat karatu take,kuma gaba ɗaya ma nawa ta ke ta yi ƙarama da yawa".

   Tunda ya fara magana Abba ke kallonsa,ya na son fahimtar wani abu a tsakanin Yisham da Lamrat finally yanzo ya gane,ɗan kishin giɗa yayi a jikin sofa,sannan yace.

   "Amma dai na san baka manta da al'ƙawarin daka ɗaukarwa mahaifiyar yarinyar nan ba,da ka san ba za ka iya ba tun lokacin sai ka ce kana da wacce za ka aura,ba na son wani surutun banza ka je ka fara shiri end of this mounth you getting marry,kuma kaje ka sami Lamrat ɗin domin ka ji abin da ta ke buƙata".

     Jiki babu ƙwari ya tashi ya shige part ɗinsa,yana zuwa ya huce bathroom kayan jikinsa ya cire sannan ya sakarwa ƙansa shower,ya ɗauki wajan 10minutes a haka ruwa na sauka a kansa,gaba ɗaya ya rasa sukuni a ransa da zuciyarsa gaba ɗaya,ya rasa me ya ke ji game da auran Lamrat,gaba ɗaya ya manta ya ce da Abba mujaheed ke sonta ba shi ba,no ta yaya kuma mujaheed zai zauna da wata Lamrat a matsayin mata,zancen banza kenan,wani numfashi ya fitar mai zafi,ji ya yi kasala ta saukar masa,fitowa yayi a bathroom ɗin ya zura wata farar jallabiya ya faɗa saman bed ɗinsa yana tunanin mafita.

Lokacin da Abba ya gama yi mata bayani,ji tayi gaba ɗaya garin ya fara juya mata,wani dishi-dishi take gani,zuwa yanzo ba ta fahimtar abinda Abba ke gaya mata,can taji yace.

"Tashi ki je Lamratu Allah yayi maki al'barka kinji."

   Da taimakon Allah da na Meenat ta samu ta shiga ɗaki,tana zuwa ta murɗa key,zama tayi kasan capert ta fara kuka mara sauti,me ke shirin faruwa da ni ne,wanne Yisham ɗin Abba yake nufi zai auramin?ta ya ya zan iya zaman aure da mutumin da na tsana sama da komai na rayuwarta,tunawa tayi da Daddy tun jiya da su kayi waya yace mata yana hanyar dawowa,wayarta ta ɗauka tayi dailing number amma swich off,cilli tayi da wayar,ta ɗauki tsahon lokaci tana kuka mai tsuma zuciya,sai da taji kanta yana yi mata ciwo sannan ta tashi ta yi al'wala ta yi sallah,sanan tabi bed ɗinta ta kwanta asuba ta gari Lamrat.

   Lokacin da labari ya iskewa Huda ji ta yi gaba ɗaya zuciyarta ta tsaya da komai.

"What Yisham Lamrat za ta aura?na yaudari kai na naso mutumin da bai san ina yi ba,tabbas ba zan taɓa da ina sonka ba Yisham koda hakan zai zama ajali na,wallahi da ace ba Lamrat ba ce babu abin da zai hana na soke auran nan,na shiga uku ni Huda ta ya ya zan iya zama naga wanda nakeso he getting marry to someone else not me,wayyo Allah,na shiga uku".

   Jin alamun tafiya ya sa ta yi saurin haɗiye kukan,fuskarta ta share sannan ta fito parlour inda tabar Meenat da Shatuu, Shatuu ce ta kalleta sannan tace.

"sannu Huda da aiki,sai hakuri fa"

Kafin tayi magana Meenat tace.

"Me ya sameta kuma?"

  Cikin sauri Huda tace. "uhm babu komai kin san Shatuu da neman magana ai".

   Tunda su ka fara magana Lamrat bata ce komai ba,ta zura hannunta a tsakanin cinyoyinta,ɗayan kuma ta harɗe hannunta a kirji,ta zurawa ƙofa ido,ita kaɗai ta san me take tunanin a lokacin,mafita take nema wacce zata taimaki Huda Amma ta rasa,ita tasan bata son Yisham amma idan ta tuna wasiyyar da Abba ya bata ya ce inji Mummy sai ta ji ba zata iya gojewa auran Yisham ba,amma tasan dole akwai wani babban al'amari,ta gama fahimtar Huda domin tasan tana mutuwar son Yisham kawai ta yi shuru ne saboda bata da mafita.

A 1 week letter

  Komai na shirye-shiryen auran Lamrat da Yisham ya gama kammala lokaci kawai ake jira wanda zuwa yanzo saura sati guda a fara shagalin biki.

Mujaheed kowa hauka ne kawai bai yi ba lokacin daya samu labari,ya yi kuka har ya gaji,gaba ɗaya daina fitowa yayi domin bazai iya ci gaba da kallon Lamrat a matsayin matar yayansa ba,tun abin na damunsa har yayi hakuri yaci gaba da addu'a domin neman zaɓin Allah,ya fito yana shirye-shiryen biki dashi.

  A ɓangaran ango kowa ba'a cewa komai,domin ba zaka taɓa fahimtar abin da ke zuciyarsa ba,yana cikin farin ciki shi kaɗai yasan abin da ke saƙawa, ya ajjiye komai har zuwa lokacin da za'a kai amarya.

Har ya kwanta sai ya tuna umarnin Abba,wando ne a jikinsa three qauter,sai farar t.shirt,tashi yayi ya sako daga bed ɗinsa,fita yayi part ɗinta ya nufa,ya na zuwa dai-dai kofar ya tsaya ya saka hannu ya murɗa kofar cikin sa'a ya jita a buɗe,fitowar ta kenan daga bathroom daga ita sai towel wanda ko cinya bai gaba rufe mata ba,jin gina yayi a bayan kofar ya saƙale hannayensa a kirjinsa,jin an buɗe kofa tayi saurin juyowa karaf suka haɗa ido.

LAMRAT Where stories live. Discover now