LAMRAT 141-145

967 54 1
                                    

️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
       *NIMCY LUV*

@wattpad
  Nimcyluv

       much guys yanzo kafce ya bar book ɗin Lamrat ya koma na Sai na aureta👯‍♀️👯‍♀️👯‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

        *➰➰141-145*

*FINALLY LAMRAT AND YISHAM THEY  ARE TOGETHER*

Turus yayi ganin kofar a rufe kuma yaga lokacin data rufe,hannu yasa ya fara knoking amma no responding abu kamar wasa haka ya dinga bugon kofar amma fur Lamrat taƙi buɗewa,ganin bazata buɗe ba haka yaja jikin yayi hanyar part ɗinsa zuciyarsa nayi masa wani irin ciwo wanda babu mai iya yi masa maganinsa sai Lamrat,da wannan tunanin ya shige part ɗinsa.

Su Umma da Abba najinsa yana bugo haka suka dinga dariya sosai daman sunsan za'a rona,a zahiri Umma dariyar kawai take amma can ƙasan zuciyarta tana tausayawa yaronta halin da yake ciki itama tana buƙatar komawar Lamrat ɗakin mijinta,amma babu yadda zatai wannan shine kaɗai gatan da zataiwa Lamrat amatsayinta na Uwa a gareta.

Tofa abu yayi abu an shiga wasar ƴan ɓoya tsakin Lamrat da Yisham,indai yana gida ba zata taɓa fitowa waje ba sannan ta kulle kofarta da key,yayi bugon yayi begging yayi rarrashin amma fur taƙi buɗewa,haka ya ƙarɓi number ta wajan Meenat kira babu irin wanda bai ba text kam idan yayi goma a rana yayi kaɗan.

A duk sanda yake buga kofarta yana rarrashin ji take tamkar yana tafiya da bugon zuciyarta,haka zata shige toilet tai ta kuka tamkar zata haɗiyi zuciya,ita kaɗai tasan halin da take ciki aduk numfashin da zatai to baya tafiya saida soyyayar mijinta,sosai take jinsa a ransa amma babu yadda zatai dole ta nunawa Yisham kuskurensa.

Masha Allah yau take juma'a yau aka fara bikin Mujaheed da Huda,sai Kuma Meenat da Faisal,amaraye sunyi kyau har sun gaji da haɗowa musamman Meenat wacce ke kama da Yisham kaya iri ɗaya suka saka kasan cewarsu ƙawaye,ƙarfe 5 dai² aka tashi kowa yayi hanyar gida.

Cikin nutsuwa yake dreving na car ɗinsa,ango kenan yasha gezner mai kalar ash wacce ta amshi skin ɗinsa,daka ganshi kasan yana cikin farin ciki da kwanciyar hankali kaf damuwar zuciyarsa ta yaye,a hankali ya kalli amaryarsa wacce take jin gine jikin sofa ɗin kujerar,ɗan murmushi yayi sannan yace.

"amarya amsha ƙamshi lafiyarki lau ki kayi shuru haka?"

Jiki a sanyaye ta kalleshi tace.

"lafiya nake na ɗan gajine"

Dariya yayi still hankalinsa nakan toƙin da yake yace.

"a lallai bari nayi parking sai nayi maki tausa ko"

Ɗan conu bakinta tayi gaba tace.

"a'a Yaya pls kaini gida kaji"

Ɗan cije lips ɗinsa yayi lokaci ɗaya yaji soyyayarta ya fara shigarsa,wanda yake ta addu'ar hakan dan zama da mutumin da bakaso akwai damuwa,baice da ita komai ba yaci gaba da dreving nasa.

*****      ******      ******

Abba kam ya dai-dai ta ƙanwar matar wacce ake kira da Sumaiya sosai suka fahimci juna,acan inda suke aka ɗaura masu aure suka tare yanzo haka suna da wata 4 da auren inda ake saran Sumaiya nada juna biyu.

A cikin satinnan ya gama shirin komai domin zaman can ɗin ya ishesa gaba ɗaya hankalinsa yayi gida,babu wacce keson gani sama da gudan jininsa Lamrat,cikin satinan suke shirin zuwa siyyaya kam yayiwa Lamrat kamar hauka hadda kayan bebies a tunaninsa yace yanzo Lamrat ta kosa haihuwa(😛lol Abba ka dawo ka tarar da cakwakiya).

Yau asabar karfe 10 na safe jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa najeria garinsa na haihuwa,wani sanyi ya keji a ransa koba komai yau zai kwanta a ƙasarsa yau zaiga Inna yau zaiga Lamrat,juyawa yayi yaga Sumaiya na sharar bacci gaba ɗaya ta kwanto jikinsa,ɗaya ɓangaran kuma ƙanwar Sumaiya ce Khadija sai kuma kakar Lamrat ta wajan uwa Hajiya lubabatu,Abba Allah ya saukeko lafiya.

            ********

Karfe 5 dai² aka fara tafiya dinner amare sunsha kyau sanye suke da kaya gwon mai kalar red and golden anyi masu make up idan kagansu saika su ƙara ganinsu sabida kyansu.

Babbar ƙawa kuma ƴar uwa Lamrat ita tasha kwalliya mai tsari da ma'ana,wata duguwar rigace a jikinta mai kalar pink da blue an tsaga rigar daka bayanta ta ɗaura head mai kalar blue sai hand bag ɗinta itama blue sai wani gutun mayafi shima blue wanda ta ajjiye a gefen kafaɗarta.

Amare sun hallara an fara cashewa a wajan biki,guri yayi guri jama'a sun cika sai kayan sojoji kake ganin sabida angon Meenat shima captain ne,Meenat ce ke rarraba ido ganin lokaci yaja ba Lamray babu Alamarta.

Sako ƙafarta kenan cikin hall ɗin hakan yayi dai-dai ta wata waƙa da D.j ya saka mai suna wait for me,cikin sanyi tasa ƙafarsa da niyar shiga taji ansaƙalo hannunta cikin na wani,da sauri ta juyo taga waye nan idansu ya sarƙe cikin na juna saurin ɗauke kai tayi sabida yadda zuciyarta ke mata bugu,ba ƙaramin yayi ba sanye yake da gezner pich colour yasha babbar riga kayan sai gyalli suke,ganin ta tsaya taƙi tafiya yasa ya sunkuyo saitin kunanta yace.

"yadai ƴan mata?yaya ki kaga mijin nakin?"

Shuru tayi masa batai magana ba,sai bugun zuciyarta ke ƙarowa tabbas da ace tasan zaizo babu shakka da ba zata zoba,hannunta ya mstsa da ƙarfi harta saki wata ƴar ƙara,ɗagowa tayi ta kalleshi dariya yayi mata sannan ya kashe mata ido cikin sanyin murya yace.

"Madam lets go"

Tafiya suka fara a hankali tamkar sune amaren har suka iso cikin hall ɗin,D.j ne ya fara maganar cikin kwarewa ta aikinsu yace.

"yau akeyinta gobe sai labari ga yayan ango da amaryarsa sun iso,abada waje wannan lokacin kane kowa yayi nasa ya gaya"

Murmushi kawai Yisham cike da jin daɗi babu abinda ke masa daɗi irin ya juya yaga sayibarsa Lamrat wacce yayi kwanaki ko watanni bai ganta ba,tsayawa yayi ya ciro kuɗi ya fara liƙin ƴan dubu-dubu sabbi,ganin Lamrat zata gudu yayi saurin riƙe kugunta ya fara rawa da ita a hankali tamkar yana juya beby,haka akai dinner cikin jin daɗi karfe 10 dai² aka tashi fakar idonsa tayi ta shige cikinsu Shatuu,haka yaita nemanta yarasa tana koƙarin shiga mota taji ankama hannunta an fara janta da sauri har zuwa wajan motarsa buɗewa yayi ya dannata cikin motar shima ya shiga,haka su Shatuu suka dinga dariya harda riƙe ciki.

Motar ya shiga ya zauna sunkai wajan 10minutes a haka har aka fata tafiya,can ya ɗago kai ya kalle sannan yace.

"Lamrat"a hankali ta ɗago ta kalleshi mamakin yadda idonsa ya sauya lokaci ɗaya yayi,langwabar  da kai gefe yayi haɗe da ɗan turo bakinsa like beby hakan ba ƙaramin kyau yayi masa ba,sunkuyar da kai tayi ba tace komai ba shine ya ƙara magana.

"ayau kuma a yanzo nakeso ki yanke hukunci akaina,koki koma gidana ko kuma ki rabani da nunfashi na gaba ɗaya ki huta"

Hawayene ya fara sauka a idonta shuru tayi dan bata da amsa,kalleta yayi cike ta tausayi amma ya fita abin tausayi yace.

"banson wannan kukan ban maki dole ba,amma ya kamata kiji tausayi na Lamrat kin yanke hukuncin da ba kisan komai akai ba"

Rasa abin faɗa tayi tabbas tana buƙatar mijinta,sannan ƙimar ko wacce mace gidan mijinta sosai ta fara kuka wanda bata san kona mene ba sam bata san kona mene ba,ya daɗe yana kallonta ya najin kukanta kamar ana zuba masa dalma a zuciya da ƙyar ya buɗe baki yace.

"menai maki ni pls,ki daina banso"

Bata san lokacin da zuciya ta ɗebe taba ta faɗa jikinsa haɗe rushewa da kuka,shi dariyma taso bashi bakinsa yakai dai-dai kunanta yace.

"kina kuka kamar wata beby"

Ɗagowa tayi haɗe da turo bakinta waje,hannu tasa ta daki kirjinsa sannan ta ƙara kwantar da kanta a kirjinsa.

More Comments#
Vote#
Remain 1 page

LAMRAT Where stories live. Discover now