LAMRAT 91-95

803 43 1
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

*💖💋Romantic story💋💖*
         *NIMCY LUV*

      
       *➰➰91-95*
 
      *SAVE THE DATE*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

💫💫💫💫💫Zaro ido yisham yayi jin abinda doctor ya faɗa.

Gyara zama kaɗan yisham yayi yana tunanin maganar doctor,ko wacce mace akwai yanayinta ita kuma ta kalar kenan ko yace halitta,kallon doctor ɗin yayi yace.

"shikenan doctor zan duba maganarka,pls koda su abba sunzo kada ka gaya masu conditon ɗin da lamrat ke ciki pls"

Murmusawa doctor yayi kaɗan,sannan ya miƙawa yishan file ɗin hannunsa yace.

"baka da matsala da hakan,amma dole a kula domin hakan zai iya afecting na rayuwarta"

Doba file ɗin yisham ya fara,sai da ya gama sannan yace.

"zan iya ganinta yanzo?"

Miƙewa doctor yayi haɗe da yin gaba yace.

"ok biyoni zuwa ɗakin" yana gaba yisham yana binsa a baya,har suka ƙaraso wani special room,kofar ya buɗe ya shiga yisham ya taka masa baya.

A kwance suka sameta tana bacci,numfashinta sai sauka yake a hankali,ta ƙara fari sannan ta rame kaɗan wai duk a kwana ɗaya,doba ta doctor ya ƙara sannan sukai sallama da yisham ya fita,kora mata ido yayi bayako kiftawa,idonsa yaja ya lumshe a hankali yana sauke numfashi.

A hankali take buɗe idonta dishi-dishi ta fara gani,daga ƙarshe idonta ya buɗe tar a kansa,karaf suka haɗa ido,sun ɗau lokaci a haka sannan ta ɗauke nata idon ganin bashi da alamar ɗauke nasa.

"Sannu ya jiki?" shine abinda ya faɗa

" Uhm" kawai tace mai sannan taja idonta ta rufe.

2 mounth

Su lamrat suna shekarar ƙarshe na kammala secondry school,komai na alamun girma ya gama baiyana a jikinta,tafi meenat komai saidai meenat ta nuna mata tsayi,umma kowa sam bata barin zama babu hijab ba,hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa lamrat ba,sabida wani irin kallo da mujaheed ke mata abin yana takura mata,

"yisham daman na kira ka domin na faɗa maka cewa,ƙarshan watan nan za'ai auranka da lamrar".

Comment#
Vote#

LAMRAT Where stories live. Discover now