LAMRAT 61-65

1K 51 0
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
         *NIMCY LUV*

*Read before you taking any action✌🏻*

      *➰➰61-65*

     *THE NEW HOUSE*


    *Masu kirana da masuyimin messges nasan ko suwaye,saka maƙon sunjini shuru ina gdy mara misaltuwa a gareku,hhhh Lamrat tana gdy da saƙon ta'aziyya da kukaiwa mahaifiyyar ta lol*



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

💫💫💫💫💫Bai tsaya ko inaba sai hospital,daret likitoci suka amshi lamrat suka fara dubata,wata nurse yisham ya samu yayi mata bayanin komai akan ta kula da lamrat kafin gobe ya dawo,ya bata kuɗi maso yawan gaske tana godiya, uhm kawai yace mata yabar wajan ya ƙoma gidansu lamrat.

Yana zuwa ya tarar har anyi mata sallah za'a kaita makwamcinta na gaskiya,shine ya fara kama makarar sannan Daddy sai abba sai kuma wasu ƴan uwan da sukazo,haka aka kaita babu wanda zaice yaga kukan Daddy addu'a kawai yake zabgawa matarsa halinta na gari ya bita, namijin duniyya kenan dan ko yisham saida yayi kuka da yaga angama sakata a kabarinta amma banda Daddy haka akaci gaba da zaman maƙoki.

Washe gari da safe yisham ya shirya ya tafi asibiti yana zuwa ya tarar da nurse ɗin, tayi saurin zuwa wajansa tace. "Sir daman yanzo ake shirin kiranka tun jiya taƙicin komai sai kuka take tana kirar Mummy ga zafin zazzaɓi yaƙi sakinta ta hana kowa ya taɓa ta bare ayi mata injection yanzo ma haka tun safe take bacci tana gaf da tashi" kallon matar yisham yayi yace. "ok thank you"sannan yayi gaba ya tafi room ɗin da aka kwantar da ita,yana shiga ya ganta a kwance tana bacci numfashinta yana sauka a hankali,gani yayi ta ƙara fari kamar babu jini a jikinta gashin kanta ya barbazo ya rufe mata fuska sabida tsawonsa,kara sawa yayi gefen gadon ya zauna sannan yasa hannu ya ɗaga ta cak, ya goyata a bayansa,sannan ya gyara gadon ya jin gina pillow a gefen gadon ya sauƙota ya kwantar da ita a wajan pillow ya tattara gashin kanta ya ɗaure da ribbow ɗinta da ya gani a wajan,tsayawa yayi ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana ƙare mata kallo sai yanzo yake ganin kamarta data mahaifiyyarta,farace irin farinnan mai kyau bacan ba,tana da hanci dogu wanda ya tsaya a tsaitin bakin ta,gashin idonta zara-zara na girarta ma haka saidai shi a kwance yake kamar anyi jagira sabida sham ɗinsa gashin baƙine sosai,kwayar idonta kuma abin mamaki ba baƙa bace baron ce kamar an ɗiga mata wani abun dan haka ba kowa ke iya haɗa ido da ita ba,kallonsa ya mayar ga bakinta ƙarami ne sanan lips ɗinta suna da ɗan ƙauri gasu kalan pink,gashin kanta har gaban goshi,saida ya gama ƙare mata kallo sannan yaja tsaki yace.

"Auran irin wannan matan ai hatsarine wallahi,yarinya kamar aljana haba,shikam zai nemi sulhu da ita tayi karatunta sosai shi zai zaɓa mata miji dai-dai da ita amma shi sam baya ra'ayin aurata,murmushi yayi yace wannan kyan naki ai ba abin mamaki bane Mummy balarabiya ce,Daddy kuma shuwane dole kiyi kyau ai,yana tsaka da tunaninsa kamar daga sama yaji tace. "stop looking at me haka mana" zaro ido yayi wanda baisan yayi shiba,sannan ya haɗe rai yace.

"mezan kalla to,keda namiji a guna ai duk ɗaya,kitsaya iya matsayinki ok" uhm what ever dai ka kalle ni koma mece ni,nika kaini gida Mummy na gida tana jirana danna san zuwa yanzo sungama shiryamin party  ok"

Gabansa yaji ya faɗi kardai ace ta manta abinda ya faru da Mummy shikowa daya shiga uku,haɗa rai yasakeyi sannan ya joya yana kallan idonta sai kuma yayi ƙasa danasa idon,yace. "wanne party kuma bayan ana partyn kika faɗi baki da lafia kin fiya shirme kedai"

LAMRAT Where stories live. Discover now