LAMRAT 71-75

857 48 1
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
*NIMCY LUV*


*➰➰71-75*

*ABOUT THE NEW SCHOOL AND CHALLANGES 2*


*Read before you taking any action✌🏻*



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


*My frnds Dan Allah inason ko wanne gruops na buɗa naga wannan page ɗin yana yawo this is my wish*




💫💫💫💫💫Wajan 5minutes suka jiyu Yisham ya fasa ƙara,gaba ɗayansu suks miƙe tsaye suna tunanin abinda ya sameshi yake wannan ƙarar,cikik sauri Mujaheed ya fara taga step ɗin benen Meenat ta rufa masa baya cikin sauri,itakam Lamrat waje ta samu ta zauna kan sofa tana murmushin gefen baki.

Suna zuwa suka sameshi a zaune akan ƙafarsa sai haɗa gomi yake na'a zaba, da sauri mujaheed yayi kansa haɗe da jan ƙafar tasa,saurin rontsa ido yayi yanajin wata a zaba na rasa kwakwalwarsa da yana da iƙon yin kuka da babu shakka saiya yishi,zaro ido mujaheed yayi ganin yadda ƙashin ƙafarsa ya fito,sannan yabi wajan da kallo yace.

"meenat menene wannan a wajan?" sauke numfashi meenat yayi haɗe da cewa. "brother i think karkashine da mai aka kwaɓashi"da ƙarfi yisham yace. "karkashi!" shuru mujaheed yayi yana tunanin mai ya kawo karkashi wannan wajan ganin bashi da amsa yaja bakinsa yayi shuru,Yisham ne yaja ƙafarsa da ƙarfi harsai da tayi ƙara alamar ya gyara ta sannan ya kallisu meenat yace. "Karku sake naji kun gayawa Mami karkashine ya faɗar dani,kawai kuce tuntube nayi,wallahi naji maganar uhm, i can't emaging what am gonna do you" mujaheed ne ya taimaka masa ya kwanta akan gado.

Yana daɗe yana tunanin kalolin a zabar da zai mata,yasan cewa babu shakka itace ta aikata masa wannan abun,yarin ya baki da hankali bakisan wane yisham ba,wallahi sai nayi baki abinda ko ganina kekai saikin kusa fitsari a wando,idonsa yaja ya lumshe yana jin zafin da ƙafarsa take masa,amma shi sam ba ita bace a gabansa burinsa bai huce yaga Lamrat ba.

*Two weeks letter* sosao suke karatu babu ƙafar yaro,meenat da lamrat ajinsu ɗaya basa so a rabasu a koma mene,wajan zamansu ɗaya komai nasu tarane,itama meenat da yake tana da kyau dai² sakamaƙon Mami bafulata nace,time ɗin break ne yayi dan haka suka fita waje,suka zauna a wajan da aka tana da dan cin abinci,meenat ce taja coler abincin tana buɗawa taga gidan farko soyayen dan kaline wanda yaji kwai,na biyu kuma farfesun kayan cikine wanda yaji kayan ƙamshi,na uku soyayar shikafa ce wacce taji kifi da kayan lambo,meenat babu ɓata lokacin ta fara cin abinci,can taga lamrat bataci tace.

"ke bazaki ci bane"ɗan tabe baki tayi tace" kedai ci kawai inada abin da zanci" tana faɗin hakan ta ɗauko wani ƙaton cake a jakarta kana ganin cake ɗin nan kasan yaji kayan haɗi,kaloli uku ne a jikinsa ko wacce kala daɗinta da banne,kallonta meenat tayi da mamaki tace.

"ina kika samu cake haka?" murmushi lamrat tayi tace. "kedan idan zakici kawai ciki bana son tambaya ni" suna cikin yin break huda ta ƙarasu wajan,dan itama makaran tar suke hadda su shatuu,nan suka ci gaba da cin abincin da hirar karatu wasu suce sun gane wasu kowa a ƙasin hakan, tunda suka fara magana lamrat bata ce komai ba sai yanzo. "daman ina zaku gane karatu kuna shegen surutun da bashi da amfani"ta faɗa tana yin hanyar class.

Huda ce ta kalli meenat tace. "wai meenat ko a gida lamrat bata magana ne?" dariya sosai meenat tayi tace."wannan ai miskilace ba'a gane gaban ta bare bayan ta,idan kikaga tayi magana hadda dariya to mujaheed ne a wajan,ko Mami" huda tayi ta gomi tace. "nikam inason naga tana magana a cikinmu walahi" sai lokacin shatuu tayi magana dan itama surutu bak dameta ba tace. "rashin fahimta ne huda,amma ai tana magana kawai dai kun fiya surutu ita kuma bata shi shiyasa kuke ganin bata son magana".

Washe gari tun safe suka shirya zuwa makaranta,amma lamrat bata fito ba,can meenat ta hango ta tana sakkowa daga step ɗin benen hannun ta ɗauke da wani abu a leda,sam meenat bata damu da sanin kome ne ba,Wajan Mami lamrat ta nufa tana zuwa ta rungometa tace. "Mami na ayi mana addu'a sai mundawo" addu'a mami ta bisu da ita da kuma fatan Alkairi.

suna fita suka ga ba motar da aka saba kaisu bace,tsayawa lamrat tayi tace meenat taje taga waye,tana zuwa taga yisham ne ya saka airpies a kunnannsa da shi,motar ta buɗe ta shiga gidan baya,lamrat na ganin haka itama taje zata shiga gidan baya kenan taji yace.

"kee!waye zai zama driver ku?, dalla malama dawo gaba ni inada abinyi" bata kulashi ba dan yau bata son magana kwata-kwata dan haka ta buɗe ƙofar gaba ta shiga ko ƙarasa zama batayi ba yaja motar a goje yabar wajan.

Suna isa motar su huda na tsayawa,har wajan motarmu tazo tana jiranmu,tunda ta ƙarasu wajan ta zubawa yisham ido ko ƙiftawa batayi,harsu lamrat suka fito bata daina kallonsa ba,mtwws lamrat taja tsaki tayi gaba ita kuma meenat taja hannun huda sukabi bayan lamrat.

Zaune suke suna yin break,yauma lamrat ko kallon abincin batayi ba ta ɗauko cake irin na jiya da kuma apple tana ci,kallonta shatuu tayi tace. "kekam sam bakison abinci,amma duk da hakan bakya rama saima wani girma da kikayi,ni har tsoro girmanki yake ban wallahi,gaba ɗaya kinfimu komai"gyara zama meenat tayi tace kema dai shatuu kya faɗa,ai inaga da wuri zatayi aure ta barmu da biro da takadda musamman yadda naga yaya mujaheed na rawar ƙafa may be dashi za'ai"ta gomi huda tayi kana ta kalli meenat tace.

"wai shima wanda ya kawoku yayan kune,naga kuna kama,pls ki gaida shi"mtwwss lamrat taja tsaki haɗe da mikewa ta bar wajan.

A hankali take tura ƙofar ɗakin tana shiga taga babu kowa hamdalla tayi,sannan tayi wajan frizer tana buɗewa taga cake,dariya tayi sannan tasa hannu ta ɗauka haɗe da daukan apple,miƙewa tayi dan fita a ɗakin saurin sakin kayan tayi haɗe da jada baya,ganinsa tayi jingine a jikin kofa ya harɗe hannunsa a ƙirji...

(more comments more typing💁‍♀️🤷‍♀️daman kwana biyu a sama nake jina,karku manta da shere sabida wasu fans ɗin)

LAMRAT Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon