LAMRAT 131-135

884 53 0
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💖💋
           *NIMCY LUV*

@wattpad
  Nimcyluv

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

         *➰➰131-135*
*HEART BROKED ESPECIALLY YISHAM*


Ummace fa karɓi ta kaddar ta buɗe domin ganin abinda yake ciki,ta daɗe tana karantawa kafin ta saki ta kaddatar ta zabga uban tagumi.

Abba ne ya kalleta cikin tunanin abinda ya faro yace.

"ina fatan lafiya ba wani abu bane ko?"7

Hawaye Umma ta fara cikin konar rai da takaici take magana.

"Wai ace yaronnan duk zaman auren da suke da Lamrat bai taɓa saninta a matsayin ƴar mace ba?babban abinda tausayin yarinyar bata da lafiya,my dear doba ta kaddar ka gani" ta faɗa tana goge hawayen fuskarta.

"Innalillahi wa'inna ilaihir" raji'un kawai Abba ke maimai tawa, kallon munaya yayi yace.

"yarinya mungode Allah yayi maki al'barka kinji"

Murmushi tayi naji daɗi koba komai ta samu hanyar tai makon Lamrat,tashi tayi tai masu sallama.

Abba ne yasa hannu ya ɗauki wayarsa yayi daining number Yisham,tana fara ƙara ya ɗauka cikin zafin rai Abba yake magana.

"Captain duk inda kake kayi maza kazo yanzo kuma ka tawo tare da Lamratu"yana gama faɗin hakan ya t kashe wayar tasa.

Ji yayi kansa yana tsara masa ganin tsaiwa ba zata kai masa ba ya nemi waje kusa da Abba ya zauna,sam ya kasa gane wanne mood yake a yanzo ace aure wajan 2years amma mutum baisan matarsa ba,ya tabbatar da shine hakan ba zata taɓa faruwa shi daman yasan za'a rina domin dukkan abinda suke ai katawa yana sane dasu,kamar daga sama yaji Umma tace.

"yauwa Mujaheed mungama magana da Abbanka,kaje ka nemi auren wannan yarinyar ƙawar Lamraru Huda,kuma saura naji labarin baka jeba"

Kallonta kawai yayi haɗe da jinjina kansa dan bazai iya magana ba,suna nan zaune su kaji ƙarar tsaiwar mota a wajan cikin sanyin jiki suke shigowa ɗakin gaba ɗayansu sanye yake coffe boyal sai black cap yayi matuƙar kyau sai ƙamshi yake zabgawa.

Tana biye dashi tamkar bata son tafiya sabida ya nayin jikinta babu kwari,wata milk abaya ce a jikinta mai zanan stone blue tayi rolling kanta da mayafin abayar cikin siririyar murya tayi sallama ta shigo ciki wani farin ciki taji da zuwanta gidan domin dunda tayi aure babu inda take zuwa,inda Umma take zaune ta nufa tana zuwa ta faɗa jikinta tana sauke numfashi(kai Lamrat Umma dai sirikar kice😒)ta ace zata iya kuka to tabbas yan zone ya dace tayi kuka mai issarta ko zata samu sauƙi a ranta,lafewa ta ƙarayi jikin Ummata ko gaidasu ta gagara yi.

Shima waje ya samu inda Mujaheed yake ya zauna,a hankali yace.

"Umma barka da gida"shuru tayi bata bashi amsa ba,jiyayi jikinsa yayi sanyi domin indai Umma tayimai haka to tana matuƙar jin haushinsa,yasan cewa ba zata amsa ba dan haka yayi mata ya koma kan Abba yace.

"Abba sannu da gida"

Ɗan gyara zama Abba yayi haɗe da cewa.

"yauwa Captain"Mujaheed ne ya kalli ɗan uwanda ya gai dashi daga nan babu wanda ya ƙara magana.

Wajan 20minuted suna haka kana Abba ya kalli Yisham yace.

"Captain inason ka bawa Lamratu ta kaddar sakinta tunda baka sonta,ni bazanma baki ba Amma kasani haƙƙin marainiya daga ɗauka bazai taɓa barin kaba indai ba itace ta haife maka ba"ya faɗi yana kallon Lamrat wacce tayi kwance jikin Umma.

Kallon Abba kawai Yisham yake yama rasa mai zaice wai ya saki Lamrat to akanme,shuru ne ya biyo bayan abinda Abba yace ganin bashi da niyar magana yasa Abba ƙara mai-maita abinda yace,kamar mai koyan magana haka Yisham ya buɗe baki yace.

"wane irin saki kuma Abba?,ko wani yace maku inawa Lamrat wani abune?" wannan tambayoyin Yisham ya jerawa Abba lokaci ɗaya.

Kallon ka rai namin hankali Abba yabi Yisham dashi,kafin yace.

"ni kakewa wannan tambayoyin kenan ko?to ka sani duk abinda kake ai katawa Lamrat mun sani hatta tafiyar da kayi washe gari da aka kai maka ita,kai bama wannan ba dukkan rashin lafiyarta mun sani kuma kasan maganin abin kaƙi ɗaukan mafita dan mugunta,bana son dugun zance nace ka bawa Lamratu ta kaddarta tunda baka sonta"

Tab ɗin shikam saidai Abba ya yan kashi dan hannunsa bazai iya rubutawa Lamrat saki ba,idan yayi haka ai yaci amanar Mummy data yarda dashi,kansa ya ɗaga ya kalli Lamrat sannan yacem

"Kee!tashi mutafi"Umma ce ta zaro ido haɗe da riƙe haɓa tace.

"na shigesu da yaranan zamani wato ta bika ka ƙarasa kasheta ko?kee Lamratu maza tashi ki huce ɗakinki"

Bai ƙara magana ba ya tashi jiki a sanyaye yayi hanyar part ɗinsa(lol zaman gida ya ganka Yisham).

*After 1month*

Bai taɓa jin zaiso abu a duniya har dazai wahalar dashi ya nemi bashi kunya ba sai yanzo,bai taɓa tunanin ƙiyayya na zama soyyaya ba sai a ƴan kwanakin nan,rabon da ya ganta da idonsa ya manta yadai ji su Umma na maganar ta samu admission na makaranta tama fara zuwa,to duk wannan abun da izinin wa?bashi da burin daya huce ya ganta da idonsa ko zata gane halin da suke ciki,kila haka take fita da wannan banzar shigar nata mtwss yaja tsaki na takaici,shikam wakke abune zaiyi wanda zaisa a bashi matarsa?tabbas yau dole na ya samu Lamrat kota wanne hali ne.

Itakam Lamrat gata nanne ba zaka taɓa iya gane halin da take ciki ba,badan bata da damuwa tana koƙarin ɓoyewa ne sabida karta bawa Umma kunya,amma kullum bata iya bacci sabida yadda ta keji sonsa ya fara shigarta wanda ba tayi tsammani ba.

To masha Allah an damu dai-daito tsakanin Huda da Mujaheed,Meenat daman tun bikin Yayanta Yisham ɗaya daga cikin abokinsa yace yana sonta yazo haka an tsaida maganar biki nan da wata biyu masu zuwa,daman ita Shatuu bayan bikin Lamrat da wata ɗaya akai bikinta wanda zuwa yanzo tana da ƴar mai kama da ita.

"how long zaki ɓoye damuwar da take ranki Lamrat" cewar Meenat.

Ɗan kallanta Lamrat tayi sannan tace.

"meaning?"

"uhm kina wahalar da kanki,mai yasa ba zaki bawa zuciyarki damar kula da wanda take soba?ada nasan bakison Yaya Yisham yazo kuma tabbast akwai soyyayarsa wacce ke kwance ƙasan zuciyarki amma kina wasa da damarki" Meenat ta faɗa tana latsa wayar hannunta.

Tashi  tayi domin ta fara jin bacci bata ƙara magana ba ta miƙe tayi waje domin tafiwa part ɗinta.

Saida ta tsaya a hanya taci kukanta wanda ba zata iya cewa ga dalilin yinshi ba,ganin babu mai rarrashinta yasa ta share hawaye haɗe da turo ƙofar ɗakinta tana shiga ta murza mata key,juyowar da zatai ta ganshi kwance akan bed ɗinta.

LAMRAT Où les histoires vivent. Découvrez maintenant