LAMRAT 76-80

836 46 1
                                    

*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💋💖
*NIMCY LUV*

*➰➰76-80*

*LUV AND HAPPINESS*



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Eid mubarak my fans,ina rokon Allah yayi maka rahama,Allah ya karɓi tubanmu fiye da tunaninmu,ubangiji yaji ƙanmu,Allah yasa munyi ibada karɓaɓɓiya🙌👏*

Wannan page ɗin na sadaukar ga dukkan masoyan lamrat🥰inajinjina maku bisa soyyayarku,comments ɗinku yana firgitani😘Amma kuyimin afuwa sabida typing ya ƙaro na sabon book ɗina,(sai na aureta) su oo mutanan lamrat an daɗe da fara regester sai na aureta,akan naira 200 kacal👌😘saina jiku

💫💫💫💫💫saurin sakin kayan tayi,haɗe da jada baya,ganinsa tayi jingine a jikin kofa ya harɗe hannunsa a ƙirji,lumshe idonsa yayi,yanajin tsanar yarinyar har cikin zuciyarsa yarasa maizai mata ya huce,ganin zata gudu yayi saurin kamota,sakin ƙara tayi haɗe gantsara masa cizo a hannu,ko motsi baiba saima ƙara ƙatse mata hannu da yayi, a hankali ya buɗe bakinsa kamar bayaso yace.

"ɓarauniya kawai,ki tabbatar duk abinda kikaci nawa saikinyi amansa anan wajan kuma" bai gama faɗin abinda yayi niya ba yaji ta faɗo jikinsa gaba ɗaya,ƙanƙameshi tayi ta fara kuka haɗe kiran sunansa.

"kayimin afuwa yayana,bazan ƙara ɗaukar maka abuba,ka tuna niɗin marainiya ce,bani da kowa,dan Allah yaya karka daken,haba yayana ɗan albarka"sosai take kukan kuma taƙi yadda su haɗa ido,hannu yasa ya ɗagota suka haɗa fuskarsa babu yabu babu fallasa,so yake ya gano gaskiyar abinda take faɗa amma ya kasa,sakamakon idonta da yake a rufe,magana ya fara kamar bayaso.

"kee! Kada nasake ganin ƙafarki a ɗakinnan,wato sabida kina taƙama da iskanci shine idan na ajjiye abu zakizo ki ɗauka,na sake ganin ƙafarki saina harbeki stupid gril kawai get out of my room"

Bata jira jin abinda zaice ba ta fita tana boye dariyar dake cinta,uhm ai idan kasan wata baka san wata ba,angaya maka ni banzace,wallahi natsaneka yisham,bana sonka kwata-kwata i hate you,jitayi tayi karo da abu a gabanta,ɗagowa tayi domin duba waye,mujaheed ta gani yana mata murmushi,ta rasa kwana biyu mai yasa yake shisshige mata,murmushi tayi tace.

"aa bro ya akaine kake wannan murmushi haka,kamar anyi maka kyautar kujerar makka"

uhm kawai yace mata sannan yaja hannunta suka fara sauka daga step ɗin benen,tsayawa tayi taƙi tafiya,shima tsayawa yana kallonta alamar tambaya,dariya lamrat ta fara haɗe da cewa.

"Allah bro nina gajine kawai ka ɗaukeni,wlh banson bene"

Baki ya saka yana kallonta,babu yadda ya iya haka yasa hannu ya ɗauke,aikuwa ta sakale wuyansa tana dariya,shima dariya yayi yace

"beby lamrat ashe baki da nauyi?"

Uhm kawai tace mai,ta ƙara kwantar da kanta a kirjinsa tana shaƙar kamshinsa,hakan yayi dai² da fitowar yisham daga ɗakinsa,jiyayi gabansa ya faɗi,ransa ya ɓaci.

"mtww ƴar isa kawai,shima mujaheed dake banza ne hadda ɗaukanta,zanyi maganinsa wallahi"

Haka rayuwa ta fara yiwa lamrat daɗi cikn gidansu captain yisham,hankalinta ya kwanta,ta tattara yisham ta sashi a gefe,ko ganinsa tayi zata tashi a wajan,shima hakan yayi masa daɗi.

Ɓangaran mujaheed abun ba'a cewa komai,kullum cikin tunanin lamrat yake,bashi da nutsuwa idan baigan taba,mafarkinta kowa yasha yi babu adadi,lamrat yarinya ce mai shiga sosai,joyawa yayi akan bed ɗinsa yanason tattance abinda yakeji game da lamrat amma ya kasa,nutsuwa yayi sosai ya rufe idonsa yana sauraron bugun zuciyarsa,a hankali bakinsa ya furta.

"wannan wanne irin soyyayane,luv with lamrat,no tayaya hakan zai kasance,infat yasan lamrat batason meye so ba, bare soyyaya, guda nawa ma take 15 years ya salam,tashi yayi zaune yana tunanin mafita dan abin ya fara bashi tsoro kar yaje zuciyarsa ta buga akan yarinyar da batasan yanayi ba,shuru yayi yana tunani,can ya kara cewa bro yisham,da sauri ya tashi ya fita a ɗakinsa.

A zaune ya sameshi akan sofa yana kallon star life,da murmushi a fuskarsa yace.

"aa bro kallo kakeyi ne?"

Shuru yisham yayi bai magana ba,mujaheed yasan hali dan haka ya zauna kusa dashi yace.

"bro daman magana nakeson nayi dakai akan lamrat"

Dam yisham yaji gabansa ya faɗi amma ya dake yace.

"ok metayi maka lamrat ɗin?"

Shuru mujaheed yayi can kuma ya kalli yisham yace.

"bro daman inason lamrat ne,i luv her,i want to marry her".


Ƴar mutan sheka ce😇

LAMRAT Donde viven las historias. Descúbrelo ahora