LAMRAT 146-150

1.5K 65 6
                                    


*💖👯‍♀️LAMRAT👯‍♀️💖*

💖💋Romantic story💖💋
       *NA'IMA SULAIMAN*
             Nimcy luv

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

@Wattpat
Nimcyluv

     *gaba ɗaya bansan mezance ba tabbas yau ina cikin nishaɗi da jin daɗi mara misaltuwa,nagode masoya na sosai wajan bani haɗin kai🙏🏻🙏🏻ina godiya da  kungiyata wacce ta bani damar rubutu acikinta tnx alot.*

     farin ciki mara yankewa,nagodewa kowa,wannan page ɗin sadaukarwa ne ga dukkan mai karanta book ɗinan,jama'ar facebook ngd sosai luv you sabida Allah.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
 
     *➰➰146-150*
        *END OF STORY*

Hannu yasa ya riƙe hannun data dake shi matso da kansa yayi daf da face ɗinta wanda hakan yasa kirjinsu ke gogawar na juna,cikin kwayar idonta ya kallwa wanda itama shi take kallo yace.

"oyya beby maza dakeni indai hakan zai maki daɗi"

Mai makon ta dakeshin kamar yadda yace sai kawai tashafe da kuka wanda zan iya cewa na shagwaɓane,hannunsa ya saka a saman lips ɗinta haɗe da cewa.

"Shiit pls"

Ɗan buɗe bakin nata tayi nan hannunsa ya faɗa cikin bakinta,dole ka fanshe muguntar da kayimin nima zan rama,ɗan yatsan nasa ta fara tsotsa tamkar ta samu sweet lokaci guda ta faɗa lumshe ido wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta,shuru yayi bai magana ba sai wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya da yake saukewa few minutes idonsa ya sauya kala red,kanta ya tallafo saitin fuskarsa yaga yadda face ɗinta yayi jage-jage da hawaye hakan yasa yakai bakinsa saitin idonta ya shiga lashe hawayen fuskar nata,ganin yana koƙarin haɗe bakinsu tayi saurin kwace fuskarta,kallonta yayi sannan ya ɗan kwaɓe fuskarsa alamar shagwaɓa tunda suka zauna sai yanzo ta buɗe baki tace.

"Yaya nifa ba gidanka zan koma ba,kawai dai na yafe maka laifinka ne"

  Wanni kallo yayi mata na baki da hankali hannu yasa ya dalle mata baki wanda hakan yasa har ƴar ƙara tayi dan zafi,kamo ta yayi gaba ɗaya ya sata a tsakiyar kirjinsa gaba ɗaya yayi mata rumfa da faffaɗan kirjinsa turarensa yabi ya addabi zuciyarta cikin fusata yace.

   "Lamrat na fara sonki tun bakison wace keba,na fara sonki a lokacin da kika fara ganina wanda zan iya cewa kema a lokacin kika fara sona,Lamrat kada kiyi mamaki idan nace dukkan abinda na aita maki akan sone,farkon ganina dake na fara gwada maki kalar muguntarmu ta sojoji domin yi maki gwaji ga mamakina sai naga baki da tsoro duk da irin kwarjinina amma kin raba abinda nai maki wonderfull,nayi maki mugunta na saki tsallan kwaɗo da kika tashi sai kika zubamin karkashi wanda kika kosa karyani,wow beby i like ur stayel na fahimci bakison yimin magana ba tare da nayi maki abinda zaki kulani ba hakan tasa dukkan abinda zai ɓata maki rai naƙeyinsa,lokacin da kika fara ɗaukan cake a ɗakina a ranar naje nayo shopping nasiyo wasu cake ɗin masuwa domin naga kinaso sosai,nayi tafiya zuwa enugo tunaninki bana sonki yasa na tafi na barki ko?mun sauka enugo lafiya inda aka karka samu muka fara faɗa da ƴan konan bakin wake munsamu nasarar kashe amma sojojinmu an harbi wasu ina ɗaya daga ci amma ni a hannu aka harban wanda hakan yasa sai da nayi jinyar wata uku cif a asibiti muna shirin dawowa gida wani faɗan ya ƙara tashi,babu abinda nake tunanin a lokacin saike kada na mutu acan ban ƙara tozali dake ba,hakan tasa bana iya cin komai na rame nayi baƙi,maganar rashin lafiyarki kowa ina sane da komai domin wani zuwa asibiti da nayi doctor ya tabbatarmin kina da matsala a mahaifa wanda hakan zaisa a ɗoraki a magani dan haka a kula dake kafin kisan kanki a matsayinki na ƴar mace sai kin gama shan maganinki wanda zuwa yanzo komai yayi dai-dai tsayawa yayi da magana ya haɗiyi wani yawo mai ɗacin gaske yace,maganar Zezee kowa zan iya cewa ƙanwar abokina ce wacce bata da kowa a nan tazo karatune hakan yasa yace na kula da ita,daga baya tace tana sona wanda hakan yasa muka samu matsala,shin duk irin waɗanan abubuwan ba zaisa kiyi hakuri ki koma gida naba?amma bazan maki dole ba"yana gama faɗin hakan yayiwa motar key sai gida.

LAMRAT Where stories live. Discover now