MAHREEN PAGE 2

61 16 2
                                    

💅  *MAHREEN*   💅



WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




PAGE 2

Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi na sake gyara kwanciya ta, Ina tinanin matsayin Mansoor a waje na da zuciya ta.

Mansoor na d'aya daga cikin samarin da ke so na a makarantar mu, dik da cewa tinda na shiga makarantar ya ke so na Kuma nima Ina ganin shi ya na burge ni saboda tsarin ado da Kwalliyar shi da kamalar shi, sannan da ajin da yake da shi, amma ban tab'a kula shi ba duk irin qoqarin da ya ke Yi na ganin na kula shi d'in,kamar wasa idan ya zo dole sai ya wuce ta gaban ajin mu ya ganni ya ke Jin dad'i, haka nima duk sanda zai wuce d'in na gan shi zuciya ta na samun nutsuwa da nishad'i,Ina da qanne a makarantar Wanda bana so su dinga kula samarin makarantar, to ta yaya ni da ke son kula da qanne na zan b'ige da yin saurayi a makaranta?

A wannan lokacin ba Mansoor ne kawai ke so na ba a makarantar mu, hatta da principal din makarantar tamu wanda yake tsoho ne wai Shima so na yake,a cikin malamai da wasu d'alibai su ma ba a bar su a baya ba wajen qoqarin gwada sa'ar su, Wanda na kula hakan na faruwa ne a duk sanda maza suka kula da macen da bata kula kowa sai su yi ta qoqarin tura kan su dan ganin sun zama na d'aya a wajen ta,musamman in Allah ya mata kyan sura.

A hankali na kasa jure irin so da qaunar da Mansoor ke nuna min, na fara qoqarin karya dokoki na da na gidan mu, domin mahaifin mu a Koda yaushe ya na mana nasiha da cewar,

'A duk sanda Wani ya gan ku ya ce ya na son ku, kar ku tsaya kula shi a saman hanya, ku ce Masa ya zo gidan ku ya same ni, saboda ba a ce wa namiji ba a son shi direct Wani Mugu ne,sai ya Iya Yi Maka wata muguntar, Wani Kuma da gaske yake auren ka yake so ya yi, Kun ga idan aka samu na gari Wanda Allah ya nufa da shi za a yi sai mu muyi bincike akan shi,'

Wannan dalili ne ya sa duk yawan samarin da nake yi gida nake aika su wajen mahaifi na ko wajen yayana Wanda shi nake bi, he is that type of over protective brothers d'in nan, he loves me so much kamar yanda nima Ina son shi sosai,ya na kula da mu matuqa, baya qaunar ganin Wani saurayi na bin mu a duk lokacin da Baba baya gari shi ke tsayawa ya sa Ido akammu, Kai ba shi kad'ai ba ma gaba d'aya yayun mu su na da qoqarin kulawa da tarbiyyar mu a Koda yaushe.

Amma dik da haka na take wadannan dokoki da tsaro na gidan mu na fara kula Mansoor, bai tab'a zuwa gidan mu ba dik yanda ya so ya zo bana bari, qanne na ne kawai suka San da zaman shi a matsayin saurayi na na makaranta, Mansoor na da tarbiyya ta yanda ya ke taya ni kula da mutunci na da qima ta da darajata ta 'ya mace a cikin makaranta,bai tab'a Yi min maganar banza ba, Ina girmama shi kamar yanda ya ke girmama ni.

Ina tsaka da tunanin shi na ji bud'e qofar toilet alamar Wani ya shiga, sake juyi na yi na lumshe ido Ina karanto duk wata addu'a da ta zo baki na saboda in samu bacci ya d'auke ni, Ina da wuyar yin bacci, domin tin Ina qarama ta se kowa ya yi bacci ya barni, har yanzu da nake da shekara sha biyar a duniya bata sauya zani ba.

Mahaifiyar mu ta koya min cewar a duk sanda na kasa bacci, in Yi ta karanta ayatul kursiyyu, ko In yi ta yin tasbihi ga Allah, nan da nan zan ji bacci ya d'auke ni,dan haka kuwa ba b'ata lokaci na kulle Ido na na hau yin tasbihi ga Allah, ban San sanda bacci ya d'auke ni ba, sai farka wa na yi na ga 'yan uwana ana hada-hadar yin sallar asuba.

Cikin hanzari na miqe na shiga toilet na yi uzirin da zan yi sannan na d'aura alwala na fito, na tada sallah, Ina idarwa na bi layin 'yan uwana da ke karatun qur'ani, gari na fara haske kowa ya yi addu'a aka shafa aka hau gyaran gida, masu girki suka nufi kitchen kowa ya kama aikin da zai yi.

Ni Ina cikin Wanda suke girki a gidan mu, domin Baba ya kula da bana qaunar wanke wanke, sai ya tsame ni daga cikin qanne na ya had'a ni da yayu na muke girki dake Ina da girman jiki na kamo yayu na,kowa da ranar girkin ta, ko Kuma lokacin girkin ta, misali in Addah Ummu ta yi da safe ni sai in Yi da rana da dare a duk ranar girkin Mama, Addah Firdous Kuma sai ranar girkin Ummah take nata, baba baya qin cin abincin da muka dafa tin muna koyo komai cab'a shi da muka yi haka zai ci abun shi saboda ya San koyo muke Kuma shi ke bamu kwarin guiwa lokuta da dama in na Kai masa abinci, ni da kaina na San tuwo bai dahu ba amma haka zai ta yabawa, har na zo na iya.

MAHREEN Where stories live. Discover now