MAHREEN PAGE 28

32 7 2
                                    

💅  MAHREEN 💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 28:



"Ki na nufin dai ba su gan ki a wajen ba ko kuma sun gan ki kawai suka ci gaba da hirar su" na faɗa cikin dariya.

"Oho musu, amma da alama ba su kula da ni ba ma kwata-kwata,sun gigice da ganin su Aunty Hafsah Maman Najeebu sai tambaya ta ke wai, Wagga kuma daga ina? Ke suhwa ta daura wallah (ke super ta daura wallahi) ke ga kunnen ta, ke ji hannun ta zobbunan gwal sun ka saka, d'iyan wana ? ('ya'yan wane ne? Ke baki ga yanda suka gigice da tambaya ba saboda kawai su na son su ji su waye suka zo wajen ki,"

"To da so suke na mutu da kaɗaici ko? Su sun guje ni se na zauna ban da me kula ni a birnin Kebbi ko? To ai Allah ba haka yake lamarin shi ba, yanda suke so ba za su samu ba har abada,"

Hira muka ci gaba da yi da Suwaidatu daga qarshe na ke ba wa Hafsat labarin abinda ya faru zuwan su ta waya, mu kai ta dariya.

Hafsat na daga mutanen da suka qaunace ni domin Allah ba dan ina da wani abu ba ko su na tunanin zan ba su wani abu, hatta da mahaifiyar ta da na je gaishe ta ta nuna min qauna kamar ta jima da sani na dama haka ta tarbe ni, mutane ne su masu karamci da mutunta ɗan Adam. (Allah ya gafarta wa mahaifin ku)

Wata iriyar rayuwa muka dasa me 'yanci a gidan, ba takura ba sa ido ba kuma tsoron wasu za su gani su ji haushin mu, mune wasan guje-guje, mune 'yar gala-gala, mu ne carafke, duk wani wasa da zai sa mu nishad'i yin shi mu ke da iyalai na ba tare da tunanin wani zai gani ya ji haushi ba.

Mutanen unguwa kuwa na sake tsame kai na daga cikin su, tunda abinda aka sanar da su akai na ba yanda zan na goge shi a zuciyar su tunda ban san mene ba su kuma ba su mu'amalance ni ba balle su san wacece ni, Se na kyale su akan kowa na da ra'ayin yarda da abinda ya ji ko kuma ya yi bincike dan sanin gaskiya, dan haka sai na maida rayuwa ta daga gida, sai gidan Maman Ameenah dattijuwar kirki wadda ta ɗauke ni a matsayin 'yar ta ita da Baban Ameenah,ganin haka se ya sa nima na riqe su a matsayin iyaye na, har nake ba wa Mama da Baba labarin su, su kuma su yi ta yi musu addu'ar alkhairi, nakan ce wa Mama yanda ki ke kula da yaran wasu a garin da ba su da iyaye ba su da dangi shi ne nima Allah ya haɗa ni da mutanen kirki.

Ana haka muka samu labarin za mu yi sabbin 'yan haya, a cikin watan da muke ciki suka fara dawo da kayan su bangaren Maman Ameerah wanda ya ci wani irin dattin da kamar debo bola akai aka zuba,dan haka ba qaramin gyara wajen ya sha ba kan ya dawo hayyacin sa, duk wanda ya gani ba zai gane cewa wannan shine gidan da aka ci dafdala a cikin shi ba.

Waje nan da nan ya ɗauki haske da kyalli kamar za a saka sabuwar amarya, a da duk mun gwada buga qusa a jikin ginin se ta qi zama saboda qarfin ginin gidan, komai qarfin qusa in aka Saka ta a ginin se ta yi wuta ta fice, dan haka da na ga an sa wa sabuwar maqociyar mu labule se na sa hope din nima zata bugu ne in aka sa naci dan zama ba labulen ba dad'i musamman yanda aka fara iskar damuna se mutum ya ji kamar a sahara yake tsabar yashin da ke cika waje.

Da misalin 7;40pm ina tsaye a saman kujera ta ina ta qoqarin cigaba da gwada sanya labule na ko zan samu ya shiga muka ji qarar motoci na tsayawa a bakin gate ɗin gidan, shiru mu ka yi dan mu tabbatar da ko nan ɗin ne duba da cewa dare ya yi bana tsammanin wasu baqi, mun tabbatar da nan gidan ne a lokacin da aka buɗe qaramar qofar gate ɗin aka shiga, hayaniyar mutane muka ji sosai kamar ana biki, hijabi na na dauka na sanya saman kayan bacci na masu guntun wando,na sauka daga saman kujerar da na haye ina gwada buga qusa, sannan na leqa waje, hasken fitilun waya ne suke ta walwali a cikin duhun daren,nima ina tsaye ina haska tawa fitilar wayar,sallama mu ka yi wa juna da mutanen nan sannan na gane sabuwar maqociya ta ce ta ta zo tare wa, dangin ta suka rako ta kamar sabuwar amarya, nan take se abun ya burge ni na qara washe baki ina masu sannu da zuwa, godiya suka min sannan suka buɗe sashen su suka shige nima na koma gida, buga qusar da ban ci gaba ba kenan har yah Maheer ya dawo daga masallaci muka ci abinci mu ka yi shirin kwanciya.

MAHREEN Where stories live. Discover now