MAHREEN PAGE 30

26 8 2
                                    

💅  MAHREEN  💅








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




PAGE 30:

Mu na fita mu ka ga wani bawan Allah wanda ni ban san shi ba amma Yah Maheer ya san shi ya na mana nuni da maqotan mu, wato gidan Maman Abdurraheem ya kama da wuta, ginin mu a Manne yake da juna,hankali tashe mu ka nufi qofar sashen nata, gani muka yi qofar a rufe take, of course dole qofa ta zama a rufe mana tunda ba sa gida? Ta baya muka zagaya a gigice ni da Suwaidatu hankali na tashe na bude windown ta na kitchen wani hucin zafi ne ya buge ni se na hango wuta na tashi a ciki amma bata mamaye ko ina ba, tunanin zura Suwaidatu ta window ne ya zo min a rai na in ta shiga ta kashe ta fito, dan da zan iya shiga ni zan Shi na kashe na fito, wata zuciyar nan take ta hane ni da yin wannan aikin gangancin, cikin jimamin abinda zan yi muka ji Yah Maheer na kira na, a rude na koma sashen mu, ashe wuta ta bi ta silin ta shiga sashen mu, kafin ka ce me gidan mu ya cika da matasa da maqota da mata, Yah Maheer na qoqarin fitar da akwatin da credentials din mu ke ciki wasu matasa na qoqarin fidda kayan mu, amma wutar nan bata bada damar daukan kaya ba, ta na gama wa da gidan mu har ta faɗa gidan Hauwa'u da wata baiwar Allah da ake kira Maman Khadeejah wadda ta shigo dan taimaka mana, wuta ke ci ba tsaya wa ba qaqqautawa ina tsaye a tsakiyar parlour na ina jin yanda tiririn wutar ke duka na amma gaba ɗaya hankali na baya jiki na,ni ba tunani nake ba ban kuma san me ke faruwa ba a kewaye da ni, cannn nesa da saurare na na Ji ana faɗin,

"Ke ki fita daga wajen nan, ki gaggauta fita wutar ta ci saman wajen da yawa fa kar ya fado akan ta"

Yah Maheer da ya zaci ina waje ne ya kalli inda nake tsaye cikin parlour na da ke ci da wuta, wurgi ya yi da akwatin hannun sa ya isa gaba na ya na min magana, ganin bana gane komai sai hawaye da ke zubar min ne ya sa shi kama ni ya rungume ya fitar da ni daga cikin wajen,can jikin katangar gidan ya tsayar da ni ya na duba jiki na ko zai ga wani alamun quna be gani ba, komawa wajen akwatin takardun mu yayi ya dauka ya kai gaba na ya ajiye sannan ya janyo fridge d'ina gaba na da TV na se ya koma suka ci gaba da fidda abinda ya samu, duk abin nan da ake Yah Maheer na komai a  guje ya na neman layin Ahmad mijin Maman Abdurraheem dan ya sanar da su abinda ke faruwa amma ba ta shiga.

Hankalin shi tashe ya roqi wani a wajen ya ce ya kira masa maqocin mu saboda su san halin da ake ciki saboda su zo su bude wajen a samu ko ba yawa a fidda masu wani abun.

Ana haka Hauwa'u da mijin ta suka iso bayan gidan su ya gama qonewa qurmus,ga ta da ciki, kuka ta dinga yi itama, ni kuwa ina nan inda Yah Maheer ya aje ni tsugunne ina tsiyayar da hawaye ina tasbihi ga Ubangijin da ya halicci wuta, sannan ina neman tsari daga azabar ta.

Wuta ce jajazur sakamakon kusan komai nawa na parlour red ne, komai ma lasar shi take a wajen abun gwanin ban tsoro, ba abinda nake tunawa se qiyama, na yi istighfari ban san adadi ba saboda tsoron Allah da na ji ya shigo zuwa ta.

Gidan Maman Ameenah aka dinga kai kayan mu da suka rage ajiya,se wani gida wanda ban san shi ba har yau kuma ba su neme ni dan su bani kayana ba .

Muna gidan Maman Ameenah Maman Abdurraheem ta dawo dan mijin ta ya riga ta zuwa aka buɗe aka debi wasu kayan nasu, nan gidan Maman Ameenah aka kawo mata ita ma,cikin jimami da kuka a idon ta itama ta shiga muka zauna tare muka jajanta wa junan mu abinda ya faru, Maman Abdurraheem ta
Shiga damuwa sosai a wannan lokacin itama, zaune muke ana ta shiga da fita ana mana jaje, se ga Maman Ameerah ta zo ta na kukan tausayin mu, cikin jimantawa ta ke sanar da ni yanda akai ta san gobara ta  same mu.

Godiya na mata tare da fatan alkhairi, daga qarshe ta mana sallama ta wuce wajen Hauwa'u, ban san ya suka yi ba dai amma qarshe gidan ta Hauwa'u da mijin ta suka koma da zama.

Mu kuma a ranar na tafi gidan Maryam ɗin Uncle Inuwa mu ka kwana ni da Suwaidatu, mu na nan abokin Yah Maheer Bashar da ke zama a Abuja ya bamu aron gidan shi da ke unguwar Gesse tunda su ba anan suke zama ba yanzu, Bashar abokin aikin Yah Maheer ne mutanen kirki ne shi da matar shi Rasheedah  Alqali, tun Rasheedah na amarya Bashar ya kawo mana ita muna Alieru qtrs, ta na da fara'a sosai kuma wayayyiyar mace ce 'yar boko, Rasheedah bata da matsala sam a mu'amalar ta da mutane haka ma mijin ta Bashar.

MAHREEN Where stories live. Discover now