MAHREEN PAGE 29

25 7 5
                                    

💅  MAHREEN  💅


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 29:

Gaba ɗaya hankali na ya tafi wajen kallon ajin da matar ke tattare da shi wanda ya sanya idanu na cika da ganin kyan ta duk da cewa ba wata kyakkyawa bace sosai, yanayin shigar ta da ajin ta ne ya qara fito da kyan ta, gaishe ta na yi sannan na maida hankali na gefe guda ina tunanin yanda Maman Abdurraheem ta ke ta murnar ganin matar da alama ta na da mahimmanci a wajen ta, bangaren Maman Abdurraheem suka shige su na ta murnar ganin juna, ni kuma se na tashi na tattara kaya na na shige nawa bangaren na yi alwala na yi sallah sannan na hau girki, ina yi ina karatun wani novel da na aro wajen Aunty Sumayyah, (Maman Amirah) ban gama girki na ba Maman Abdurraheem ta shigo muka zauna mu na hira, anan take sanar da ni qawar ta ce ta zo nuna mata motar da mijin ta ya sai mata kwanan nan,hirar maganin mata ta hau yi min har kalar wanda qawar ta ta ke amfani da shi,mamaki duk ya kama ni, daga Shan maganin mata se a maka kyautar mota? Ko dai dama can mijin ya yi niyya ne? Daga sama na jiyo muryar Maman Abdurraheem ta na cewa,

"Na taya ta murna, amma mu da mazan mu ba su da halin siyan mota ko albarka aka saka mana ai mun gode"

Dariya mu ka yi a tare, ina ci gaba da jinjina lamarin.

"Ke bari ma zan baki wani magani ki gwada ya na da kyau, sannan akwai lalle da zan baki ki qunsa a qafar ki, da wani ruwa, ke in ki ka sha ruwan nan ko? Hummmm ba a cewa komai, ki bari kawai zan baki su ki gwada mugun tsada ne da su in ya qare se kin nema"

"To ni ina na ga kuɗin siyan maganin mata musamman me tsada? Ai kedai kawai ki bani domin Allah na sha a samin albarkar nima "

Dariya mu ka sake yi, cikin zuciya ta ina addu'a kar Allah ya bata ikon bani maganin nan, musamman lallen.

'wanne irin lalle ne na mallaka ko farin jini? Me aka saka a ciki? Sannan menene a cikin ruwan da zan sha ina aka samo shi? Ba zan iya sha ba gaskiya'

A fili kuwa ina ta biye mata mu na magana, nan take na tuna wani maganin mata da karambani na ya kai ni na sha shi da jimawa, awanni kaɗan da sha Yah Maheer ya dawo, sai da komai ya kankama na hau zubar da jini ba qaqqautawa ba tsayawa se da na yi kwanaki biyar sannan ya tsaya, na zaci period ne na sake gwada sha, jini ya sake balle min har da guda guda, abun tun ya na ban mamaki ya dawo bani tsoro,duk sanda na sha maganin mata za a yi abu d'ayan uku ne.

Ko na dinga zubar da jini har se aikin maganin ya qare a jiki na.

Ko na dinga qunci da yawan neman faɗa da masifa da bala'i Dan a Kula ni na yi fushi na qi bada haɗin kai.

Ko kuma qatoton qurji ya fito min guda ɗaya tall raina kama ka ga gayya wanda motsin arziqi ba zan iya ba har se aikin maganin ya qare a jiki na.

Ganin haka ne ya sa na sawaqe wa kai na wahala, gashi ba zan iya ce mata kar ta bani ba se ta ga na raina qoqarin ta, tunda akwai wadda ta taɓa sanar da ni cewar a garin Kebbi mace ta nuna ta na son ki da alkhairi shine ta baki tsarabar maganin mata, a haka dai maganar bani maganin mata ta tashi ba a ban lallen da ruwan ba se aka bani gumba da madara na sha cikin iko na Allah sai ban zubar da jini ba, amma fa haka nan Yah Maheer da kan shi ya ɗauke wuta, za mu kwana waje ɗaya yanda muka saba maqale da juna amma ba zai nemi komai a waje na ba har safiya ta waye, haka da safen ma za mu koma baccin safe kamar yanda muka saba amma haka za mu tashi ba abinda ya gitta, gajiya na yi da wahala na cire rai akan komai na sa wa raina se maganin ya bar aiki jiki na komai zai koma mana normal, tunda ni kaina se na ji ba zan iya fara miqa kai na da kai na ba se ya nema.

Rayuwar mu muka ci gaba da gudanar wa kamar wasu 'yan uwan juna na jiki, zama muke mu sha hira duk ta san mutanen gidan mu a baki na wanda dama zai wahala ka zauna da ni baka san Mama...Baba...Innata...da yaran gidan mu ba gaba dayan su, saboda su ne rayuwa ta, yanda kuwa Yah Maheer ke kula da ni be taɓa damun Naman Abdurraheem ba dan ban taɓa gani ba a fuskar ta ko a maganar ta, duk watarana ta kan tsokane ni  in ta ga ya min wani abu takan ce, 'Uhmm ka ga masoya/ mu ma dai Allah ya sa mu na da masoyan' wata rana kuma in ya yi wani abu da ya burge ta sai dai ta hau yaba masa, ba dai ta kushe ba, ta ce na roqi Allah ya sa ita da mijin ta su koma kamar yanda muke, murmushi na kan yi na janyo wata hirar a bar maganar mu.

MAHREEN Where stories live. Discover now