MAHREEN PAGE 32

23 8 2
                                    

💅  MAHREEN  💅










WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







PAGE 32:







*Mai so a sanya ta a group ɗin MAHREEN2 paid book ta min magana ta wannan No 09031416423*


Qofar parlourn gidan( Kamar ) soundproof ce saboda in aka rufe qofar wanda ke ciki baya jin me ake yi a parlour, sannan wanda ke parlour ba ya jin me ake a ciki.

Mun riga da mun rufe qofar gidan baki ɗaya daga gate ɗin gidan har qofar shiga parlourn, sanda Suwaidatu zata tafi cikin gidan ta rufe qofar key ya na jikin qofa ta waje, we became trapped a cikin parlour no any other way out, mu na nan zaune ba tare da mun san me ke faruwa ba, mu na ta cin soyayyar mu da tsinken tsire hankali kwance mu a dole an bamu waje.

Sauro ne ya dame ni na tashi ina mita na ce,

"Gaskiya sauron nan kun sha na Allah ya isan ya yi yawa haba, duk jiki na cizon sauro ne so suke su kada ni qasa, tashi mu koma d'aki Please na gaji da zaman nan yanzun nan za su dauke wuta na san 12am ya kusa"

Yi ya yi kamar be ji ni ba, cike da shagwaba na zube a jikin shi ina roqon ya tashi mu shiga ciki, a hankali ya buɗe ido ya na kallo na sannan ya ce,

"To d'aga ni, in dai ki na so mu tafi ki d'aga ni na miqe tsaye da qafafu na ba ki na ikirarin ke mai qarfi bace? Qiwar tashi nake ji"

"Ohhhhhh za ku wa ka sha mamaki, ni sai in ɗauke ka ma, ina zuwa"

Tashi na yi tsaye na dinga qoqarin d'aga shi ya zauna ma da duwawun shi na kasa, yaraf na sake kwantawa a jikin shi ina kukan shagwaba ina roqon shi ya tashi mu tafi, amma ya qi, ba mu yi aune ba sai gani mu ka yi an ɗauke wuta, cikin jin haushi na ce,

"Great ! Burin ka ya cika ai sun ɗauke wutar wayoyin mu na cikin d'aki ba abun haska wa,"

Buɗe idon shi ya yi da ya ke a kulle tun dazu ya kalli hasken farin wata da ya ratso labulayen parlourn ya shigo, sannan ya maida kallon shi gare ni ya ce,

"To ba ga shi Allah ya bamu haske mai sanyaya zuciya ba, kalli fa ki gani kalar fatar ki ce kawai bana gani saboda na fiki haske"

"Mafarki kenan na faɗa maka na Fika haske da ina yarinya, ka tambayi mama ka ji"

Dariya ya yi sosai sannan ya ce,

"To ni kin ganni ne da ina yaro, ke ma kin san na fi haka haske ko ba a faɗa maki.ba ko?"

"To na Ji, ni dai tashi mu tafi"

Kamar wanda aka yi wa allurar qarfi haka ya miqe, ya kama hannu na na kwace na koma bayan shi na d'ale ina buga qafa ta a jikin shi kamar me buga machine na ce,

"Yauwaa mu je, laaa mun manta bamu kashe AC ba"

Komawa ya yi da ni a bayan shi ya kashe AC, sannan muka nufi hanyar fita ina tsokanar shi na ce,

"Mijin 'yar lukuta, kai yanzu ko nauyi na baka ji ko?"

"Wa yaga Yar paper, Ke ki ke ganin kan ki da girma ni har yanzu kamar Maijiddah(Autar mu kenan) nake ganin ki"

"Tabdijam sauke Ni to bana son goyon"

Riqe qafafu na ya yi gam, ya ce,

"Baki isa ba ai, har d'aki se kin je a haka yarinya ni na gayyace ki goyo?"

Door handle ya kama zai murd'a dan ya buɗe mu shiga cikin gida sai ya ji wajen ya riqe ya qi bud'uwa, sauke ni ya yi ya ci gaba da qoqarin buɗewa,qofa ta ce ba sai ka buɗe ni in gani ba?

MAHREEN Kde žijí příběhy. Začni objevovat