MAHREEN PAGE 25

35 15 3
                                    

💅   MAHREEN   💅





WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 25:



Machine ne ya ci burki a baya na da qarfin gaske, ina buɗe ido na a hankali sai na kula na bar kan hanya na fara hawa titi, mutumin har ya fara masifa sai ya kula da yanayi na, cikin rage faɗan da ya fara min ya ce,

"Ke Wagga lahiya ki ke kuwa?"

Nan da nan kuwa hawayen da nake ta maqalewa suka hau sauka da gudu, zafin su na qona kumatu na na durqusa na ɗauki jaka ta da ta fad'i na ci gaba da tafiya, biyo ni ya yi ya ce na hau ya kai ni gida,Na so na yi musu sai na ga Kabu kabu ne ko banda kuɗi zan iya tsayawa maqota na karba na biya na basu daga baya dan dai nera saba'in in Allah ya yarda ba zan rasa me ara min ba.

Komawa baya na yi na hau a hankali na sanar da shi Alieru qtrs za a kai ni,nan da nan kuwa ya dauki hanya sai unguwar mu, mu na isa na ce ya jira na dakko masa kuɗin shi ya ce min,

"Basshi d'ai" (barshi kawai)

Godiya na masa na shige cikin gida, ina shiga na yi wurgi da hijabi na na kwanta a qasan carpet na kunna standing fan dama ta saman a kunne take, kuka na buɗe baki da qarfi ina yi, saboda ciwon da ko ina na jiki na yake min, na yi kukan da ban taɓa yi ba a rayuwa ta ranar har se da bacci ya ɗauke ni,Ko juyi na yi sai na b'are baki na ci gaba da kuka na kafin wani baccin ya sake ɗauka ta.

Duk abin nan da ake na rashin lafiya ta ban taɓa qin yin girki ba, saboda Yah Maheer baya son cin wani abincin in ba nawa ba sai dai in lalurar hakan ta kama ya zama ba yanda zai yi to zai ci a wani wajen, se kuma in mun je gida, ko maqota ne suka kawo abinci baya ci, tin da na dawo garin ya dena cin abincin kowa.

Wata rana da jima wa ban mantawa mu na hira da Maman Ameerah a game da maza da ke cin abinci a ko ina, se na ke faɗin cewa shi baya da wannan halin gaskiya duk da ya kan ci amma se dole,cikin nuna jin haushi ta ce,

'Wa ya faɗa maki baya cin abincin waje?'

'Ba ina nufin ba ya cin abincin waje kwata kwata ba, in dai Ina nan ba ya cin abincin ko ina ya gwammace ya zauna da yunwa ko ya yi ta shan fruits, shi ya sa sanda ya fara zama a garin nan duk sanda ya je zan ga ya rame'

'Ai kuwa ya na cin nawa, kuma rama da ya yi ai saboda ciwon qodar da ya yi ne baki ga har baqi ya yi ba a lokacin,kuma haka ɗaliban shi mata za su dinga zuwa duba shi har abincin suke kawo masa, na kan ce Allah ya kiyaye kar su masa asiri tunda matan garin nan akwai shegen asiri in suka ga namiji su na so se ki ga budurwa ta kai shi wajen malami an asirice mata shi'

A lokacin nan na ji raina ya ɓaci wato a gaba na ne yake nuna ba ya son cin abincin kowa a bayan ido na se ya hau ci, ko da ya dawo na tare shi da maganar ina ta masifa, be ce min ci kan ki ba se da na gama sannan ya ce,

'Da ta faɗa maki ina cin abincin ta ta taba gani na da idon ta na ci abincin wani waje haka kawai ba dalili? Na tan ma saboda mijin ta na gayyata na ne kuma kin san babu kyau a gayyace ka cin abinci ka qi, ke kin ga shaida ai sanda ku ka zo bread ne se fresh milk da fruits su ne abinci na na kan kuma sai nama haka da kifi soyayye na ci, kuma da take maganar 'yan mata ba ɗalibai na bane, sannan ba sanadin na kwanta jinya suka zo duba ni ba? Yanda suka kai haka suke kwashewa tunda ba iya ci ma nake ba, kaiii wannan matar na rasa me yasa take so dole sai ta ja min masifa ina zaune lafiya da iyali na, sannan in banda abinki Zan zauna da yunwa ne idan na ji ina son cin wani abu ba bread ba ke da kan ki ki ke matsa min se na je na siya na ci, ra'ayi na ne bana so na ci wani abincin in ba naki ba, sannan kamawa take nake cin wani abincin idan ba nakin ba, ai komai dalili ne da shi ko? Dan Allah ki dena ɗaukan maganganun matar nan ba kowanne ne ke da amfani ba"

MAHREEN Where stories live. Discover now