MAHREEN PAGE 24

44 14 0
                                    

💅   MAHREEN 💅













WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 24:









"Wai ke irin yarinyar nan ko? A siyo maki sweet da chesee, ba ki gajiya ne kullum se kin raka shi? Ni fa ba zan iya yanda ki ke yi ba ko da yaushe ka yi ta manne wa miji ai se ya gundura da kai"

To ni wace ma amsa zan bata ne? Kallon ta na yi fuska ta ɗauke da murmushin da Yah Maheer ya dasa min, ban ga abinda zai goge min shi ba a wannan lokacin, kawai se na sa kai na shige sashe na na bar ta.

Garin ya qara dinkewa da zafi saboda damina da ke gabatowa dan haka zafi sai ya qara yawa sosai, ba sassauci ko ta ina, in an kunna fan zafi take bayar wa bamu da AC, amma ina da standing fan da kuma ta sama,katifa muka dakko muka saka a tsakiyar parlour muka bubbuɗe windows da qofofi, ta haka ne muke samun iska ta dan ratsa, duk da cewa in zafi ya yi zafi bishhiyoyin ma sai in ga kamar tare iskar suke dan ba sa kad'awa sam.

Ga jarabawa na gabatowa sam bani da hutu bani da sukuni,nan da nan kuwa sai ciwo ya taso min, ga ciwon ciki ga qurajen zafi manya manya ga zubar jini wanda na fi wata guda ina yin shi.

Watarana ina zaune a kujera a parlour na kunna waya ta, ta na da TV  na kunna ina kallon KB TV se na ga ana tallar wasu masu maganin Islamic,ina kallo kawai na kau da kai na a raina ina ayyana.

'Kai na gaji da shan magunguna, ba na baturen ba ba na Islamic din ba, in qiyashi za ai daga farkon rayuwa ta zuwa yanzu na sha maganin da bai da adadi bai da iyaka, ana ta kashe kuɗi a banza, ba ma zan faɗa masa maganar me maganin nan ba kar ya ce se mun je' (na manta hali na na bayyana masa komai ko da laifi na aikata kuwa se na fallasa kai na da kai na)

Da sauri na kashe wayar na aje ta gefe na, na kwanta na yi lamoooo ina tunanin yanda rayuwa ta take tafiya,kusan kullum cikin ciwo ko kuma wata lalurar ,nan take na daga hannaye na sama na ce,

"Allah na gode maka akan dukkan baiwar ka da ni'imomin ka da ka yi min,Allah ka yi min baiwa ta jinya Ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawa ka qara min lafiya da imani, Allah ka qara wa miji na hakuri da juriya game da lalurori na, Allah ka qara masa arziki mai albarka ka jiqan iyayen shi Ameen"

"Ameeen ya mar'atussaliha, Allah ya qara wa Mama da Baba lafiya da nisan kwana me albarka"

Shine abinda Yah Maheer ya ce, wanda ya shigo ya ji ina addu'a a fili,da sauri na tashi na je gare shi, har zan rungume shi na fasa, na tsaya ina mamakin yaushe ya dawo ban ji qarar machine ba?

"A can na ajiye shi yanzu zan fita kasuwa na yi mana 'yar siyayya, na ɗan samu wasu kuɗi ne na ce bari na je kasuwa, ga jaka ta aje can, me da me ya kamata a qaro?"

"Alhamdulillahi, Allah ya qara bud'i mai albarka, zauna ka sha ko ruwa ne mana, ballantana na gama girki ma"

"Ni fa abinda ke burge ni da ke kenan, da an sauke na safe a maida na rana ba a zama da yunwa da mutum ya nema yake samu"

"Ai daga wajen ka ne, da baka ajiye wa me zan dafa?"

"Ke dai ki gode Allah kawai kamar yanda nake gode wa Allah da ya bani ke a matsayin matata, kaiiii gaskiya ni ɗin fa na haɗu, se da na bari duk mazajen nan suka gama haukan su wai su suna son ki, na lallabo na lallabo ta bayan fage na dauke ki"

(Kirarin da yake yi wa kan shi kenan a koda yaushe, musamman in na yi abinda ya burge shi sai ya dinga jin shi kam ya gama yin Sa'a a aduniya, sai ya hau kuranta kan shi akan ya lallabo ya ɗauke ni cikin sauqi ba hayaniya)

"Kai dai ka ci gaba da godewa Allah ɗin dan shi ne ya baka ba wani laben ka ba"

"Ehhh ai shi yasa ni bana wasa da tashi kullum cikin dare ina yi wa iyaye na addu'a in roqa maki rahamar Allah da gafarar shi sannan in gode masa da ya bani ke a matsayin mata"

MAHREEN Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ