MAHREEN PAGE 33

31 8 4
                                    

💅  MAHREEN  💅











WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





*ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL FIFUL WHATSAPP ME ON THIS DIGITS 09031416423 IF YOU WANT TO BE IN MAHREEN PAID BOOK GROUP....THE PAYMENT WILL BE AFTER I FINISH THE WHOLE NOVEL THANK YOU*

PAGE 33:


Ido biyu mu ka yi da Rasheedah wato matar mai gidan da muke ciki, cikin farin ciki da sakin fuska na tarbe ta mu ka shiga cikin gidan ina yi mata sannu da zuwa, har dakin da aka sauke mu na shiga da ita, muka baje anan mu ka hau gaisawa.

Rasheedah na ɗaya daga cikin mutanen da suke so su ga yau ace nima na riqe d'a ko 'ya na kai na,dan haka ta na qoqari sosai wajen bani shawarwarin da suka dace,wannan ne dalilin da ya sa bayan mun gaisa ta d'akko maganar haihuwa,ta ke sanar da ni wani method da ake yi na IVF wato In Vitro Fertilisation, nan take ta hau yi min bayanin yanda ake yin shi, ina ji sai na ji hankali na ya tashi tsoro ya cika zuciya ta, amma ko a fuska ban.nuna mata hakan ba, ina ci gaba da tsifa ta mu na ta hirar, can qasan zuciya ta ina tunanin me zan kawo mata,bamu da komai sai ruwan pampo, se wake da shinkafa da na dafa kuma kaɗan ne ba yawa,haka dai na miqe na je na debo ruwan sha da abincin na kawo, muka ci gaba da hira,cikin hirar ta take sanar da ni cewar ta na dauke da ciki, murna na fara yi ina yi mata addu'a ita da abinda ke cikin ta, haihuwa ta biyu kenan za ta yi da izinin Allah, nan take take nuna min da zata samu hutu tabbas da hakan zata fi so, ni kuwa Se  na hau yi mata nasiha da nuna mata ta gode wa Allah ta kuma rungumi kyautar da ya musu hannu bibbiyu, ni ai na ishe ta misali, gashi shekarun aure na sun fi nata kuma ban haihu ba,godiya ta yi wa Allah ta miqe ta ce za ta shiga toilet.

Tashi nima na yi na bi bayan ta muka fita, dake toilet din daf yake da dakin da muke se ta shiga, daga yanda ta fito na gane she was pleased with yanda nake kula da wajen, tunda dama tun da ta shigo na kula ta na ta murmushi.

Freezer din su ta buɗe ta gani ni Kuma Ina biye ina bata labarin karbar naman kan da aka yi, muke dariyar ban san ma'anar langab'u ba,nan take nake sake bata hakurin b'ata freezer din da na yi wajen wanke wa,ta nuna babu komai,mu na ta tafiya se gamu har kitchen, ta ce za ta d'au ki oven qarami, to ni shangai furar daka ban ma san da zaman shi a gidan ba, ina biye da ita ta d'akko shi,se a sannan na san da zaman shi.

Gani ta yi kamar da risho muke amfani nan take ta nuna rashin jin daɗin ta, ta ce,

"Mi da baku anfani da gas cooker? Kuma haɗe yake da electric fa, naga baku anhwani (amfani) da abubuwa da yawa mi halan?"

Murmushi na yi mata na hau magana cikin barkwanci na da mutane ke yawan faɗin ina da shi, na ce,

"Yo ni ina na iya amfani da kayan nan? Kedai banni da rishon da shi na saba, Allah ya saka maku da alkhairi abinda ku kai mana,Allah ya biya ku ya rufa asiri duniya da lahira,"

"Ameeen, amma wallahi da kun yi amfani da komai, na ga ba TV ina TV? Ki na zaune ke kaɗai"

"Ai bamu tarar da TV ba, da alama ba TV a parlour ko an daga ta"

"Ohhh aikin....(ta kama suna) ne, shi ne ya tattara har da TV,"

"Babu komai wallahi, dan Allah ki ma bar wannan maganar ai mu Alhamdulillahi ba abinda za mu ce sai godiya"

A parlour muka tsaya ta yi min sallama na koma na ɗauki hijabi na na raka ta har bakin mota ta shiga ta ajiye oven ɗin ta sannan ta sake jaddada min mu yi tunani akan IVF din nan, an yi wa mutane da dama kuma ana dacewa.

Godiya na yi mata sosai sannan na koma gida ina tunanin maganganun ta, na hanga na hango ba ta yanda zan iya yarda a min wannan abun, se na ga kamar za a wahala matuqa, ni kuwa bana son wahalar da wajen nan, irin yanda nake da shegen tsoro ba zan iya ba, ko da Wasa ban yi wa Yah Maheer maganar ba, fatan alkhairi na yi mata saboda yanda take so na da alkhairi ,ya na da yawa shi da Suwaidatu su ka ci abinci mu ka hau hira sama sama.

MAHREEN Donde viven las historias. Descúbrelo ahora