MAHREEN PAGE 12

37 13 3
                                    

💅  MAHREEN  💅











WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 12:






Ko da na fito daga d'aki na kafin na tafi watsa ruwa se da na leqa ta, ganin cewa bacci take kawai se na wuce ba tare da yin kwakkwaran motsin da zai farkar da ita ba, wanka muka yi baki d'aya sannan muka shirya cikin kaya marasa nauyi, muka koma parlour na sa mana abun sallah kamar yanda muka saba ya ja mu sallah.

Bayan mun idar mun yi azkar ne ya janyo mana qur'anin mu babba mai fad'i a saman TV stand dan ya fi ni kusa da shi ya yi min nuni da in je gare shi yanda muka saba yin karatun a tare ina cikin jikin shi, alamu na yi masa da kaina alamar Ah ah, yanzu ba mu kad'ai bane dole yawan zama a manne da junan mu ya ragu,tashi na yi na je d'aki na dakko wani qur'anin na zauna a inda na yi sallah nesa da shi, na bud'e surar da muka tsaya, muka fara rera karatun qur'anin mu cikin nutsuwa.

Tashin muryoyin mu ne ya tashi Suwaidatu a bacci, cike da kyab'e baki irin na wanda suke son yin kukan nan, bayan mun kai qarshen aya na ce mata,

"Kin tashi? Je ki yi alwala ki sallah se ki zo ki ci abinci in yaso da kin yi isha'i se ki koma baccin ki ko?"

Gani na yi ta kasa tashi, sai na ajiye qur'anin na je gare ta, ina tab'a jikin ta na ji ya d'auki wani irin zafi zauuuu, tausayin ta ne ya kama ni, da sauri na hau neman maganin saukar da zazzabi, a saman cinya ta na dora ta na balli maganin Yah Maheer ya miqo min ruwa na bata a baki, cikin yunqurin yin amai ta dinga qoqarin shanyewa, a haka har Allah ya taimake mu bata dawo da shi ba, ta na nan zaune a saman cinya ta kai ba dankwali da rigar da zani na wani yellow d'in  material a jikin ta na yi feeding din ta abinci da kyar ta iya cin shi,abu daya ne ya sake damu na, zama na da na dan yi da ita da yayun ta na kula suna son shan kunu, ni kuma gashi banda shi, dan za a dama kunu tin da safe a babban bokiti a ajiye a kowanne lokaci mutum ya so sha zuwa zai yi ya kamfata ya sha har cikin dare shan kunu suke, sannan ina tunanin na yi qanqanta a kula da ita tinda nima dika dika nawa nake? Yanzu gashi bani da kunun bata gasu da son kunun tsiya.

Dan bana manta zuwan Yayan ta da suke d'aki d'aya,Yah Maheer ya girme shi, ita kuma shine babba a d'akin su, mai suna Isma'il ya zo shi da Abubakar, zuwan shi na farko da na basu abinci suka ci ana hira se da ya tambaye ni ko ina da kunu? Zuwan shi na biyu ma haka, sannan akwai wani zuwa da ya yi still bayan ya kammala cin abinci se ya samu doguwar kujera ya hakimce ya miqe qafafu ya yi zaman shi ya na ta tilawar qur'ani domin Isma'il is claming Ustaz a koda yaushe,hadari ya taso sosai, a zaton mu zai tafi can gidan kawun su ne inda ake riqon shi tinda hadari ya taso goma na dare ya yi, ya kuma ci abincin da ya kan zo ci da dare, Yah Maheer na matuqar so mu je mu kwanta amma ya yi zaman shi, sannan shi be ce anan zai kwana ba, kuma be ce tafiya zai ba gashi har ruwan sama mai qarfi a wannan lokacin ya fara sauka,ji yayi garin ya yi sanyi ya yi ni'ima, sai ya juyo ya kalle ni ni da Yah Maheer da ya kasa jurewa se da ya ja ni zuwa jikin shi, cikin muryar shi ta ustazai ya ce,

'Wato ainihin Amarya kyan wannan ruwan da ake yi mutum ya samu shayi me zafi ko kunun da aka dama me zafi, ya na zaune yana korawa,'

A hankali Yah Maheer ya ce,

"Kai kenan da ka ke gwauro,ni kuwa ina da plans,"

Dariya na yi kawai dan ban sani ba ko Isma'il ya ji ko be ji ba,ni dai da kalmar "gaskiya ne" na bishi da ita, tada ita na yi daga cinya ta na zaunar da ita gefe, a raina ina ayyana,

'Anya yarinyar nan me maqon gida zata yarda ta zauna da mu kuwa?'

Gashin kan ta na sake kallo a karo na ba adadi na sake ayyana.

'Lallai ina da aiki a gabana, ga yarinya me kyau masha Allah amma duk rashin gyara ya sa ta dafe"

A haka muka kwana ranar cikin jimamin zazzab'in da Suwaidatu ke yi, da safe kuwa bayan na gama yi mana abun karyawa sai na dora ruwa mai zafi na mata wanka na wanke mata kan ta da na tsefe shi tsaff, sannan na taje shi na mata oiling,na yanke mata farce se ga shi zazzab'in ya sauka, ta dawo normal, a ranar se da Yah Maheer ya je ya siyo kunu dan kuwa na matsa masa na ce tinda bamu da geron yin kunu dole a nemo mata kunu dan ta fi son shi.

MAHREEN Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon