MAHREEN PAGE 27

33 8 8
                                    

💅 MAHREEN 💅









WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 28:



Komawar mu Birnin Kebbi ta yi daidai da komawar su Suwaidatu makaranta, dan haka babu bata lokaci ranar Litinin ta saka wankakku kuma gogaggun kayan ta ta tafi makaranta, tun kafin mu tafi hutu nake wanke mana kayan mu na goge mana na ajiye saboda irin haka, kar ya zamana mutum bashi da lokacin wanki balle guga kuma an koma makaranta.

Maman Zakiyya maqociyar mu ta tashi har an maye gurbin ta da wata amarya mai suna Hauwa'u, ban taɓa had'uwa da Hauwa'u ba, ban taɓa shiga gidan ta ba tun da muka dawo, katangar gidan ta haɗe suke da ta gida na, ban san da zaman ta a unguwar ba sai wata rana na fita backyard ɗin mu zan yi wanke wanke na ji su ita da mijin ta, anan na tabbatar da cewa an yi baquwar amarya,murmushi na yi na musu fatan alkhairi a cikin zuciya ta, na qudurta a raina da an kwana biyu zan shiga mu gaisa na gabatar da kai na a matsayin maqociyar ta.

Har na yi sati ɗaya ciff ban samu na leqa Hauwa'u ba, ina ta hidimar iyali na, domin a wannan lokacin Yah Maheer ya na yawan zama a gida baya fita, ni kuma in dai ya na gida dama sabo na ne ba inda nake zuwa muna tare da junan mu, ko ba za ai hira ba mu na nan manne kamar chewing gum kowa na latsa waya ko shi ya na rubuce rubuce a takardu ni ina manne jikin shi ina latsa waya da dai sauran su.

Wataranar alkhamis ba na mantawa saboda Yah Maheer na azumi ranar na fito qofar parlour na ina share wa, sanye nake da qananan kaya na kamar kullum sai na ɗora wata milk color riga a sama,wadda ta fi dacewa da a kira ta da net, kai na babu dankwali kamar ko yaushe, sai dai wannan karon ya samu kitso manya guda biyu da na kan yi saboda kar ya zauna a hargitse ga quraje ga rashin gyara.

Wata mace na gani fara ta shigo,tun daga nesa na ga ta na min wani kallo wanda iya sani na ban san matar ba, ban taɓa ganin ta ba me zai sa ta na min mugun kallo kamar ta ga wata maqiyyiyar ta? Maida kai na na yi qasa na ci gaba da Shara ta tunda dama ban san ta ba na tabbata wajen maman Ameerah ta zo, kamar daga sama sai na ji Muryar ta ta na faɗin,

"Aunty? Aunty ki na ina?"

Nan take na ɗauki Muryar ta maqociyar nan tawa ce wadda ban shiga gidan ta ba,cikin murmushi na miqe na isa gare ta na gaishe ta, a yatsine ta kalle ni, sannan ta ce,

"Lafiya qlou,ashe ki na kula mutane"

Nan take se na ji ban ji daɗin yanda take min magana ba,

"Ban gane ina kula mutane ba? Da wani ya ce maki bana kula mutane? Ko dake ban yi mamaki ba duba da yanda ake min munafurci a fad'i abinda ban yi ba, Allah ya kyauta,"

Jikin ta ne ya yi sanyi dan ta zaci zata faɗa min magana na yi jugum kamar sokuwa, se ta ji na bata amsa, tun daga nan ni da Hauwa'u sai ya zamana daga gaisuwa in mun haɗu ba ma qarawa ba ma ragewa, a rana ta kan shigo gidan mu sau ba adadi duk sanda ta ga dama zata shigo ta fita.

Anas almajirin mu ma ya dena zuwa waje na sai dai wajen Maman Ameerah, daidai da gaisuwa ba ta haɗa ni da shi, zan iya wucewa ya wuce shima ba tare da ya ce min ci kan ki ba, abun mamaki yake bani matuqa musamman in na duba yanda muka riqe shi da irin kyautatawar da mukai masu shi da abokan shi, me na masa da na cancancin haka a wajen shi? Wata zuciyar ce ta kwabe ni akan saka damuwa akan abubuwan da basu da mahimmanci, ai kuwa nan da nan se na tattara komai na watsar na ba wa iyali na mahimmanci .

A dan zuwa wajen Maman Ameerah da nake yi mu gaisa ne lokaci zuwa lokaci, ta ke nuna min mamakin ta akan halayya ta ta rashin tsoro da tsaya wa kai na a duk inda na ga za a cutar da ni ko a min ba daidai ba, har watarana ta na faɗin.

"Ni fa wallahi gidan hayar da muka fara zama a Bauchi mugun tsoro na suke, su na girmama ni sosai ba wadda ta isa na ce eh ta ce ah ah"

Dariya na yi tare da buga qafa da qarfi, na yi amfani da hannu na na daki qasa sannan na ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now