MAHREEN PAGE 17

21 11 0
                                    

💅 MAHREEN 💅

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 17

Hidimar bikin Kabeer qanin Yah Maheer da Ke bi masa ce ta kankama ba kama hannun yaro,duk Wani ayyukan girke- girken biki da duk wata hidima da ya kamata ace na sa hannu a ciki ban tsaya wata qiwa ko son jiki ba da ni ake yin komai, kuma ina aiki ne domin Allah ba dan ace wance ta na ta aiki ko ganin ido ba.

Abun da ke matuqar burge Ummahn su da ni kenan, wato rashin gudun aiki ,da rashin qiwa wajen aiki,ko da zan yi in dawo Ina ciwon jiki saboda rashin sabo da aikin yawa kamar nasu ba na qin yi zan shiga a yi komai da ni a tashi.

Bayan kammala biki an Kai amarya gidan ta da ke cikin garin Bauchi Wanda yake da dan tazara da gidammu, amma hakan be hana ni Kai musu ziyara ba bayan kwana biyu da yin bikin nasu.

A hankali muka fara shaquwa da Habibah matar Kabeer wadda ta girme ni a shekaru Kuma ta fini sanin kan duniya, da wannan sanin duniyar da ta fi ni da Kuma girme min da tai a shekaru ta yi amfani wajen Jana a jiki har na sakankance da ita na d'auke ta kamar 'yar uwar da muka fito gida d'aya.

Ta b'angaren Habibah kuwa yanda na ɗauke ta Sam ba haka ta ɗauke ni ba ashe, kallo na kawai take a matsayin tsanin da zata taka ta cimma burikan ta na mallakar dangin miji da Jan dangin miji a jikin ta, duk wata tambaya da za ta min akan kowa na gidan da zuciya d'aya nake zama na bata amsa, sannan da zuciya d'aya nake hira da ita, har ya zamana ba ma boye wa juna abubuwan da suka shafe mu, watarana naje gidan ta sai muka shirya sallar da zata fara a gidan miji za mu je Liman Katagum tare da ita, cikin sa'a sai ya zamana matar Isma'il ma zata je a lokacin ta na d'auke da tsohon cikin ta na fari.

Ko da na koma gida muna hira da Yah Maheer na sanar da shi sai ya ji dad'i da farin cikin yanda muka had'a kammu ni da matar qanin shi, nasiha ya dinga min akan yanda zan ci gaba da zama da kowa lafiya, sannan ya dinga yaba min akan qoqarin da nake na zama da kowa lafiya da nuna kulawa ta da soyayya ta zuwa ga 'yan uwan shi da iyayen shi, nuna masa na yi ai ba komai, nima ai haka yake son 'yan uwa na da iyaye na kamar nashi, dan haka dole na kula da nashi, muna hira Ina gyara akwatin mu na tafiya har na gama tsaf, kallo na ya yi ya yi murmushi sannan ya ce,

"Baby na ke da ki ke ta had'a kaya tin yauuu Se fa jibi ne tafiyar,ko tsabar kin matsu mu je gida inda zaki shiga dangi ki manta da ni?"

"Habaa ba haka bane, kasan akwai kayan Suwaidatu da zan had'a, shi yasa na fara da nawa, bana son yin abu a qurarren lokaci ka sani"

Langwab'e Kai ya yi kamar wani abun tausayi sannan ya ce,

"Allah sarki ni bawan Allah, yanzu in mun je gidan ma ganin ki wahala zai min, gashi na ce ki min tausa tin d'azu kin qi"

A gaskiyar magana tausa na daga abinda bana so a rayuwa, na farko ni ban San dad'in ta ba in ni ake wa, sannan in ni zan yi wa wani sai in ji ana soken hannaye qashi na Sukata, duk sanda na fad'i haka sai Yah Maheer ya ce Ina fad'a masa magana dan na ga ba shi da qiba, Kar na damu zai yi qiba ne sai ya wuce gori a waje na watarana.

Cikin nuna ni fa bana son yin wata tausa na qarasa gare shi na hau yi masa tausa, abokin shi ne ya kira shi a waya suka hau gaisawa, qarshe suka b'ige da hira,cikin sauri na yi amfani da wannan damar na je parlour na sa Suwaidatu d'ebo kayan ta da na goge mata na fara had'a mata tata jakar, takalman Yah Maheer na kwasa na sa a jaka na tsaya Ina kallon kayan namu Ina nishin gajiya, ta baya na na ji an tab'a wuyana, daga Jin haka ba sai na juya ba na San wanene, dan haka kawai sai na tsaya Ina sauraran me yake cewa haushi na shiga ta.

"Baby na dan Allah ki yi hakuri ki cire min kaya na ba da ni za ku tafi ba akwai wani aiki da ya taso daga baya zan biyo ku, I am so sorry darling Kar ki fushi dan na San ba Kya fushi," ya qarasa maganar shi cike da tsokana.

MAHREEN Where stories live. Discover now