MAHREEN PAGE 16

24 14 2
                                    

💅  MAHREEN  💅


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



PAGE 16:



Ni Mahreen na taso na tarar da mahaifiya ta ta na yi wa Baban mu wanki,tin muna qanana har muka yi wayau musamman qananan kayan shi ita ke wanke wa sai dai da wata lalura, ko kuma aiki ya mata yawa ko dai wani abu makamancin wannan, domin akwai sanda hannun ta ya samu mummunan rauni, amma ya na fara warkewa ta ci gaba da yi masa wanki ba tare da ma ya san ta ci gaba da wankin ba, manyan kayan shi da wasu daga fararen kayan shi kawai yake bayarwa a yo masa wanki da guga a waje, dan haka sai nima na qudurta cewar da yardar Allah nima ni zan dinga yi wa miji na wanki da guga, dan haka duk randa Yah Maheer ya cire kayan shi zan d'auka in je in jiqa se na tara kamar guda uku a bokiti d'aya sannan zan wanke, haka zan cakud'a fari da blue me duhu ko green me duhu, har su zuba su b'ata farin, sannan wajen guga in na goge su to fa bana iya daidaita kafad'un a karkace a shagid'e nake gogewa.

Bawan Allah duk irin tsaftar shi da iya karin gugar shi haka zai saka wanda na yi masa ya fita, abokan shi su yi ta masa dariya su na fad'in,

'Amma dai wannan gugar/wankin amarya ne ko?'

Se dai ya yi murmushi ba tare da ya amsa su ba,se ya dawo ne zai sanar da ni abinda ya faru, ya had'a da nuna min shi fa he is satisfied with the qoqari da nake wajen kula da kayan shi da tsaftace su, da kaina na zauna na ga rashin dacewar abinda nake yi, dan haka watarana da Isma'il ya zo mana ziyara se na deb'o kayan na kai masa parlour na ce dan Allah ya koya min yanda ake wanke kowanne kaya ba tare da wani ya b'aci ba, sannan ya koya min yanda ake gugar kayan maza me kyau, ba b'ata lokaci kuwa ya koya min da kyau, tin daga ranar Yah Maheer be sake saka kayan da suka samu zubar kala ba, sannan guga take tafiya samb'al.

Ina zaune ina ta tunanin baya ina murmushi na ji sallamar shi ya dawo daga masallaci, sabuwar tarba na masa wadda ta sanya shi shagala da kallon gayu na, gyaran murya ya yi sannan ya ce,

"Baby Na wannan rigar fa? Kin ga yanda ta karb'e ki kamar a jikin ki aka d'inka ta, sai ki ka yi kama da babyn roba irin masu kubul kubul d'in kumatun nan"

Tura baki na yi saboda ya ce min 'yar lukuta, tini na fara qaqalo hawaye ina son na masa kuka, se hawaye ya bayar da ni ya qi zuwa, dariya ya dinga min sannan ya ce,

"Yarinya na san dika tricks d'in ki you can't fool me, zo nan"

Maqe kafad'a ta na yi na qi zuwa, qasan raina ina jin kamar na fasa kuka, akwai tausayin shi fal raina, ya dawo daga tafiya ba zan iya bashi wata nutsuwa gamsasshiya ba, dan haka na qi zuwa dan bana so ya saka ran samun wani abu a waje na a wannan rana.

Duk wani wayo da dabara da yake min se na qi zuwa, qarshe ma tashi na yi na ce,

"Ahhhfff ka ga muna ta shiririta mun manta baka ci abinci ba fa, ina zuwa na kawo maka"

Had'e fuska ya yi, ya kira suna na,

"Mahreen ! Zo waje na"

Jin haka da na yi kawai se na saki kukan da nake ta dannewa a can qarqashin zuciya ta, da gudu na tafi na fad'a jikin shi, ya kuwa sanya hannayen shi dika biyu ya rungume ni da kyau, kuka nake kamar zan shid'e saboda tausayin kaina.

Kun san dai yanayin jikin mai qiba, yawan sanya pant and pad is not easy at all,ballantana ni da pad d'in ma bata isa ta da towel qarami nake qunzugu a rana sai na jiqa towel sama da uku da jini, ina yi ina wanke wa ina shanyawa,dan haka gaba d'aya cinyoyi na a goge suke, sannan na gaji da yawan shiga toilet gyara jiki na, ga toilet na gidan haya wannan ya shiga wancan ya fita,ruwan wanke towels din ma kan shi watarana wahala yake dan kuwa babu, ina cikin damuwa sosai, gashi na riga na san in jinin ya fara zuba yana jimawa kan ya d'auke, yanzu yana iya ya gama weekend ya koma ba wani abu da ya gudana tsakanin mu, gashi ya yi sati d'aya dama baya nan, ji yayi na kasa yin shiru ba tare da na shirya ba se na ji ruwan hawayen shi a baya na, da sauri na d'aga kai na kalle shi,hannu ya sa ya share min hawaye na sannan ya yi qoqari ya taya ni gyara kwanciya ta.

MAHREEN Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon