MAHREEN PAGE 5

35 15 0
                                    

💅  *MAHREEN*  💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 5:





A gidan Baffan mu aka ajiye amare, dan haka a nan aka ajiye ni tare da Yah Kabeeru nan gidan yake zaune da iyalan shi, kowa ya yi mamakin gani na, murmushi na dinga yi ina musu kallon ba kun taho kun bar ni ba? To gani se yaya?

Murnar gani na aka d'auki yi aka hau tambaya ta ya akai na zo? Na basu labari da yanda driver ke zuqa gudu kamar ba rayukan mutane a cikin motar, can muka baro motoci da yawa ba su iso ba, dan kuwa Motar da  Addah Ummu ke ciki ma na riga ta zuwa, bamu wuce can asalin garin mu ba inda nan ne za a ajiye Addah Ummu sai da suka iso Baffan mu ya musu nasiha sannan aka dauki hanya.

Tafiyar minti arba'in da biyar ce ta sada mu da garin, inda na isa a motar uncle d'in Yah Maheer, ina ta bud'a hanci da ganin ni ma wata had'add'iyar baquwa ce ta musamman a wajen, garin Liman Katagum gari ne mai cike da ni'ima da kwanciyar hankali a wancan lokacin, ga tsafta da kyau a idanun mai kallo, wata iriyar iska ce mai sanyi ke kad'awa da dare wadda ke sanya mutum jin shauqin soyayya ko da ba ka da saurayi ko budurwa sai ka hau imagining ka na da su, yanayi ne da yake ratsa dikkan gab'ob'in jiki da ruhi, hakan ce ta sanya na fita qofar gidan Addah Ummu ina shaqar qamshin bread da ke tasowa daga wajen gidan, ina fita sai na ga ashe gidan bread d'in a kusa yake da su, murmushi na yi a raina na ce,

'Su Addah Ummu an zo gida, za a wa brodi cin Allah tsine uwar me qarya'

Cousins d'ina ne su ka fito suma dan su ga gari da kyau, dik da cewa babu wutar lantarki a lokacin amma akwai hasken farin wata sosai, ta yanda mutum zai iya ganin duhu ko hasken suturar d'an uwan shi, tare da cousins d'ina muka fara tattaki dan ganin ya garin yake, mu na tafe mu na hira cike da nisha'di, can gidan kuma an kai mana abinci manyan yayun mu da Goggonayen mu duk sun ci har an fara aikin gyara gidan amarya.

Bamu dawo ba sai da muka gaji dan kammu sannan muka dawo, ina zaune na gama cin abinci riqe da waya ta qarama wadda Yah Maheer ne ya sai min ita, ina ta latsawa, kira na gani ya shigo da wata Number da ban sani ba, a hankali na amsa wayar na kara a kunne na kamar me tsoron kar a sace ta ta wayar, sallamar da na ji ce ta sanya ni ajiyar zuciya mai qarfi,

'Ina Mansoor ga samu wannan Number tawa?' daga can b'angaren shi na ji ya amsa tambayar da ban furta a labb'ana ba.

'Kar ki damu na samu Number ne a wajen Ikleema' (Qanwar shi)

"Allah sarki ya kk?"

"Lafiya qlou tafiya ba sanarwa"

"A yi min afuwa, na san ka san ana biki a gidan mu, kuma dole zani kai amare, shi yasa ban sanar da kai ba,"

'Kar ki damu,da fatan kun isa lafiya?'

"Lafiya qlou alhamdulillah, ka san rabo na da garin nan kuwa?"

'Ah ah sai kin sanar da ni'

"Tin dawowa ta daga gidan Addah Babba"

Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,

'Lallai an jima, tin ki na 'yar tatsitsiyar ki, gashi yanzu kin girma'

Tura baki na yi cike da shagwab'a ta da take jan hankalin masoya na ba tare da na san tasirin da take da shi a wajen su ba,

"Me ka ke nufi? Ka na nufin dai har yanzu ni yarinya ce, ka san dai na san body language din ka da duk wani amo da ke cikin muryar ka ko?"

Cikin jin dad'in furuci na ya sake kashe murya ya ce,

'Da gaske?'

"Sosai ma"

Kamar daga sama na ji muryar Aunty Meenah ta na cewa,

MAHREEN Where stories live. Discover now