MAHREEN PAGE 21

50 10 0
                                    

💅   MAHREEN  💅






WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 21:




Suwaidatu ce ta shigo ina ciki ban san me ya shigo da ita ba, ina jin muryar ta sai na ji wani kwari ya zo min na daga murya na ce ta je ta nemo taimako qofar ta rufe na kasa fitowa, ai kuwa cikin qanqanin lokaci ta fita sai gata da Maman Ameerah sun taho, nan fa suka dinga kiciniyar buɗe qofa, tun ta na yi a hankali har se da ta dakko wuqa, qarshe dai da kyar aka samu qofa ta buɗe, ko da na fito daga banɗakin gaba daya na jiqe jagabbb da gumi kamar ba wanka na yi ba, numfashi na dinga fitar wa a wahale ido na duk ya kakkafe, banda salati ba abinda nake yi a cikin raina, Maman Ameerah  ta ce,

"Ai na zata malam ya sanar da ku qofar na da matsala se dai ban san abun ya kai haka ba, na yi mamakin irin wannan rufewar da ta yi"

Kallon ta na yi a karkace yaushe ma muka zauna da Malam ɗin a daddafe na zagaya na mata godiya da fatan alkhairi na shiga d'aki, kwanta wa na yi a ƙatuwar katifar da ke dakin wanda nan ne Suwaidatu zata dinga kwana, ji na yi ba wata iska da ke shiga ta, kwalin da aka sako tukwane na na yage suka kuwa zubo ta gefen inda na yage din, na hau firfita ba ji ba gani, a hankali hankali na ya fara dawowa jiki na, na ji bacci na mamayata, to amma ban yi sallah ba, dole na miqe na je na yi alwala na yi sallah, ina idarwa na nemi baccin na rasa se kawai na shirya na ɗauki jug ɗin da aka zuba min ruwan sha da ban sha ba lokacin da muka zo sannan na yi hanyar waje, ina fita na isa saman tabarmar da Maman Ameerah ke zaune da yara, na sake gaishe ta sannan na buɗe jug zan sha ruwa, ina kai wa na ji wani tiririn zafi ya daki fuska ta, nan da nan na janye shi na sanya hannu na, mamakin zafin da ruwan ke da shi ne ya kama ni na kalli Maman Ameerah na ce taɓa ki ji,a ɗan tsorace da ni ta Ke Se ta qi sanya hannu, daga baya na kula irin mutanen nan ne marasa saurin yadda da mutane, murmushi na yi na ce,

"Kin Ji zafi kuwa ruwan nan kamar an kara a wuta, lallai garin nan da zafi sosai"

Sannan ne ta dan yi murmushi ta ce,

"Ayiii haka garin yake ai se ma da rana"

Nan da nan na ji gaba na ya fad'i cikin sauri nace,

"Auuu a hakan da ake gasuwa da rana ya fi?"

"Sosai ma"

"To Allah ya sauqaqe mana ya sassauta mana zafin nan, wannan ai se kitse na ya d'ige tsaff"

Dariya ta yi, sannan ta miqo min abinci, karba na yi na mata godiya sannan na ce suwaidatu ta je ta yi alwala ta yi sallah.

Tashi ta yi ta tafi,Nima ina gama cin abincin na yi mata sallama na koma ciki, Yah Maheer na ganin mun shige ciki shima ya biyo bayan mu, ko da muka shiga se yake sanar da ni qofa fa bata da kyau sosai mu yi a hankali,ya manta be faɗa mana ba, cikin jin haushin shi na ce,

"Eh ai da na maqale na mace a ciki da ka huta tinda baka faɗa ba tun da wuri se da na shiga na jiyo qamshin lahira sannan za ka faɗa"

"Subhanallahi Babyna me ya faru?"

Banza na masa na shige dakin mu na karkade gadon sannan na buɗe akwati na zaro zanin gado na saka na haye abuna na hau addu'ar bacci, ina gamawa na fara shafawa na kwanta, Yah Maheer ashe na can Suwaidatu na bashi labarin me ya faru, ina jin sanda ya buɗe qofa ya shiga ya cire kaya ya daura towel din shi da na tarar a dakin tinda shi dama kayan shi na nan ciki.

Se da ya je ya yi wanka ya gyara jikin shi sannan ya hawo gadon, ina jin shi amma na yi kamar bacci nake yi, dan ya bani haushi da na mutu a cikin banɗakin fa?

Kwanta wa ya yi a jiki na ya na shafa kai na, ya ji shiru ko motsa wa ban ba, hakan se ya bashi tabbacin bacci na yi,dan kuwa baccin gasken ne ya yi gaba da ni, ban sake sanin me ya faru ba sai washegari da asuba.

MAHREEN Where stories live. Discover now