MAHREEN PAGE 31

26 9 2
                                    

💅  MAHREEN  💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 31:








Mun isa garin Kano da misalin uku da rabi na rana, gidan shiru saboda a  wannan lokacin 'yan biki basu fara zuwa ba, tunda sauran sati ɗaya da wasu kwanaki ne,kowa na can cikin gida, amarya ta tafi gidan qanwar Mama gyaran jiki can bawo road, sudanis ne sun iya gyaran jiki sosai, a hankali muka ja akwatin mu muka shiga gidan, a zato na bayan an gaisa za a d'akko maganar gobarar da mu kai dan a yi mana jaje, a lokacin na yi niyyar bayyana yanda abun ya faru saboda in da taimakon da za a yi mana a yi mana, amma duk wanda mu ka gaisa a gidan se na ga ba wanda ya damu da ya ji ya abun ya kasance.

Kayan jikin mu kawai sun isa shaidar sauyin rayuwar da muka samu, shiru na yi na hadiye abinda nake ji na tausayin kai na a cikin 'yan uwa, nima na faɗa hidimar biki tsundum, dama Yah Maheer ya bani dubu goma gudummawar biki, na bayar na riqe sauran dubu goma da ya ce na riqe a hannu na ko zan buqaci wani abun a ciki na je na yi qunshi aka yi wa Suwaidatu baqi da ja itama .

Mu na nan zaune duk wata hidima da za a yi ban ware kai na ba kamar yanda ba wanda ya ware ni, har zuwa ranar da Addah Babba ta zo gidan, na yi murna sosai da ganin ta itama ta yi murna sosai da gani na domin mun jima bamu haɗu ba, sai dai ta zo ba ta da lafiya ni na zauna kusa da ita har ranar da aka fara gudanar da bikin, bikin da ya tara dangi masu dimbin yawa da abokan arziqi, kamar yanda kowa ke kwalliya nima haka na sanya ɗaya daga cikin ɗinkin mu da Yakubu tsara mana, gaba ɗaya fitted gown ya min sai dai yanayin style din kowacce daban ne, se gashi na yi wani irin kyau me ban mamaki kamar wadda ta sanya kaya masu shegen tsada,duk inda na shiga sai an yaba kyan da na yi, ganin dangi da abokan arziqi sai ya mantar da ni duk Wani baqin ciki da damuwa da ke raina, hankali na ya kwanta na wannan lokacin, duk kuma inda amarya take ina nan biye kamar yanda ta min a biki na ta na kusa da ni koda yaushe nima haka na kasance a bikin ta se inda na ga be dace ace yayar amarya na wajen ba se na bar ta da qawayen ta.

Ranar da aka yi dinner kuwa na sha kuka musamman da aka sanya Waqar Ameenah Ameenah 'yar Auta Ameenah Tauraruwar mata....na kasa dena kukan farin ciki a wannan lokacin ita kan ta amarya se da ta yi kuka ganin yanda wajen ya cika da dangin ta da masoyan ta.

Mu ne har azare mu ka raka amarya d'akin ta, Masha Allah gidan Ameenah ba qaramin kyau ya yi ba alhamdulillahi, kwanan mu ɗaya washegari mu ka kamo hanya mu ka koma Kano, daga nan muka je bauchi ziyara zuwa na gidan su Yah Maheer na ga tarbar da ta min dad'i domin kuwa duk sanda mutum ya maka alkhairi ka faɗa,sun nuna alhini da kuma jajanta min gobarar da mu ka yi sannan sun yi mana addu'ar neman tsari kar Allah ya maimaita mana shiga wannan mummunan hali a gaba, godiya na dinga musu har ina hawaye saboda na ji dad'in yanda su ka tuna kuma su ka jajanta mana ainun, kamar koda yaushe se da na dinga kai ziyara daga wannan gida na shiga na fita wancan ba hutawa, ranar qarshe da zan gama ziyara ne na je gidan Rasheedah babbar 'yar Yayar Yah Maheer wanda duk zuwan da zan yi sai na je gaishe ta kamar ibada, daga qarshe na je gidan Ruqayya qanwar Yah Maheer ɗin da suke Mama ɗaya, sai gidan Cousin din shi Ladidi mutuniyar kirki da son zumunci, bana manta wa ina Bauchi ta na yawan kawo min ziyara ta na so na tsakani da Allah.

Da yamma muka koma gida a gajiye,abinci muka ci na yi wanka sannan na sanar da su cewar gobe za mu tafi bauchi daga nan mu koma Kano inshaa Allahu.

A cikin daren Ummah ta sa aka je gidan Dada (Yayar su Yah Maheer babba) aka karbo daddawa da kuka da kubewa busasshiya da kanwa se albasa wanda tun zuwanmu ta aika kuɗi aka yi mana wannan dakan, na ji dad'i sosai na samu kayan na killace su a cikin kayan mu, sannan muka yi shirin bacci.

Da asuba bayan na yi sallah gari ya waye na yi sharar tsakar gida, na sa yara suka wanke banɗaki sannan muka ci abinci, da misalin tara da rabi na safe mun gama shirin tafiya Bauchi, har tasha yaran gidan suka raka mu, mu ka rabu cikin kewa da qaunar juna.

MAHREEN Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα