MAHREEN PAGE 23

41 16 1
                                    

💅   MAHREEN  💅










WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 23:








Mun fara samun shaquwa da su Ameerah sosai ta yanda ko abinci za su ci sai sun dakko sun kawo waje na, ni kuma sai in zuba wa Suwaidatu nata su haɗu su ci, na kan zuba mata da yawa sosai yanda zai ishe su su ci su qoshi su dika,duba da cewa su kaɗan ake zuba masu.

Ban taɓa damuwa ko na ji haushin yawan shigo min da suke yi ba, hasali ma ina jin daɗin zuwan su, ina samu in koyar da su duk wata tarbiyya da aka koyar da ni nima a gidan mu,yaran na da nutsuwa da hankali, musamman Ameerah, ta haddace duk abinda mahaifiyar ta bata so,kuma ya na wahala ta aikata abun nan, a haka na gano yawan hana su zuwa sashe na da ake yi, watarana ko wuce wa na yi zan ganta ta na satar kallo na idanun ta cike da hawaye da na ga haka na san ranar an hana su zuwa kenan se nima na kama kai na, Ameerah yarinya ce fara me kyau ta na da qaramin jiki shi yasa suka kusan yin kai ɗaya da Husnah qanwar ta, shi kuwa Muhammad qaramin yaro ne da ba zai wuce shekara biyu da watanni ba.

Watarana na zuba musu abinci sai na ɗauki namu dan in kai mana mu ci ni da Maman su, Yah Maheer na d'aki ya na cin nashi. (Kun ji babbar wauta, na bar miji na a daki ya na cin abinci shi kaɗai na dauka zan je ci da maqociya, duk zaman lafiyan da mace ke yi da maqociya kamata ya yi a zuba abinci a kai musu kema ki zauna ki ci naki ke da mijin ki).

Ina kaiwa se na ga Maman Ameerah na b'ata rai, sai ban kawo komai a raina ba saboda cikin da ke jikin ta, ga zafi, sannan kusan haka halin ta yake ko da yaushe se tai ta bata rai sai dai in ita ta so ta yi fara'a to fa za ta yi,zama mu ka yi muka jawo abincin ta, taliya ce da miya, ni kuma shinkafa da wake da mai da yaji da cabbage da dai sauran tarkacen da za su qara mata dad'i, gaba ɗaya lissafi na ya bani yanda nake son wake da shi kafa haka kowa ke son shi,bana tunanin cewa kowa fa da favorite food ɗin shi, a cinkishe da fuska muka gama cin abincin nan, bayan kammala ci ne na tattara wanda ya zube, na ɗan zauna hira sannan na koma sashe na.

Ina zuwa se na ga su Suwaidatu sun cinye har ma ta qaro musu, zama na yi ina nazarin bata ran da take ta yi, na menene? Dan dai bata kusa haihuwa ba balle in ce ko cikin ciwon naquda take ko dai na mata wani abu ne da ya bata mata rai? Qudirta wa na yi a raina zan bata hakuri ko in tambaye ta ko na mata wani abu ne, dan ni bana so mutum ya dinga zama da ɓacin raina.

Daki na shiga na tadda Yah Maheer ya ci abinci ya na zaune da wayar shi a hannu, zama na yi kusa da shi na dora kai na a kafadar shi ba tare da mun ce wa juna komai ba,mun jima a haka kamar masu jiran ɗaya ya fara cewa wani abu, a tare mu ka kalli juna muka buɗe baki da niyyar yin magana, dariya muka yi sannan ya tallabe hab'ar shi ya ce min,

"Bismillah.. ladies first"

"Inyeee bature..."

"Suna na, kin san haka Innah Halima ke kira na Balarabe? Saboda tsabar fari da kyau na ina qarami?"

"Yanzu dai na ji amma ban san da hakan ba...ammmm dama kawai ina so na faɗa maka wata magana ne,"

"Game da me fa?"

"Ka ga Maman Ameerah ce se in ga ta na yawan bata rai ko me akai mata oho, ka san na faɗa maka watarana hana su Ameerah zuwa nan take, gashi sai in ga kamar yaran ba sa qoshi watarana har rama suke su yi duhu ina so ina jan su a jiki sosai su saba da ni su sake sosai ina ganin kamar maman su bata so"

Gaba ɗaya ya tattara hankalin shi a kaina ya na ji na ya na sauraro na, kuma ya na fahimta ta sannan ya san hali na ina so in kawo ra'ayi na ya ban shawara ko ba zata min dad'i ba, amma laifin shi ɗaya ya fi bani shawara according to yanda raina ba zai ɓaci ba, se in abu ya kwabe se ya ce kaza ya so ce min amma se ya ga kamar ba zan so ba raina ze ɓaci shi yasa ya fasa ya ce kaza,in na ji haka se kuma in dawo ina jin haushin shi muna faɗa.

MAHREEN On viuen les histories. Descobreix ara