MAHREEN PAGE 3

41 13 1
                                    

💅  *MAHREEN*  💅



WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



PAGE 3

Zaune na tarar da Baba a bakin gadon shi ya na danna laptop din shi gefen shi takardu ne da yawa, sai Kuma littafin addu'o'i guda d'aya a saman takardun,zama na ke qoqarin  Yi a qasan carpet d'in d'akin kafin in gama zaman ya min izinin komawa saman kujerar da ke gefen gado, ban b'ata lokaci ba wajen bin Umarnin shi.

Gaishe shi na yi ya amsa ba tare da ya kalle ni ba, sannan fuskar shi bata nuna min halin da zuciyar shi ke ciki ba, shin ranshi b'ace yake da ni ko Kuma ya ji dad'in fad'ar ra'ayi na da na yi? A dan firgice na kalle shi na Kuma amsa Suna na da ya kira a qoqarin shi na rufe laptop d'in shi da yake.

"Na ga saqon ki, Kuma na gamsu da abinda ki ka rubuta, amma ki sani Maheer yaro ne Mai hankali da mutunci, ban sani ba ko kin samu ana zuga ki ne akan shi? Ba na so tin maza na rububin neman auren ki su zo su na gudun ki, Dan haka nake baki hakuri da ki amince da Maheer, ki maida hankali wajen yin addu'a da yardar Allah, Allah zai maki zab'i mafi alkhairi, ni Ina yi, mahaifiyar ki na yi na tabbata Allah zai amsa ya zaba maki na gari,kin Iya istikhara?"

"Ah ah Baba Ina dai ji ana fad'an sallar istihara"

"Ba istihara ake cewa ba, istikhara ake cewa, Kuma ita wannan sallah ana yin ta ne a Yi addu'ar neman zab'in Allah a cikin ta, karb'i nan"

Littafin hisnul Muslim ya miqa min Mai bango ja, ya riga da ya bud'o page d'in da addu'ar take, se na hau dubawa, Baba ya yi min bayanin yanda zan yi sallar da yanda zan yi addu'ar, ni dai da na gama ji sai na ajiye littafin na kalle shi Cike da shagwab'a ta da ta zame min jiki, na ce,

"Ni dai baba Kai ka yi sallar da addu'ar zata fi karb'uwa"

Cikin zuciya ta kuwa Ina Jin haushin yanda Yah Maheer ya Wani dena kira na a waya balle ya sa qafa ya zo Gani na, to Wani tashin dare zan hau yi ina wahala da Kai na akan shi? Baba murmushi ya yi, ya sake miqa min littafin a karo na biyu, sannan ya ce,

"Tashi ki je ki maida hankali wajen yin abinda na ce maki, inshaa Allahu ni din ma zan yi"

"Na gode Baba"

Na sunkuya na d'auki littafin da kyau na bar d'akin, cikin raina Ina ayyana

'Ai kuwa se dai Kai ka yi sallar nan na kwana bakwai ba abinda zai wahalar da bacci na in ya zo, tinda da alama dan ya ga ya samu nasara ya zubar da duk tarin masoyan da nake da su shi yasa ya ke wa mutane yanga'

Na so na qi yin sallar nan, saboda haushin da nake ji,se dai zuciyata bata bani dama ba, qarfe d'aya da wasu mintunan na tashi na yi alwala na yi sallah da littafi na a hannu saboda ban hardace addu'ar ba, na yi sallah na yi addu'a na samu waje na kwanta.

A taqaice se da na jera kwana uku Ina tashi Ina wannan addu'ar, daga qarshe na watsar na ce Baban da ke son Yah Maheer d'in ya ci gaba ni dai na gama tawa.

*****************************

*Wacece MAHREEN?*

Ni MAHREEN 'ya ce a wajen  Alhaji Muhammad Ahmad da Hajiya Raihanatu, Alhaji Muhammad na da mata guda biyu na aure, ya na da Yara guda goma sha uku masu albarka, sun had'u shi da iyalin shi wajen ba wa yaran shi tarbiyya Kuma alhamdulillah kaff yaran shi ba Wanda za a d'aga a Yi Allah Wadai da shi.

Suna na ya samo asali tin Ina cikin mahaifiya ta, 'yan uwa na ke Kira na da sunan, Kuma su ke da yaqinin shi za a Sanya min idan an haife ni,ko safa aka d'aga za a ce ta MAHREEN ce, idan hula mama ta saqa za a ce ta MAHREEN ce, ma'anar sunan MAHREEN kuwa shine, Mai kyau kamar Rana, ko za a iya fassara shi da abun so, wannan dalilin ne ya Sanya bayan an haife ni Baba ya so ya sauya sunan, suka yi shawara da Mama ta ce,in aka sauya sunan ba a Yi wa Yara daidai ba, tinda sun riga sun Saba da sunan, dan haka ranar Suna aka rangad'a min Suna MAHREEN.

MAHREEN Место, где живут истории. Откройте их для себя