MAHREEN PAGE 34

40 7 2
                                    

💅   MAHREEN  💅












WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







*Mai so a sanya ta a group ɗin MAHREEN2 paid book ta min magana ta wannan No 09031416423*




PAGE 34:








Ina nan zaune se na tuna irin wannan abun ya taɓa faruwa da ni a Kano, wata shekarar da kawun Yah Maheer ya rasu(Baba dan Juma Allah ya masa rahama)ana ta'aziyya ciwo ya turniqe ni dole na zame jiki na koma gefe na kira Yah Maheer na sanar da shi zani asibiti, dubu goma sha takwas ya zaro ya bani tare da bani hakurin ba zai samu damar raka ni ba saboda mutane da ke zuwa musu ta'aziyya, nuna masa na yi babu komai amma can qasan rai na a tsorace nake, na riga na saba komai zan yi ya na biye shi ke min jagora bana son yin abu baya nan, se in dinga jin wani tsoro na shiga ta,haka na daure na tafi asibitin na bi dogon layi kafin na ga likita, bayan na gan shi ne ya rubuta min testes da za a min na jini guda uku na masa godiya na fita, wajen da ake biyan kudi na je na tadda mata jingim a wajen se gefe layin maza ne amma ba su da wani yawa,ina nan na bi layi na sakankance kuɗin hannu na zai ishe ni, har aka zo kai na, bayan sun karbi takarda ta su ka sanar da ni kudin dubu goma sha tara zan biya, ji na yi gaba na ya yanke ya fadi, domin kuwa kudin waje na dubu goma sha bakwai da dari takwas ne ya ragu na taɓa na yi kuɗin mota.

Sanye nake da niqabi sai na ji zufa ta wanken fuska, tini na fita daga layi na koma gefe ina tunanin makama, dan na tabbata ko na kira Yah Maheer d'aga masa hankali kawai zan yi,ni ba account No ba a lokacin balle a tura min na cire ta POS wa ma ya san da POS time din, sam ban san da zaman shi ba a duniya,na san ba shi ma da shi tunda na san aljihun shi, tunani na yi dama ni da Yah Shamsu muka saba zuwa Aminu Kano duk sanda na zo shi ke rako ni in dai ba da Yah Maheer ɗin na zo ba, yawancin likitocin ma da nake gani abokan Yah Shamsu ne, nan da nan na kira shi ina daga zaune a gefen wasu flowers, ya na dagawa na ji muryar shi sai kuka ya kama ni, cikin kuka na masa bayani rarrashi na ya yi sannan ya ce,

'Haba Mahreen ga Sadeeq a asibitin me makon ki neme shi ya baki kuɗin se ki zauna ki na kuka?'

Da niqabi na na goge majinar da ke tarara a hanci na saboda kuka na ce,

'Ba zan iya kiran shi ba, ni bani ma da No shi dan Allah ka kira ka faɗa Masa'

'Akan me ba zaki iya faɗa masa ba? Bari na turo maki No shi dole ki masa magana sanda ba na nan wa zai taimaka maki a asibitin da ya wuce shi?'

Ya Shamsu ba mutum ne mai faɗa ba dan haka yanzu ma cikin lallashi yake nuna min Yah Sadeeq din dai ya kamata na nema hakan ne ya fi dacewa.

Wani sabon kukan ne ya kwace min, nan da nan zazzabin da na ke fama da shi ya qaru, a duniya bana son roqon kowa, bana son na nemi taimako wajen kowa in ba Allah ba, ko Yah Maheer da muke tare ban san in ta ce masa bani bani ba, gashi dai ba na sana'a a wancan lokacin, amma duk abinda ya bani alhamdulillah wanda be ban ba ba na tambaya se idan abun amfanin gida ne da dole sai na tambaye shi kamar su Omo sabulu da sauran su, ko ina jin shagwaba na ce ya siyo min kayan zaqi da na ke mutuwar son sha.

Yah Sadeeq Family friend din mu ne,tare suka taso da Yah Shamsu,abokai ne ko na ce aminai ne, iyayen mu maza abokai ne sosai, dan haka mun ɗauke su a matsayin yayun mu, suma gidan su sun dauke mu a matsayin 'yan uwan su,ni dai ban ji wani comfort na in kira shi na tambaye shi dubu biyu ba se nake jin zai ce na yi roqo.

No shi ce ta shigo waya ta Yah Shamsu ya turo min, ina nan zaune ina shawarar ko gida ma zani ne abu na mu riqe sauran kudin zai mana amfani in mun tashi komawa Bauchin tunda koda yaushe matsala daya ake nuna min, kuma an kasa bani maganin da zai min amfani, ina tsaka da tunanin nan se ga kiran Yah Sadeeq ya shigo wayata, ina dauka na yi sallama, ya amsa cikin yanayin saurin maganar shi ya hau min faɗan ashe ban dauke shi yayana ba,yana asibitin ina neman kuɗi se na kira Shamsu da ma baya gari, to shi ze zo ya kawo min kuɗin? Hakuri na bashi sannan ya ce ya hakura, in je bakin kitchen na asibitin na jira shi, na amsa da toh, nan take na tafi ina share hawaye na ta cikin niqabi na samu waje a bakin kitchen na zauna ina ta duban hanya, a zato na daga ward din da yake aiki zai fito ya tadda ni anan, da yake wajen nasu da nisa, ashe already ya na cikin ma kitchen ɗin ya na jira na, ina nan zaune kusan tsahon minti ashirin da wani abu, shiru ni ban kira ba shi be kira ba, can se na ji an buɗe qofar kitchen ɗin na sake kallon wanda zai fito a karo na ba adadi dan tun zamana a wajen na ke kallon masu shige da fice, ga qamshin abinci da chips na ta dukan hanci na, Yah Sadeeq na gani cikin kayan shi na likitoci ya na tsaye ya na kallo na, da sauri na miqe tsaye ya zo inda nake ya sa hannu a aljihun shi ya dakko kudin ya miqa min sannan ya ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now