MAHREEN PAGE 8

44 16 2
                                    

💅  MAHREEN   💅








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH










PAGE 8







Ina nan tsaye ina tunanin yanda zan shiga cikin d'akin na ga mutum tsaye a kaina,ba tare da na ji lokacin da ya bud'e qofar dakin ba, da sauri na kashe fitilar da ke hannu na wajen ya koma duhu sakamakon rashin wutar lantarki, murmushi ya yi ya wangale qofar d'aki na inda hasken reachable touch light ya gauraye wajen da haske, gani na yi banda wani option da ya wuce na shiga na yi fuska, tinda kashi ai kowa na yi, kuma na ga shima na sha ganin shi ya shiga kashin a can gidan mu, har ruwan flushing na yi qoqarin ja masa a rijiya ba dan ya hana ni ba,fuska na yi na wuce shi na fad'a d'akin na tsaya jikin wardrobe ina tinanin to a ina zan sauya kaya?

A hankali ya tako ya zauna a qasan gado inda ya ajiye ledojin da ya shiga da su fuskar shi bata dena bayyanar da murmushi ba,juyawa nayi na bude ma'adanar kayan da ban san kan abubuwan ba, ban san ina aka ajiye kayan bacci ba, tinawa na yi da Inda yayar mu ta nuna min ta ce in ina da buqatar sauya kayan bacci na duba, da sauri na duqa na kuwa yi arba da kayan bacci na gaba d'aya,na cikin lefe na da wanda na zo da su daga gida, wasu riga da wando light pink na d'auka masu gashi me laushi a qirji da qasan rigar, sai mayafi kalar kayan baccin nawa, ina gama d'auka na rufe na kama hannun qofa zan fita, kallo na ya yi ya ce,

"Ina zaki je?" Cikin sanyin murya na ce,

"Kaya na zan je na saka......kar ka biyo ni bana jin tsoro" na yi saurin qarasa maganar tawa.

Dariya ya yi mai sauti ya ce min,

"To ba zan biyo ki ba, amma ki tafi da key dan na rufe parlourn,"

Key na zare a jikin qofar na fita na bud'e qofar parlour na shiga, ina shiga na maida key na kulle, amma dik da haka sai waige nake ina fatan Allah ya sa kar ya zo, a haka na sauya kayan, masha Allah kayan sun Karb'i jiki na sosai, mayafi na na yafa,na so na qara fesa turare, saboda ni macece da Allah ya d'ora wa son qamshi, tin ina gidan mu in na gama girkin dare sai na yi wanka na feshe jiki na da turare ko da na Mama ne kuwa.

Kyab'e baki na na yi ina ayyana cewar,

'Gwanda ma ki tafi a haka da sauran qamshin ki har yanzu, kafin ya ga ki na fesa turare ya zaci dan shi ki ke yi'

Ina gamawa sai na samu waje a kujer qarama na zauna na yi shiruuu ina kallon yanda iyaye na suka yi qoqari, kamar yanda bana son tarkace Mamana ta sani haka aka had'a min parlour na ba tarkace, ina nan zaune ni ba me tunani ba ni ba me jiran wani abu ba, a hankali ya kwankwasa qofar, cikin sauri kuwa na miqe na je na bud'e,

"Kin yi alwala?"

"Ah ah"

"Muje mu yi to"

A tare muka fita, ya rufe wajen ya sa key a aljihu muka dau butocin mu muka tafi yin alwala,na riga shi idarwa sai na tsaya ya idar sannan muka koma ciki, sallah ya ja mu raka'a biyu, bayan mun idar ya dafa kaina ya min addu'ar da ake yi wa amare a duk daren su na farko,sannan ya hau min tambayoyi game da addini na, da fari har ga Allah na zaci qure ni yake so ya yi, har na dinga tinanin me ya kawo wannan tambayoyi kamar ana islamiyya?

Ya gama tambayoyin shi na bashi amsa, wajen banbance wankan haidha da janaba ne aka samu akasi ban san banbancin su ba, dan haka se da ya min bayani, ya na yi ya na wani kashe murya da lankwasa ta da fitar da makhareej.

Mu na kammalawa ya janyo ledar da ke ta tsinka min yawu, wato ledar kaza, nan fa ya yi bismillah ya yanko wata narkekiyar tsoka ya miqo min, kunya na ji ta kama ni, sai na kasa karb'a, ba yanda Yah Maheer be yi da ni ba akan na ci, na qi cin wannan na farkon da ya miqo min, bakin shi ya kai, nan da nan na had'iyi wani mugun yawu makwat, tsakani na da  soyayyar kaza akwai amana da soyayyar juna,nan take na qudurta a raina in ya miqo na biyu zan karb'a dan ba zan jure qamshin ta ba.

MAHREEN Where stories live. Discover now