MAHREEN PAGE 26

32 14 0
                                    

💅  MAHREEN  💅


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH


PAGE 26:

"Ah bismillah Ku ne ke tafe, ku shigo"

"Wallahi mu ne, ai cewa na yi yau dai se na shigo mun gaisa,"

"Ina yini, ya yara, ya zafin nan na garin ku?"

Cikin murmushi matar ta amsa min da ,

"Lahiya qalou alhamdulillahi, zahi gashi nan ko wallah mun gode wa Allah"

Hira mu ka ɗan taɓa kaɗan a matsayin mu na waɗan da ba su saba da juna ba, sannan ta min bayanin ita ce matar wane da ke can layin mazan mu na gaisawar mutunci ta jima ta na so ta shigo sai yau Allah ya nufa, godiya na yi mata sosai sannan da suka tashi tafiya na raka su har wajen shimfid'ar su Maman Ameerah,anan hirar ta tsaya suka tafi ni ma na gaishe su na koma ciki, washegari sai ta dinga d'akko maganar matar ni Kuma na qi bata dama, saboda ba shi da wani amfani se dai na sanya ta ta yi qarya ni kuma banda wannan lokacin sauraron qaryar ta ta ina fama da kai na.

Haka rayuwa ta ci gaba duk wani wanda nake tare da shi Maman Ameerah ke tare da shi sai ta san yanda ta yi ta hure masa kunne akai na,ana haka sai ɗaya daga cikin abokan Yah Maheer da suka samu aiki a garin Kebbin tare ya yi aure, sanda zai kawo amaryar ba laifi mu ne muka je tarbar su, Amaryar shi fara sol da ita kamar ka taɓa ta jini ya fito,da zuwan amarya sai Maman Ameerah ta dinga qoqarin jan ta a jiki, ni kuma cikin ikon Allah Allah ya riga ya haɗa jinin mu da amaryar, dan haka duk wani qoqari da yunkurin shiga tsakanin mu be samu ba a wajen ta, se ya zamana na tsira da qawa guda ɗaya a cikin unguwar tamu duk da dai akwai ɗan nisa tsakanin mu, amma ko ba komai ni ma na samu mai zuwa min da wanda zan je wa.

Ana haka amarya ta samu ciki, a duniya ina tsananin tausayin masu ciki, yin daga kan Addah maqociya ta ta Bauchi na fara tausaya musu saboda shi ne cikin da na gani tin ya na qarami har ranar haihuwar shi ina tare da ita, dan haka na ga matsananciyar wahalar da mata ke sha,wannan dalilin ne ya sa na ke tausaya wa masu ciki ainun,hakan shi ne ya yi dalilin da ya sa bana rabo da zuwa gidan amaryar saboda cikin nata mai tsananin laulayi ne, wani sa'in ko tsayuwa bata iya wa da kyau sai jiri ya dinga diban ba, abinci ko wanne iri ne aka kawo sai ta qi ci, fruits ne ya zama abokin ta, duk da cewa su din ma ba kowanne iri ba.

Haka zan bar gida na bayan na gama abinci na gyara komai zan je gidan amarya na yi mata girki na gyara mata abinda ya kamata in matsa Mata ta dan samu abinda ta ci, watarana duk qoqari na haka zata kasa cin abincin saboda ba zata iya ba bata so,akwai sanda tsabar tausayin ta sai da na yi mata kuka da na dawo gida,tsoron ciki da goyo da raino baki daya sai ya kama ni, nake ganin ba zan iya ba, kullum addu'a ta sai ta karkata akan Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhairi a rayuwa ta da addini na da rayuwar Yah Maheer miji na.

Ana haka aka samu hutun sallah, mu ka rankaya mu ka yi gida, kamar koda yaushe in za mu gida mun yi ɗinkin sallahr mu mun yi qunshi kitso da duk wata kwalliya da ake yi domin murnar bikin sallah, Amarya ta fara cin abinci duk da ba sosai bane amma ta fi da.

Sai da mu ka fara sauka a Kano mu ka huta sannan mu ka wuce Bauchin Yakubu,direct gidan Kabeer muka sauka mu ka huta sannan muka wuce LK.

Wannan zuwan ya min dad'i sosai saboda kusan kowa da kowa ya zo sallah gida, qannen Yah Maheer mata biyu da ke aure a Bauchi sun zo, cousins ɗin shi da suke aure a wani wajen duk sun zo ga matan qannen shi da yayan shi, gida dai ya cika maqil abun gwanin ban sha'awa.

Ranar sallah haka mu ka dunguma dukan mu yawon sallah, Ni, sadeeyah, Habibah, Zaituna, Bilkisu,Ladhifatu, da Umaimah (Matar cousin ɗin Yah Maheer ce kuma ita ma cousin ɗin shi ce auren zumunci aka yi musu bayan Maryam ta bar gidan aka aure ta) duk inda mu ka je se an bamu barka da sallah dan haka jaka guda mu ka ware ake zuba kuɗin barka da sallah, Memuna ita ce qarama a cikin mu dan haka ita ke riqe da kuɗin, mu na tafe mu na hira cike da matsanancin nishad'i, duk inda muka gilma mun zama kamar wasu taurari, kaf gidajen gwaggunayen su sai da mu ka je daga nan muka je gidan Babbar yayar su Yah Maheer wato Dada, anan aka yi mana goten tsaki da ya ji gyad'a, mommyn Abubakar na dauke da cikin Yaron su na biyu, ta zage ta sha gwaten nan sosai, ni kuwa da dama can ba ya burge ni se na dinga tsince gyadar da aka zuba a ciki ina cinyewa, mu na gamawa mu ka.musu sallama mu ka nufi gidan Goggon Hauwa'u (Itama yayar su Yah Maheer ce cousin ɗin shi ce) anan ma gwaten aka mana a bokiti qarami aka ce za a kai mana gida tunda yawon ziyara muke yanzu.

MAHREEN Where stories live. Discover now