MAHREEN PAGE 13

46 10 3
                                    

💅   MAHREEN   💅



WRITTEN BY HAERMEEBRAERH











PAGE 13:




Garin Bauchi shine tushen Baba zama ya kawo Kakammu garin kano har aka haifi su Baban, shima da ya tashi sai ya yi aure anan garin kanon, a hankali sai ga wata kwarya-kwaryar zuri'a ta tashi.

Sai ya kasance mu dake tasowa ba musan komai na al'adun mutanen Bauchi ba,mun san dai Bauchi garin masa ne,se dai tinda iyayen namu suka tabbatar da za su aurar da yaran su a can sai aka fara sanar da mu dikkan wasu abubuwan masu mahimmanci da ya kamata mu sani.

Na farko an nuna mana kar mu na gaishe da mutane a tsaye, domin mutanen bauchi na so a girmama su sosai, na daga cikin girmamawar in zaka gaida babba sai ka durqusa har can qasa, ba a son mata su na yawan saka kaya wanda zai bayyana tsiraicin su, wannan dalilin ne ya sa mutanen bauchi har yanzu suka riqe d'abi'ar d'aura zani da sa babban hijabi, bana mantawa da girma na an kusan aure na sai da Mama ta dinga koya min yanda zan d'aura zani, da ta ga har a wannan lokacin na kasa se aka d'inka min dogayen riguna da zani 3pieces.

An koya mana kwanon miji daban yake dole a killace shi a tsaftace shi na musamman, cokalin miji daban, takalmin miji da butar miji daban, wajen zaman miji ana gyarawa a tsaftace a sa turare, ballantana uwa uba d'akin da miji zai kwanta, an koya mana abubuwa da dama saboda kar mu shiga dangi mu zama daban.

Isma'il ya fara da tab'a duk wani abu da na killace na ce wannan na miji na ne, to inshaa Allahu shi kuma wannan abun shi zai zama abun tab'awar shi, da fari in ya d'auki abu sai dai in yi murmushi in kyale shi a zato na bai gama gane abubuwan da na ware ba, hakan da nake yi sai ya bashi damar yin abinda ya ga dama, har ta kai ya kai ni maqura na kasa jurewa sai da na tanka.

Wataranar juma'a ina kitchen na gama abinci na raba Suwaidatu ta kai wa Isma'il da Abubakar nasu,mu kuma muna zaune a kitchen d'in ni da Suwaidatu da Hauwa'u 'yar gidan qanwar Yah Maheer da ta dawo gidan da zama saboda ya fi kusa da makarantar da take zuwa, mun saka tabarma saboda girman kitchen d'in ya sa mu na iya zama a ciki mu ci abinci, sai ga Isma'il nan ya shigo.

"Ahhh abinci ake ci,"

"Eh, an kai muku naku ko?"

"Eh an kai amarya uwar gida daga kan ki wallahi an rufe qofa, cokali na zo na dauka wannan ai ba inda zai kai mutum, tinda na saba da manyan nan yanzu bana son amfani da wannan"

Waje yaran suka fita dan wanke hannu, kafin ya kai hannun shi zai d'auki cokalin da nake wa Yah Maheer amfani da shi na dakatar da shi,

"Dakata Isma'il,kar fa ka ga ina shiru ka dinga min abinda ka ga dama, wannan cokalin ka sani sarai na Yayan ku ne, amma saboda dai dole sai na yi magana an ga laifi na shine ka ke d'auka, to gaskiya daga yau kar ka sake d'aukan kayan miji na, tinda akwai wasu se ka d'auka ka yi amfani da shi da can ba da irin wannan d'in ka saba cin abincin ba"

Baki ya saki ya na kallo na, daga baya ya yi kamar be ji me na sanar da shi ba, ya ajiye cokalin hannun sa ya d'auki wanda nake wa Yah Maheer amfani da shi,ba tare da na b'ata lokaci ba kuwa na fizge na mayar na kalle shi ido cikin ido na ce,

"Da za a kawo ni ban san zan zauna da kai ba, dan haka kayan miji na kayan shi ne kar ka sake tabawa, plates d'in shi cokalin shi ba abun amfanin ka bane, ko ku a gida kuna amfani da kayan Baban ku ne?"

Fad'in haka da na yi sai ya yi mugun bashi mamaki, abun har ya kai haka? Har zan iya fad'a masa haka? Ya na gani na yarinya, gani da yawan fara'a ashe na iya fad'a? Ko d'aya cokalin be d'auka ba ya kama hanyar waje inda su Hauwa'u suka tafi wanke hannu, ya wanke hannun shi ya zo ze wuce, mu kuwa har mun fara cin abincin mu, se muryar shi na jiyo ya na fad'in.

MAHREEN Where stories live. Discover now