MAHREEN PAGE 7

29 13 0
                                    

💅  MAHREEN  💅




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 7







Ba kowa bane ya sakko daga motar nan face babban abokin Yah Maheer da suka saba zuwa zance waje na tare mai suna Alhaji Younusa, ya kafe fa sai Amarya ta fita daga motar Alhaji ta shiga tashi wanda shi ma Alhajin abokin Yah Maheer d'in ne,ja in ja aka fara a tsakiyar hanya, gudun kar a b'ata lokaci sai Alhajin ya hakura ya ce mu je mu shiga motar wancan duk d'aya ne, ba haka mu kammu muka so ba a mana juye a tsakiyar hanya, amma dole muka sauka muka shige motar aminin Yah Maheer ya ja mu zuwa bauchi, gudu ya ke shararawa kamar za mu tashi sama, ni kuma kuka nake kamar zan cire ido na,ta cikin farin mayafi na nake hango unguwanni da gidajen da muke wucewa, mu na wuce unguwar su Mansoor na ji wata iriyar kewa ta kama ni, sabon kuka na bud'e murya ta ina yi, Aunty na (Matar qanin Baba) ta juyo ta na bani hakuri, Goggon su Yah Maheer ta ce,

"Aysha batta ta koka, ko ke ce aka dauke ki daga cikin 'yan uwan ki za a kai ki wata uwa duniyar dole ki kuka, balle ita da ta shaqu da mutan gidan su da iyayen ta,za ta dena ne da kan ta ai hanyar ba qarama bace da nisan ta"

Jin haka ne ya sa na fara rage sautin kuka na, ina ta shessheqa da sauke manyan ajiyar zuciya, har muka je wudil ido na na zubar da hawaye, a hankali bacci ya fara diba na, na kuwa gyara zama na na jingina da kujera na lumahe ido na, bacci ne na gajiya da kum bashin wanda bana yi kwana biyu ya d'ebe ni, ban farka ba sai da muka kusan shiga jigawa, a wannan lokacin mayafin nawa kan shi baya saman kai na, Ina d'aga ido mu ka yi ido  hud'u da Alhaji Younusa yana kallo na ta mirror murmushi ya min sannan ya ce,

"To amaryar fa ta farka,an sha bacci,ni yarintar ta na bani dariya fa"

Dariya suka sanya baki d'ayan su, ni kuma na tura baki na ina d'an murmushi sama sama,na ji kunya sosai a lokacin, kuma da alama na jima ina baccin dan kaina a saman kafad'ar surukata(Innar Yah Maheer) na tadda shi mayafi a saman wuya na ya bar kai, hannaye na na dunqule su waje guda kamar me jin sanyi, hira suka ci gaba da yi wadda na kula tin ina bacci suka fara ta,

"Haka akwai wani zuwa da muka tab'a yi da Maheer, ta sha ado da purple material yanda ki ka san 'yar india masu duhun fatar nan,ni kin san Goggo har yau mamakin bawan Allahn nan nake? Dik cikin mu fa shi kad'ai ne bai da budurwa ko irin ta wasan nan,sai gashi ya yi taking d'in mu by surprise ya dakko me kalar larabawa,ranar da muka je ai mun ci taliya me shegen dad'i ( ba ni na dafa ba Addah Ummu ce😂) na jima ban ga yarinya me kunya ba kamar wannan, kud'i fa muka bata amma sam ta qi karba, next kuwa da za mu zo na ce to ai kuwa dole ki Karbi kyautar masoyin ki yarinya, muka siyo turaruka masu kyau, (Rose of love saman turaren wanda yake marfin turaren ne wata kwalba ce da aka yi ta kamar furen flower amma turare ne a ciki shima) sai shower gel da salt of bath, da tarkace na gyaran jiki a cikin wani box na katako me kyawun burgewa, ko da mu ka kai wannan d'in ma da kyar da sid'in goshi yarinyar nan ta karb'a tin anan na ce tooooo lallai Maheer ka yi sa'a,ka yi dacen matar aure ka riqe ta da kyau, gashi kuma da alama ta na son shi ta na mutunta shi,"

Wata harara na yi a cikin ido na da ke a rufe, a raina ina ayyana,

'Wannan bawan Allah akwai shegen surutu, wataqila shi ya sa ya nace se ya kai mu, dan ya yi ta tona asirin zancen da ya ke raka Yah Maheer d'in, wannan ko an kai ni muka gan shi zama za mu yi kamar kurame kar ya d'auki magana ya qara gaba da ita'

Hira suka ci gaba da yi Auntyna na basu labari na dan su san cewa 'yar tasu ta jiqu da tarbiyya, Goggon Yah Maheer banda gasgata ta ba abinda take kamar ta sanni dama can, (ta yi imani da cewa indai ni 'yar babana da mamana ce to kuwa za a same ni da tarbiyya, shine dalilin gasgata maganar da take yi)

Ba mu yi aune ba sai ganin mu muka yi a Ningi, dan kuwa ba qaramin gudu yake zabgawa ba,a wannan lokacin kowa baya ganin kowa sai fitilar mota dake haske gaban mu, duhu ya yi sosai, mun so matuqa a tsaya a yi sallah a hanya amma ya ce mu yi hakuri in mun isa ma had'e da isha'i, haka kuwa aka yi, mu na shiga cikin garin Bauchi ya zabga hamdala da qarfi ya daki sitiyarin motar ya kunna fitilar cikin motar sannan ya ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now