Page 1

143 9 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 1*

              ~Gani nan fitowa haneefa kiyi hakuri please charger nake dubawa"
wacce aka kira da haneefa tana tsaye tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, tayi kyau sosai cikin leshi blue wanda akayi ɗinkin half bubu, kyakkyawa ce ajin karshe fara ce sol gata doguwa batada kiɓa kuma batada rama, irin cif ɗin nan ce, ɗaurin kanta yayi kyau ta zuba gashinta d yake da tsayi da tsantsi ta baya, takalmin kafanta flat ne baki da jaka shima baki a hannunta, da alama sauri take domin ta zubawa kofan babban falon ido tana ɗan tsaki kaɗan, hannu tasa ta dafe kanta kana tace "dan Allah Noor ki fito kinsan idan munyi latti Abba will punish us"
da ɗan gudu ta fito tana sa charger cikin karamin jakan dake rataye a kafaɗarta, wata kyakkyawar budurwa ce wacce taji kyau har ta gaji dashi, farace doguwa ba kiɓa ba rama tasa bakin abaya me tsagu a gaba, fararen kafafunta idan abaya yayi gefe sai su bayyana, tana wani irin shining jikinta kamar madara, bayan tasa charger a jaka ta ɗau ribbon dake hannunta ta kama gashinta wanda ya sauka har gadon bayanta yana taɓo ɗuwawunta, kamewa tayi kana ta ɗau siririn mayafin tayi rolling a kanta, bakin glsss ta ciro tasa a idonta ya rufe mata rabin fuskan, hakan ya kara fitowa da asalin kyaunta, takalmin kafanta me tsini ne baki, cingum ta jefa a baki tana fitar da kamshi na musamman, saida ta ganta a waje kana ta fara taku cikin iyawa da yanga da yauƙi har ta iso wajen haneefa wacce take kallonta tana murmushi, tana isowa ta rungumeta kana ta lumshe ido cikin sanyin murya da zaƙin murya tace "am sorry sis Ina ɓata miki time a duk lokacin da zamu fita am so sorry please"
a hankali haneefa ta shafa bayanta kana ta janyeta daga jikinta tace "oya let's go munyi latti"
jerawa sukayi suna tafiya a tare a cikin maƙeƙen gidan, gidane na alfarma tsararre kuma kerarre gefe guda masu gadi ne da masu kula da harkokin gidan, compound suka nufa da sauri wani guard yazo ya buɗe musu marfin mota, motan baki ne kirin da jikin harda glass ɗin tinted ne, jikin motar kamar kwai gashi yana sheƙi, haneefa ce ta fara shiga kana Noor ta mika mata jakanta sannan itama ta shiga ta zauna a gefen haneefa, driver ne yazo ya shiga, gaishesu yayi haneefa ce ta amsa Noor ta maida hankali kan wayarta tana latsawa ko kallonshi bata yi ba, getman ne ya buɗe musu maƙeƙen get ɗin kana driver yaja motan suka fita, haneefa ta kalli Noor kana tasa hannu ta karɓe wayan dake hannunta, yamutsa fuska tayi kana ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace "haba hanee ki bani mana ina da chat da classmate tawa ce"
sawa a jaka haneefa tayi kana tace "da alama baki ma tsorata da lattin da mukayi ba, kin manta halin Abba ne? wallahi idan muka rasa wannan takaddan ba zamu fita outside ba muna nan nigeria har wani sati"
murmushi tayi kana ta gyara glass ɗin dake idonta tace "kada ki damu ko Abba be samar mana wannan takaddan ba, inada wanda zai bamu, ke meyasa kin fiye tsoro ne?"

numfashi ta sauke kana ta ɗau ruwan gora ta buɗe, kurɓa tayi ta rike a hannu sannan tace "noor ba zaki gane bane, inason fita a wannan satin banaso auren elham yazo ba tareda na fita waje ba, kinsan elham zatace nice best friend kuma wallahi ba zan iya ba saboda maza zasuyi yawa a wurin, kinsan fa wanda take aura ɗan babban gidane zai zama da abokai da yawa ni kuma banson cikin maza"
"haneefa kenan bama cikin maza ba har matan ma ba so kike ba, gara ki warware dan kinga Mami batason wannan halin naki na noƙe noƙe"
murmushi kawai tayi, tsayawa driver yayi kana ya juyo jikinshi yana rawa yace "hajiya mun iso"
haneefa cikin sakin fuska tace "tom mun gode"
buɗe marfin motan yayi ya fita, haneefa fitowa tayi ita kuma Noor tana zaune saida ya zagaya ya buɗe mata kafin tasa kyakkyawar kafarta ta fito, tana shan kamshi har suka jera suna tafiya, babban hall ne me kyau da alama taro akeyi a wajen, a bakin Get na shiga suka tsaya haneefa ta nuna mishi wani ticket kana suka shiga, hannun noor ta riko ganin mutane cike a wajen ana jawabi, kallonta noor tayi "zaki fara ko? sai kace yau kika fara shiga taro"
"dan Allah kada ki saki hannuna noor mutane sunyi yawa"
kafarta har harɗewa yake gani take kamar ita kowa yake kallo, noor kuma saima gyara taku da tayi tana tafiya tana kallon mutane ɗaɗɗaya ta cikin bakin glass ɗin data manna a fuskarta, da haka har suka isa wani kujeru wanda aka tanada domin baƙi, gyarawa haneefa kujeran tayi saida ta zauna kafin itama ta zauna a gefenta, hannu ta mika mata ta marairaice tareda shagwaɓe fuska tace "unty haneefa ki bani wayata to"
"a,a bazan bayar ba saimun koma gida"
turo baki tayi "dan Allah fa"
bata wayan tayi "ki kashe kisa a jaka dan kinsan nan abu me amfani za'ayi ko?"
girgiza kai tayi kana tayi reply na message ta kashe wayan tasa a jaka, hankali suka maida akan mutumin da yake jawabi, babban mutum ne me kamala da harshen turanci yake magana, mutanen wajen suma manyan mutane ne da yaran manya, kana ganin taron kasan taro ne na masu kuɗi da mukami, suna daga zaune aka kawo musu drinks da snacks haneefa ce ta karɓa ita noor bata ko kallo server ɗin ba, ajiyewa tayi a gabansu kana tace "ga ruwa da snacks"
girgiza kai tayi "I have water in my bag"
da mamaki haneefa tace "kin ɗau ruwa all the way from gida kinzo har nan dashi?"
giɗa kai tayi.
haneefa ta saba da halin kanwar tata, haka take bata cin abinda ya fito daga hannun mutane koda kuwa ruwa ne sai tace hannunsu da kazanta, tanada kyankyami gata da kallon banza, halin Noor sai haneefa ce take iyawa.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now