chapter 15

40 4 0
                                    

*HAƘƘI NA*

By
_jiddah S Mapi_

15.

                ~Noor tana shiga ɗakin ta cire mayafin dake jikinta, kallon cikin ɗakin tayi bai wani haɗu yadda takeso ba, shiga cikin bedroom tayi ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, ita dataso ta gyara rayuwan haneefa shine Allah zai jefata cikin kurkukun ƙaddara? wannan ai prison ne a wajenta, da wani ido zata fara kallon kawayenta da abokanta tace tayi aure a wannan akurkin? hakika ta tsani anwar ta tsani koda me kama dashi ne, kuka takeyi sosai har saida taji kamar zata shiɗe kafin ta rufe ido kamar me bacci tayi shiru, a wajen ta kwana ko kaya bata canja ba, anwar ma yana can ɗakin inna acan ya kwana baiyi gigin zuwa koda kofan ɗakin bane.

washe gari bayan ta tashi bata buɗe ɗakin ba tana ciki tana zaune, anwar yayi shiri cikin manyan kaya ya yiwa inna sallama ya wuce wajen aiki, noor tana zaune sai kuka takeyi har yanzu taki shiru ga idonta a kumbure, inna ta girka abin karyawa ta zuba a kula jiki a mace taje bakin kofan ta fara bugawa tana kiran sunanta "noor? noor ga abin karyawa ku buɗe ƴarnan kici kada yunwa tayi miki illa"
tana jinta tayi banza da ita, saida taji ta isheta da bugun kofa ta mike a fusace ta buɗe kofan, kallon kulan tayi kana ta karɓa, murmushi inna tayi "kici ƴata kada ki zauna da yunwa"
buɗe flask ɗin tayi taga taliya ne da wake jallof, zazzagewa tayi a kasa tana kallon cikin idon Inna, baki inna ta buɗe tana kallonta har ta gama zubar da abincin, saida taji ba komai a kula tace "na miki kama da wacce zataci wannan kazamin girkin?"
girgiza kai inna tayi, tura kofan tayi ta shiga kana ta rufe da bolt, Inna ta kalli abincin ta kuma kalli kofan ɗakin da yake a garkame, paka ta ɗauko ta kwashe kana ta zubar a dustbeen, flask ɗin taje ta wanke ranta ba daɗi.

noor kuma tana shiga ɗaki taji wani irin yunwa yana azalzalan cikinta, a hankali ta karasa wajen frij ta buɗe, akwai snacks ga kuma hollandia yoghourt ɗauka tayi ta fara ci, saida ta koshi kafin ta maida sauran cikin frij ta koma taci gaba da kuka, wani akwati dake gefe wanda Abba ya bata ta buɗe tana duba kayan da suke ciki, da alama wa haneefa ya tanada saboda aurenta, kwali ta gani ta buɗe taga wani babban waya a ciki, kunnawa tayi harda sabon sim, Kallon gaban wayan tayi hotonta da haneefa ne suna zaune a palour akayi musu, shafa gaban wayan tayi kana ta ɗau wani agogo me kyau a cikin kwali shima, a hankali tace "wannan na haneefa ne ba nawa ba bari na ɓoye mata"
tashi tayi tasa a cikin wardrobe kana ta dawo ta fara game a wayan, hankalinta yaki kwanciya a hankali ta kashe wayan ta koma ta kwanta, tashi ta kumayi kamar an tsikareta ta ɗau wayan tayi dialing wani number, ana ɗagawa ta bada saƙo tace a kawo mata zuwa Anjima,  kashe wayan tayi ta koma ta kwanta.

bada jimawa sosai ba akayi sallama a kofan gida, daga ita sai wani dogon riga da hula akanta ta fita, karɓan ledan tayi a hannun driver ta koma ciki, inna tana cikin gida ko kallon inda take batayi ba, saida ta shiga ɗaki ta buɗe ledan tana kallon goran, murmushi kawai tayi tana kallon goran, maidawa tayi cikin drower.

Anwar yana isa wajen aiki ya wuce office nashi, da kyar yake amsa ya hakurin da mutane suke gaya mishi, yana shiga office ya rufe ya zauna akan kujeranshi, ɗaga kanshi yayi sama yana kallon slin, a hankali hawaye ya fara gangara daga idonshi zuwa haɓanshi, karamin lips nashi na kasa ya ciza, ba abinda yake tunawa kamar soyayyan da haneefa ta nuna mishi, tuna lokacin da taje wajenshi siyan rake yayi, har yana tsokanarta abinda bai taɓa yiwa wata ɗiya mace ba, wayanshi ya ɗaga yana kallon hotonta wanda yasa a wallpaper, a koda yaushe murmushi ne akan fuskanta bata fushi kullum da fara'a da walwala a tare da ita, gashi rayuwa ta juya ta rabashi da ita, runtse ido yayi yana tuna lokacin da take shafa face nata a nashi, gaba ɗaya ta sa mishi soyayya wanda ba zai iya cirewa ba daga zuciyanshi, babu macen da zai kara so koma bayan haneefa, duk wani motsinshi ita yake gani, sanyinta, murmushinta, hakurinta da kuma iya soyayya da kula dashi, Allah kuma saiya haɗa aure tsakaninshi da wannan mara kunyan, wacce bai taɓa sawa a ranshi zai zauna da ita ba, takaddu birjik a gabanshi suna bukatan sign ya gagara ɗaga koda ɗaya ne, wayanshi ne ya fara ruri yaga sunan Abba, ɗagawa yayi cikin girmamawa yace "ina kwana Abba"
"lafiya kalau anwar ya ita noor ɗin ya jikinta?"
gabanshi ne ya faɗi domin baisan halinda take ciki ba, da kyar ya harhaɗa zance yace "tana lafiya jiki da sauki alhmdllh"
"yawwa to Masha Allah ka kula da ita tasha magani akan lokaci nasan halin noor da magani ka sata dole tasha, maganin yana cikin karamin akwatin dana bata"
"to Abba na gode"
Abba yana katsewa ya mike ya ɗau jaka da makullin mashin nashi, fita yayi daga company ya hau mashin ya nufi gida, ya manta amana suka bashi dole ya kula da ita, inna tana ɗaki tana bacci koda ya lekata yaga haka saiya wuce ɗakin noor, knocking yayi kana ya tura kofan bakinshi ɗauke da sallama, cikin nutsuwa yake tafiya yana kallon dakin ba abinda ta taɓa yadda aka jera haka yake, a hankali ya karasa cikin bedroom, waro Ido yayi ganin abinda take shirin yi, baisan time ɗin daya karasa da gudu ya kamo hannunta yana kwace goran dake hannunta ba, kokawa suka fara yana kokarin kwacewa tana hanawa, zaune take akan stool gaban mirror tana kallon fuskanta tana murmushi, a hankali tace "noor haneefa ta nuna miki soyayya yadda bakya zato, ta soki kamar ta cinyeki, shine zaki saka mata da haka? baki dace da wannan fuskan da gangan jikin ba, dole ne na ɓata fuskana da acid ko Allah zaisa na daina ganin kaina a madubi, wannan mugun fuska ne mara imani"
Acid ta ɗauko a gora zata watsa a jikinta da fuskanta shine anwar ya shigo yaga abinda take shirin yi.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now