page 4

57 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 4*

              ~Ɓangaren me rake, ranshi ya ɓaci da marin da tayi mishi, saide yaji sanyi lokacin da ƴar uwarta ta rama mishi, idanunshi masu kalan madara ya lumshe a hankali yana cigaba da tura kus-kus na raken, baida magana shiru-shiru ne shi, koda a wurin sana'anshi bai fiye surutu ba, da yaje sun gaisa da makotanshi sai yaci gaba da abinda yake gabanshi, yauma haka ya kasance bayan ya isa wajen wani dakali da yake zama ya kwashe raken ya jera akan table dake gabanshi, hannu ya ɗagawa mutanen dake gefenshi masu saida gyaɗa da masu saida karas, suma akan table suke akewa, gaisuwa ya aika musu suka amsa, ruwa ya ɗiba ya yayyafawa raken sannan ya zauna a gefe ya ɗau wayanshi dake ringing, a hankali yake motsa jajayen lips nashi wanda suka karawa fuskanshi kyau da armashi, gashi da kwarjini, a hankali da rashin surutu yace "hello inna ta"
ta ɗayan ɓangaren muryan tsohuwa ce tace "Anwar ya hanya?"
"lafiya kalau inna ya gidan?"

"lafiya kalau ka kula da kanka banda bin abokan banza"
lumshe ido yayi ya saba da wannan nasihan inna yanzu fa ya fita daga gida ta gama yimishi wannan faɗan yanzu kuma ta kirashi tana kara mishi faɗan, jin yayi shiru tace "kana kina ko baka jina?"
giɗa kai yayi kamar tana ganinshi, tace "na san kai ka giɗa yaushe zaka daina miskilanci ne anwar? har wani kana yiwa, ka buɗe baki kamin magana"
tashi yayi ya mika rake ya karɓi kuɗin yasa a aljihu kana ya koma ya zauna yana jinta, saida ta gama surutun kamar yadda yake faɗa kana yace "inna idan kin gama zan kashe wayan"

"kenan ka gaji da jin surutu na ko? nice aku kuma nice kala uwar zance, na dameka shine..."
katse wayan yayi kana yasa a silent ya maida cikin aljihu, baison damuwa da surutu ga inna idan ta fara bata gajiya, maida hankalinshi yayi akan sana'anshi.

Anwar kyakkyawan matashi me neman na kanshi, yaro ne wanda ya taso cikin talauci tare yake da kakarshi wacce yake kiranta da inna, tunda ya tashi ita ya gani a matsayin uwar rokonshi iyayenshi sun mutu hakan yasa ya rike kakarshi duk wani damuwa nashi wa ita yake gayawa, baya ɓoye mata komai, suna zaune a wani gida ɗan karami wanda yake da ɗaki biyu, ɗaya nata ɗaya nashi, yana saida rake kuma Allah yana rufa mishi asiri yana samu har ya ciyar da inna da kanshi a sana'an saida rake, tsakanin gidansu da inda yake saida rake basuda nisa, tsakaninsu kwalta ne ba wani nisa sosai, yayi karatu saide yanayin kasan namu yasa bai samu aiki ba, ya karanci harkan kasuwanci amma har yanzu shiru ba aiki hakan yasa ya hakura yaci gaba da sana'anshi na saida rake yana addu'a Allah ya buɗa mishi, yana da abokai biyu Nasir da Jameel, sun shaƙu sosai Nasir mahaifinshi yana da kuɗi kuma yana taimaka musu, shi kuma jameel shima ɗan talaka ne kamar Anwar ɗin.

Inna batason abinda zai taɓa mata anwar ko fita yayi ta rinƙa kiranshi kenan a waya tana tambayar ya yake ya kaza ya kaza, har sai ya gaji ya kashe wayan, idan ya dawo tayi ta masifa har tayi shiru ta sauko suci gaba da hira kamar ba abinda ya faru, Anwar yanada kwarjini da cikan haiba, baya son raini ko kaɗan bai damu da harkan mutane ba, baya shiga harkan mata, akwai ƴammata dayawa wanda suke sonshi saide shi basa gabanshi burinshi yayi sana'a ya ciyar da kakarshi ya rufawa kanshi asiri.

zuwa ake ana siya raken mutane dayawa hakan yasa yana jin daɗi domin duk lokacin da ya fito yana samun masu siya dayawa, wani ma saiya kira an kara kawo mishi dami kafin ya tashi, yana cikin gyara wanda ya kankare motan Nasir ya tsaya a gefe, kallonshi yayi kana yaci gaba da aikinshi, sauke glass yayi ya leƙo yace "inason rake"
ko kallonshi Anwar baiyi ba saboda yasan halinshi tsokana ya kawoshi, dariya nasir yayi yace "nace a bani rake ko baka son customer ne?"
cigaba yayi da gyaranshi, buɗe marfin motan nasir yayi kana ya fito, shina yana da kyau masha Allah gashi chocolate color yanada haske amma ba fari bane, rufe motan yayi ya karasa wajen anwar hayewa kan table ɗin yayi ya ɗauki rake ɗaya wanda yake a fere a gyare ya fara sha, yana sha yana kallon Anwar saida ya shanye kana yace "My gee nazo ne muyi magana"
aje wuƙan hannunshi yayi kana ya janyo kujera ya zauna yana kallonshi yace "ina jinka Nas meya faru?"
gyara zama nasir yayi looking serious yace "Abba ne yazomin da wani zance wanda banji daɗinshi ba sam"

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now