chapter 16

33 4 0
                                    

*HAƘƘI NA*

By
_jiddah S Mapi_

16.

                ~A mugun firgice ta tashi tana haƙi tana waro ido, bakinta sai rawa yake da kyar tasa hannu ta kunna light ɗin dake ɗakin, a mugun tsorace ta sauka daga kan gadon ta buɗe kofan ɗakin ta fita, a bakin kofa ta zauna tana kallon cikin gidan domin ba zata iya bacci ba koda ta kwanta ga wani tsoro da takeji kaman tayi ihu, inna dake bacci a ɗaki ta tashi dan fitsari takeji, cikin gida ta nufa zata ɗau buta taga noor a zaune, da sauri ta koma baya tana salati, kallonta tayi sosai kana tace "lafiya kika fito warhaka?"
girgiza kai tayi batayi magana ba, ganin ta girgiza kai ya bawa inna karfin halin zuwa wajenta, aje butan hannunta tayi tace "noor meya sameki? wani abin akayi miki kika fito cikin gida da wannan lokacin?"
girgiza kai tayi batace komai ba sai hawaye da yake zirara daga idonta, tausayi ta bawa inna, amma tana tsoron yarinyar saboda batada kunya, "kiyi hakuri ki koma ɗaki, idan kin kasa bacci ne kiyi alwala kiyi salla Allah zai yaye miki damuwa kinji?"
giɗa kai tayi kana ta mike ta shiga ɗakin, toilet taje tayi alwala tazo ta shinfiɗa sallaya ta tada salla, raka'a biyu tayi sannan ta jingina da jikin bango ta gyara hijabin dake jikinta ta rufe fuskanta taba addu'a, hankalinta yaki kwanciya, haneefa take kallo kowani lokaci, ji take kamar ta kira Abba ta gaya mishi abinda ya faru, saide idan ta faɗa mishi babu abinda zai hanashi tsine mata, addu'a tayi sosai kafin ta kwanta akan sallayan, bacci da kyar ya ɗauketa.

Inna tana shiga ɗaki ta tashi anwar, tashi yayi yana murza ido yace "inna"
shiru tayi, ganin tayi shiru ya gyara zama yace "meya faru inna?"
"anwar kaje ka samu yarinyar nan ku kwana tare, kada wani abin yazo ya sameta, ka jure duk wani abinda zatayi maka na rashin mutunci"
"inna meyasa?"
"saboda naga halinda take ciki, idan mutum yana cikin damuwa irin wannan ba barinshi za'ayi shi kaɗai ba"
jijjiga kai yayi "ba komai zanje amma sai gobe"
"a,a yau nakeso domin yanzu ma a waje na ganta tana zaune tana kuka kada damuwa ya mata yawa tazo ta kashe kanta muna gidannan"
tashi yayi saboda shima yayi wannan tunanin, a hankali jiki a mace yace "bari naje saida safe"
girgiza kai tayi "Allah ya tashemu"
fita yayi yana kallon kofan ɗakin, haka kawai bayason abinda zai haɗashi da wannan yarinyar, ciwon haneefa bai goge daga zuciyarshi ba bayaso ta kara mishi wani damuwan akan wanda yake ciki, ko bacci baya yi me kyau saiya haɗa da addu'a da salla yake samun bacci, a hankali ya karasa bakin kofan yana shirin knocking yaji kamar a buɗe yake, tura kofan yayi nan take ya buɗe, shiga yayi da sallama a bakinshi, babu kowa a falo dai karan fanka dana frij wanda yake aiki, komai a kimtse, wucewa bedroom yayi, kallon kan gado yayi ba kowa, ji yayi gabanshi ya faɗi, dudduba ɗakin ya fara, ajiyan zuciya ya sauke lokacin daya ganta kwance akan sallaya tana bacci, fuskanta yayi zufa sosai ta dukunkune kamar wacce take tsoron wani abu, zama yayi a bakin gadon yana so ya tasheta ta gyara kwanaciyan amma baisan ta inda zai fara ba, a hankali ya mike yana taku cikin nutsuwa, jallabiyan dake jikinshi ya ɗan ɗaga sannan yasa hannu biyu ya ɗagata sama da niyan kwantar da ita akan gadon, jinta kamar a hannun mutum tayi saurin buɗe manyan idanunta ta zubasu akanshi, saida gabanshi ya faɗi ganin manyan idanunta a cikin nashi, wani irin kallo ta aika mishi sannan ta kalli jikinta wanda yake cikin nashi, bai kulata ba ya dake ya fara tafiya da ita, zillo tayi zata faɗo kasa da karfi ya riketa, hannu tasa ta fara tureshi cikin masifa tace "saukeni"
bai sauketa ba kuma baiyi magana ba, bakin gado ya kaita ya ajeta kafin ya ɗau pillow ya wurga a kasa tareda kwanciya akan tiles ɗin dake shimfiɗe a ɗakin, zagi ta fara tana cewa "Allah ya isa haɗa kazamin jikina da naka da kayi, kai wani irin mara imani ne? sai yaushe zaka fahimci noor ta tsaneka? bata sonka ta tsani duk wani abinda ya shafe ka, meyasa ba zaka fahimci banason ganin fuskan wanda yayi sandiyyan mutuwan yayata farin cikita ba?"
a duniya babu kalman da yake mishi zafi kaman wannan kalman, mikewa yayi daga kwancen da yake ya kalleta da kyau yace "wanene yayi sanadiyyan mutuwan yayarki? ni?"
"eh mana ko bakasan talaucinka yasa aka kasheta ba?"
"ta ina? ya akayi kikasan talauci ne yasa aka kasheta?"
shiru tayi domin bataso kowa yasan wannan magana matukar Abba ya sani to wallahi ta gama yawo, ganin tayi shiru yace "idan kika kara gayamin wannan maganan sai kin gane bakida wayo"
"kaine mara wayo bani ba"
tana daga kwance tayi maganan, komawa yayi ya kwanta ba tareda ya kulata ba, tana kwance hawaye yana zirara daga idonta, a hankali tasa bayan hannunta ta share hawayen, da haka har bacci ya ɗauketa.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now