page 2

49 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 2*

              ~Ɗakinsu ta shiga ta cire kayan jikinta kana ta faɗa toilet, wanka tayi da sabulai masu kamshi kafin ta ɗaura towel wanda ko cinyanta bai rufe ba ta fito tana tsane jelan gashin kanta wanda ruwa ya taɓa, waka takeyi tana girgiza kai, zama tayi a gaban mirror ta shafa mai kana ta taje gashinta ta kalli kanta sosai a ta cikin mirror, far far tayi da manyan idanunta kana tace "Allah na gode maka daka yini kyakkyawa ajin karshe a kyau"
tashi tayi tana ɗan ja towel ɗin kasa ta zubawa jikinta ido, tabbas tana da kyau gata da diri, a hankali tace "ga kyau ga kuɗi ga hutu me kuma nake nema?"
lumshe ido tayi a hankali tace "miji kyakkyawa me kuɗi"
wani irin murmushi ta sakarwa kanta wanda ita kanta tasan ba karamin kyau yake kara mata ba, juyawa tayi taje gaban sirf ta buɗe, kayanta ne a sama jere gasu nan dayawa sai kuma na haneefa a kasa, wani riga marar nauyi ta ciro kana buɗe tana kallo, rigan baƙi ne silk hannunshi yana da tsayi sai les a bakin sai kuma igiya da za'a ɗaure ta ciki, sawa tayi a jikinta sai ji tayi kamar yana yakushinta, cije leɓe tayi kana taje gaban mirror tana kallo bayanta, zaro ido tayi ganin rigan a kone da alama da dutsen guga aka kona mata, cikin masifa ta cire tasa wani wando daga sama a ɗage daidai kugun, sai kuma kasa aka buɗe sosai kamar skirt black ne tasa top shima black, baza gashinta tayi sannan ta ɗau rigan data cire cikin rashin mutunci ta fara tafiya, tun daga sama ta fara kwala kira "Salamatu!!! Salamatu!!! Salamatu!!!"
da ɗan gudu har tana tuntuɓe matar da aka kira da Salamatu ta shigo falon, taka matattakalar take kamar bata taka kasa, fuskar nan babu alaman hakuri atare dashi, wani irin kallo take aikawa matan wacce a girme zata girmi mami koma ta haifeta, saida ta karaso inda matar ta durkusa sannan ta naɗe rigan ta wurga mata a fuska, cikin masifa ta ɗaga yatsanta ɗaya tace "kin kona min riga shine zaki dukunkune ki ɓoyemin a cikin kaya kenan kadama na san kin kona ko?"
kanta kasa tace "kiyi hakuri noor wallahi bada sanina na kona ba, ƴata ce ta kirani cikinta yana ciwo shiyasa na rikice har kayan ya ƙone"
murmushin rainin hankali tayi kana tace "ba dole cikinta yayi ciwo ba, dama yaranku na kauye me suka sani banda bin maza"
"ƴata bata bin maza ciwon ciki ne irin namu na mata"
"okay to wa kike nufi take bin maza, ni ko haneefa?"

"ba haka nake nufi ba noor kiyi hakuri dan Allah banaso na rasa wannan aikin nawa dashi nake taimakon ƴaƴana marayu ki taimaka"

tsaki taja ta tsani complain a rayuwarta batason complain, hannu tasa ta dafe kanta jin yadda matan take rokonta, juyawa tayi "zan barki amma saikin biyani kayana ki maidamin yadda kika samu idanma sabo zaki siya wannan damuwanki ne"
rike kayan tayi tana kallo, me zata fara yi? ta yaya zata biyata? tafi kowa sanin halin noor batada mutunci ko kaɗan zata iya yin komai akan kayanta.

tashi tayi zata fita sukaci karo da Abba wanda ya jima a bakin kofa,yaji duk abinda ya faru, a hankali yace "ina wuni mama"
ɓoye kayan tayi cikin zaninta sannan ta kakalo murmushi tace "ka dawo ne Alhaji? sannu da dawowa"
jikinshi a mace yace "kiyi hakuri da abinda noor tayi miki kinsan har yanzu yarinya ce"
"batamin komai bafa Alhaji nice ma nayi mata laifi"
shiru kawai yayi ya mika mata hannu yace "bani kayan"
mika mishi kayan tayi jikinta har yana rawa tana tsoron kada ya yiwa noor faɗa ko wani abin ta rama akanta, murmushin takaici yayi dan ya fahimci a tsorace take "karki damu zansa a siyo mata sabo"
komawa yayi da rigan a hannunshi ya kira driver ya bashi rigan sannan ya bashi kuɗi yace "ka samomin irin wannan rigan ko nawa ne ka siya, idan ka dawo ka bawa mana Salma wannan kuma ka kyautar"
karɓa driver yayi cikin girmamawa yace "to Alhaji"
mota ya shiga, Abba kuma ya koma ciki yana takaici da jin haushin abinda noor tayi, sallama yayi itace a falo tana ɗaukan turare a showglass wa mami, tana ji yayi sallama ta ajiye turaren taje da gudu ta rungumeshi, shima rungumeta yayi ya danne ɓacin ranshi yace "noory ya gidan?"
sakinshi tayi "lafiya lau Abba ka dawo?"
girgiza kai yayi "na dawo kawomin ruwa"
zama yayi akan kujeran yana cire safan kafanshi, ruwan ta kawo mishi da cup ta tsiyaya ta bashi, karɓa yayi "yawwa noory Ina maminku?"
"tana ɗalinta"
"call her for me"
tashi tayi ta wuce sama, binta yayi da kallo, sai yaushe zata fara ganin mutuncin mutane marasa galihu? sai yaushe zata fara girmama talaka? abin yana ɗaure mishi kai, ya rasa yadda zaiyi wannan ƴar tashi tasan daraja da kuma kiman ɗan Adam ko ya yake, mami ce ta sauko tana murmushi, zama "sannu da dawowa"
"yawwa gimbiya"
zama tayi a gefenshi tace "ya naga duk zufa bayan ga ac?"
kanshi ya ɗaura akan kujera yace "ba komai na gaji ne sosai"
"sannu kayi wanka sai kaci abinci ka huta ko?"
tashi yayi "to"
shiga ɗaki yayi saida yayi wanka yayi alwala yayi sallan mangrib kana ya sauko, samunsu yayi kowa yana falon kasa, mami tana ganinshi tace "to muje tunda ya fito"
murmushi yayi "me nayi ake jirana?"
"cewa sukayi idan bada kaiba ba zasuci abinci ba"
dariya kawai yayi sannan yaje dining ya zauna, haneefa taje ta bayanshi ta rungumeshi tana dariya tace "Abba sannu da dawowa"
shafa face nata yayi "yawwa haneefa"
zama tayi a gefenshi itama mami ta zauna, noor ce take serving nasu, ta sawa kowa abinda yakeso,ya faruk ya shigo yana waya, saida ya gama ya karaso ya zauna yana yiwa Abba da mami sannu, haneefa da noor suka gaisheshi ya amsa yana latsa waya, noor ce tace "me zansa maka?"
be kalleta ba yace "rice da stew"
tashi tayi tasa mishi kana ta koma ta zauna, aje wayan yayi ya maida hankali kan abinci, shiru sukayi sai karan haɗuwan cokula da plate kakeji, noor ta dukar da kai tana cin favorite food nata wato coconut rice da coslow, wayanta yana gefe akan dining bini bini tana kallo da alama akwai kiran da take jira ya shigo, haneefa ma tana cin abinci tana kallon mami wacce take bawa Abba a baki, murmushi takeyi domin wannan ɗabi'an mami sun saba dashi, duk time ɗin da zasuci abinci ita take bawa Abba a baki har sai ya koshi kafin take ci, faruk kam bama ya kallonsu domin sun riga sun saba, kallonta mami tayi ganin yadda take murmushi tace "hanee kema watarana haka zaki bawa mijinki abinci"
hannu tasa a fuska ta rufe mami bata jin kjnyansu, Abba yayi dariya ganin yadda take rufe fuska wai taji kunya, noor tace "insha Allah a gidan masu muƙami a gomnati ma kuwa mami"
da sauri ta dukar da kai taci gaba da cin abinci ganin tayi ɓarin zance ya faruk ya aika mata wani uban harara wanda yasa tayi shiru, ci gaba sukayi da cin abinci kowa yayi shiru, sallama akayi muryan mama salma ne Abba ya amsa, noor tayi shiru tana kallon kofa, bataso abba yasan abinda yake tafiya meyasa matar nan za tazo a time ɗin nan?"

firgigit tayi jin tace "noor ga rigan"
a hankali ta kalli Abba wanda ya zuba mata ido yana yimata kallon tambaya, cikin son dabarcewa tace "tom na gode"
karɓa tayi tasa a cinyarta tana cigaba da cin abinci, Abba yace "rigan menene?"
"am Abba rigana ne"
"meya sameshi?"
rau-rau tayi da ido kana tace "na..na...na bari ne a waje.. shine.. shine.."
"Alhaji shanya mata nayi"
mama salma tayi magana, Abba baiso haka ba yaso ta bari ita noor tayi bayani, baison ya haifar da raini tsakaninsu ne da sai yaja mata kunne yayi mata gargaɗi, hannu yasa a aljihu ya bawa amma kuɗi, taki karɓa saida mami tasa baki kafin ta karɓa tana godiya, tana barin wurin noor ta mike sum sum ba dan ta koshi ba ta bar wajen itama, tsoronta Allah tsoronta kada Abba ya sata a gaba saita faɗi gaskiya.

binta Abba yayi da kallo har ta ɓace, a ranshi yace "Allah ka shiryamin noory ta fara ganin darajan talaka da marasa arziki ameen"

tana shiga ɗaki ta rufe kofan ta jingina da jikin bango ta dafe kirji, godiya take yiwa Allah da yasa salamatu bata faɗi abinda ya faru ba, turo kofan akayi a tsorace ta juya tana kallon ko waye, haneefa ce ta shigo tana murmushi tace "noory meya faru na ganki a tsorace?"
"ba komai"
tayi magana tana ƙarasawa bakin maƙeƙen kyakkyawan gadonsu wanda aka ƙawata wa kowa nashi da kayan ado irin na India, zama tayi a bakin gadon ta buɗe data tana duba sakonnin da suke shigo mata ta watsapp, saida ta karance duka na reply tayi na bari ma ta bari, Instagram ta hau tana amfani da suna queen beauty, sakonni ta gani daga manyan masu kuɗi waɗanda take alaqa dasu, hannu tasa ta janyo lallausan pillow ta ɗaura kanta akai tana murmushi tana reply, haneefa kam toilet ta shiga tayi freshen up kana ta fito tasa rigan bacci tareda fesa turare ta haye gado, wayanta ta mikawa Noor tace "samin a caji"
hankalinta yana kan waya bama taji abinda haneefan take faɗa ba sai murmushi take.

saida haneefa ta taɓa ta sannan tayi firgigit tace "meya faru?"
tsaki taja kana tace "nikam ki samin caji, ace chatting kika maida hankali haka akai? dawa kike chat haka?"
"nida ƙawata minal ne"
"to ki gaisheta"
jijjiga kai kawai tayi taci gaba da chat nata, kashe wutan ɗakin tayi kana tace "good night"

"night have a nice dream"
tayi magana tana mamakin yadda haneefa bata damu da chatting ba, bata wani damuwa da latsa waya, simple life takeyi batada kawaye dayawa abin yana bawa noor mamaki, saida tayi chat sosai kana ta kashe wayan ta jona caji, toilet ta shiga tayi fitsari kana ta dawo ta kwanta, ganin haneefa tayi nisa a bacci ga blanket ya janye daga jikinta, ta mike ta gyara mata blanket ɗin kana tayi mata peck a goshi, komawa tayi itama ta kwanta nan bacci ya ɗauke ta.

a cikin bacci ta fara mafarkin wai ana aure a gidansu auren haneefa, kawayenta ta tara sunyi anko sai shagali ake, yaron yace ba anan nigeria zasu zauna ba, noor sai kula da baki take, murmushi ne akan fuskarta tana bacci tana mafarki me daɗi.

*Washe gari*

Bayan sun idar da sallan asuba suka fara shirin school, noor tasa wani riga da wando rigan fari har gwiwa sai wandon ash color, ta kame gashinta kana ta ɗau farin hijabi guntu tasa, Baby bag pink me laushin gaske ta rataya a bayanta, takalmi snicker tasa kana ta fito hannunta rike da milk shake, suna dining su duka kowa yayi shiri Abba shirin zuwa office shima ya faruk yayi kyau cikin shadda dayasa da alama company zai tafi, zama tayi tana kallon haneefa wacce tayi shirin school itama tayi kyau uniform nasu iri ɗaya, gaishesu tayi suka amsa ta zuba tea ta fara sha, saida suka gama breakfask Abba yace "ku kula da kanku noory banda raini"
girgiza kai tayi kana suka fita a tare, driver ya buɗe musu lafiyayyen mota suka shiga, fita sukayi daga gidan suka nufi hanyan school, babban makaranta ne ya samu kuɗi ma'ana an kashe kuɗi a school ɗin, kana gani kasan na yaran masu hannu da shuni ne, get aka buɗe musu suka shiga har ciki, bayan yayi parking ya fito ya buɗewa noor, haneefa kamar yadda ta saba yauma ita da kanta ya buɗe ta fito, noor tana gyara zaman jakanta ta mikawa haneefa milk shake ɗin dake hannunta, saida ta gyara ta karɓa tana sha suna tafiya a cikin babban filin school ɗin, ajin su haneefa shine farko, shiga tayi bayan sunyi sallama ita kuma noor tayi gaba tana shan abinta hannunta ɗaya akan jakan dake bayanta tana tafiya tana kallon kowa ɗaya da rabi, ɗalibai wasu na kan desk wasu na zaune a asalin wajen zamansu, ta shiga class ta samu waje ta zauna tana cigaba da shan milk shake nata, bata yiwa kowa magana ba har malami ya shigo, babu wanda ya mata magana dan kowa yana ji da kuɗin babanshi, sai can wata ta shigo itama sa'ar noor ce, chocolate color kyakkyawa da ita, teddy bag nata ta aje a gefen Noor kana ta zauna tace "noory?  yau kin fito da wuri what happened?"

lumshe ido Noor tayi kana tace "kibari kawai kinsan unty haneefa da shegen sauri, da fatan dai kinzo mana da pot?"
jijjiga kai tayi, malamin dake teaching yace "kai? wa yake surutu?"
ko ɗago kai noor batayi ba, taci gaba da magana batama san yana yiba....

*08144818849 Jiddah S Mapi*

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now